HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 41-45

” Eh toh, dama Zeenat ce tazo, shine tayi min magana akan tana so dan Allah ka kira Bashir kace yazo ya dauke ta, Ashe tun ranar da mukaje suna gida bata koma ba, shi kuma be zo ba.”

” Toh… Ina Zeenat din?”

” Gata.”

” Bata wayar.” 

” Gashi.” Ta mika mata,

” Ina wuni?”

” Lafiya lou, ya gida?”

” Lafiya lou.”

” Menene ya faru?”

” Dama…” Ta bashi labarin da ta bawa Iman bata rage komai ba, murnushin yayi yana daga zaune, a kalla yasan zuwa yanzu ta dawo hayyacin ta, ta kuma yi nadama tun daga yadda ta kwantar da kai tana masa magana, ya kuma tabbatar da uwar ta ma tayi laushi tubus, dama abinda yake so kenan, su russuna wa Iman dinsa har su nemi alfarma a wajen ta.

“Shikenan ki koma gidan zaizo anjima.”

“Nagode Nagode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara girma…”

“Amin.”

” Hello…”

” Baby zan kiraki anjima, ki kula da kanki kinji? Bye.”

” Bye.” Ta kashe wayar

” Yace naje gida zai zo.” Ta fad’a cike da murna

” Masha ALLAH hakan yayi.”

” Bari kiga na tafi, Mama bata san nan nayo ba asibiti nace mata zani, Nagode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci.”

” Amin.”

Kofa ta rakota tare da bata kaya masu yawa a cikin leda tace ta gaida gida, ta kuma sa aka fitar da ita har in da zata samu abun hawa. 

*Ayi min afuwa jiya nayi kuskure wajen cewa Iman tayi sallah bayan tayi bari, ban ma lura da aika-aikar da nayi ba sai daga baya, ban yi editing page din ba sam ina ta sauri na tura. Ayi hakuri kuskure ne

_ZAFAFA2022????_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO_*

_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*????????

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*????????????

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*????????

09134848107

2/25/22, 18:10 – Buhainat: *Hafsat Rano*

      _Halin Girma_

            *43*

***kiran Bashir din yayi bayan sun gama wayar, be same shi ba, kila baya kusa. Ajiye wayar yayi ya maida hankali sa wajen Aji da suke magana kafin shigowar wayar tata.

“Me ma kake cewa?”

“Ungo nace.” Yayi masa dakuwa

Dariya ya saka har da buga kafa

“Dan tsohon nan akwai riciki, toh ba zan waya da matata ba, naga kaima idan yar tsohuwar chan ta kiraka cikin rawar jiki kake zuwa.”

“Gwara ni ai, kai daga gani mijin tace ne ai, sai uban rawar kafa sai kace kanka farau a aure.”

Sake fashewa yayi da dariya cikin son kular da Ajin yace

” Naga alama dai kana taya yar tsohuwar chan kishi ne.”

” Oho dai, matanmu na dah sun fi naku na yanzu komai da komai.”

” Habawa, banda tawa matar dai, tawa daya tamkar da dubu ce.”

” Toh Baban masoyan duk duniya, kaine ma ramiyo yake ko wa?”

” Romeo ake cewa, ai nama fishi.”

” Kaji dashi, Allah yasa dai kar ayi lusarin sarki wanda mace zata dinga jujjuya shi, ya kasa aiwatar da komai.”

” Ai tunda kuka dage sai kun bani mulkin nan haka zaku hakura, ana cikin zaman fada zaku ga nayi fit na fice toh Itace tayi kira.”

Mikewa Aji yayi cikin kuluwa yace

” Ka bada maza wallahi, kaga tafiya ta ba zan iya kin wannan shirmen naka ba mara kan gado.”

” A gaida min tsohuwar sarauniyar taka, zan shiga anjima naci tuwon wajen yar tsohuwa.”

Murmushi kawai yayi, ya fice fadawan sa suka bi bayan sa, yana da kwarin sa har yanxu ba zaka taba cewa ya kai shekarun sa ba, Allah ya bashi lafiya me inganci sai dai fatan gamawa lafiya.

  Yana fita Bashir ya kira, sai da ta kusan katsewa sannan ya daga yana mikewa tsaye daga kishingid’ar da yayi dan yana so yaje yaga Ammi dan da wuri sai wuce gobe, sai kuma ya gama tsaf da chan sannan zai tattaro ya dawo nan din.

” Yallabai barka da warhaka, ayi min afuwa ashe ka kira.”

” Barka dai Bashir, eh na kira ai ban dauka ma ta shigo ba.”

” Wallahi network din ne, Allah ya baka yawan rai ya aiki?”

” Mun gode Allah.”

” Masha ALLAH, Allah ya taimaka ya bada sa’a.”

” Amin, alfarma nake nema wajen ka.”

” Habawa, wane mutum, ka fadi ko menene kake so, an gama kawai.”

” Bashir kenan, toh Nagode. Dama so nake idan Allah ya kaimu bayan Magriba kaje ka dauki matar ka ku tafi gida, shi aure daka gani ya wuce duk in da kake tunani ko hasashe, hakuri shine ribar zaman dan haka ka ajiye duk abinda ya faru a baya, ka fuskanci rayuwar ka.”

“In Sha Allah an gama, dama so nake ita da mahaifiyar ta su fuskanci rayuwar yadda take.”

“Zuwa yanzu sun gane ai na sani, kaje ka dauki iyalin ka.”

“Zanje in sha Allah, nagode Allah ya kara girma.”

“Amin nagode.”

Sallama sukayi ya ajiye wayar, dama yana son yaje ya tafi da ita dan ya gane yadda ta damu ta dawo ko da text message din da take masa, shima kuma abinda yake so kenan, abu daya ya saka shi delay shine kayan dakin da ya saka akayi mata masu kyau daidai kudin sa, sai sabon gidan da Moh din ya bashi a lokacin bikin me kyau madaidaci two bedroom da falo da kitchen sai parking space, wanchan gidan da aka kaita hayar sa suka karba amma ba shine ainahn gidan da ya bashin ba.

  Kayan duk sun zama ready an saka komai an kwaso kayan kitchen dinta an zuba mata gidan yayi kyau daidai gidan amarya. Shi kansa yanzu yake jin sa a angon na gaske, bayan doguwar dambarwar da suka sha da hajjajun sa karshe dai sun rabu bayan ya dawo ya tarar da ita suna aika-aikar su da kawayen ta, da yayi magana ta taso masa kamar zata dake shi, karshe ma tace ya saketa ta gaji da auren sa, ta samu wani sabon saurayin me jini a jika, da farko yayi ta mata magiya akan tayi hakuri amma fafur taki, sai kawai ya danne zuciyar sa ya saketa, aikuwa yana sakin nata yaji wani sakayau kamar an zare masa wani mugun nauyi, sai ya hau tunanin ta yadda akayi ma ya aure mace irin ta bayan ya san abinda take aikatawa, abu daya ya sani shine kwadayin abun duniya ne ya kwashe shi har ya yarda ya amince ya aureta, bayan ta jika shi da kudi masu yawan gaske.

   Text message Moh ya turawa Iman yace ta fadawa Zeenat ta shirya zaizo bayan sallah, aikuwa tayi mata forwarding text din tana gani kuwa ta kirata ta dinga mata godiya. Dakin Mama ta wuce ta sameta a zaune ta rafka tagumi yadda abubuwan suka sauya mata a lokaci daya shine yake bata mamaki, ba tun ranar ta gano Abba so yake ya maida auren su da Maman Iman ba, sai yau ta gasgata hakan da yace mata ya tafi Abuja. Karamin hauka tayi masa amma yayi biris yayi tafiyar sa.

   Ko da Zeenat ta zo mata da labarin zuwan Bashir din sai taji dadi, a kalla zata huta da maganar yan gidan da ma makwafta akan zaman Zeenat din a gidan.

“Sai ki hau shiri ai, kafin yazo, kinje kin shantake a asibitin da tun dazu kika dawo ai da kin yi shirin da ya kamata.”

“Anya ma asibitin kawai kika je?”

“Eh mama, chan naje likitan ne be zo da wuri ba.”

“Toh sai ki shirya.” Tace mata

“Toh.” 

Daki ta koma ta dan harhada abinda zata hada, ta zauna tana lissafin awowin da suka rage, sai ga Mama ta shigo da Madara a kofi me dumi ta bata tace ta shanye, ta karba ba musu ta shanye tas ta bata kofin ta fita.

  Har akayi sallar magriba aka idar da wajen minti talatin be zo ba, ta gama matsuwa Mama na lura da ita, ita mamaki ma take yadda ta juye lokaci daya. 

  Ana idar da sallar isha’i ya aiko yaro wai Zeenat tazo inji Bashir, da sauri ta mike Mama ta harare, ta koma jiki a sanyaye ta zauna

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button