HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 16-20

 

Halin Girma    16

*****************

Yana zaune a daki kiran Aunty Faty ya riske shi, dagawa yayi yana tashi dan yasan dalilin kiran

“Mun shirya tafiya kawai zamuyi kana ina ne?”

” Ina cikin gidan bari nazo.”

Yace yana cire wayr, takalmin sa ya zura ya fito falon, fadawan dake wajn part din suka yunkuro jin motsin sa, da hannu yayi musu alamar kar su bi shi ya shiga takawa zuwa shashen Fulani da ya san a chan zai same su. 

   Babban falon ta ya nufa in da ya tarar da su da yawan su, daga gefe akwatuna ne masu yawan gaske, da ido ya bi kayan kafin ya zauna suka hau tsokanar sa da ango ango, yawancin su yan uwan Ammin sa ne,sai dangin Bubu da matan abokan sa da badu da yawa sosai, komai Takawa yace sai Bubu yace masa ba sai an zo ba, ayi komai a nan din kawai. Yanzu ma dan dai abun kamar al’ada ne, shiyasa kawai Takawa yace ya kyale su idan yaso sai ya zama ba kowa da kowa ba.

  Anty Faty ce ta tashi ta hau nuna masa yadda kayan suke

“Wannan saitin na Takawa ne, gasu nan 12 ne cip, kaya ne na alfarma komai da kasan ya kamata a saka an saka ciki, sai wannan masu pink din su kuma saitin Ammi ne, suma Sha biyun ne kamar na Takawa, wadannan kuma masu purple din na Hajja ne da dan tsohon mijin ta Aji, guda shida ne gasu nan ko? Sai masu maroon din nan na karshe, namu ne dan muma ba za’a bar mu a baya ba, suma guda 6 ne idan ka hada set nawa kenan? ”

” 36!” Yace yana sake bin kayan da ido.

” Wadannan kwandunan  kuma, gasu nan guda 24 kowanne da ka gani, abokin Bubu Maimartaba sarkin Ghana ne ya aiko dasu.”

” Allah sarki.” Yace yana murmushi

” Kilishi fa?”

” Auw kaga na manta ko? Gasu chan fito dasu Harira.”

Tayi wa daya daga cikin bayin dage tsaye daga gefen kayan magana, 

” No a barsu bana bukatar su, a barsu anan zan duba su daga baya, akwai kayan da za’a kai na rabon da zasuyi a dangi, suna cikin Ford 2 nasa an saka su, zaku duba kafin ku wuce, komai yayi in sha Allah.”

” Owk shikenan, kaga wadannan boxes din da kasa aka yi musu design a dubai da hoton ku?”

” Na gani aunty sunyi kyau sosai, su nake so a fara fitowa dasu, dan Allah aunty ayi duk yadda nace.”

” An gama karka damu.”

” Shikenan, Musaddik zai shige muku gaba, ya za’a yi tafiyar?”

” Eh da wai kamar motoci goma haka, sai wanda za’a zuba kayan Hilux din Takawa masu rufin bayan nan, idan yaso sai su biyo baya ko?”

Murmushi yayi me aji, ya girgiza kansa yana ayyana kalar tsiyar da ya shuka yana kuma jinjina abinda zai faru nan da wasu yan awoyi. Bed room din Fulani ya shige, ya sameta da yan uwata da suka zo, ya zaune tsakanin wasu tsofaffi biyu ya dinga tsokanar su ya hanasu sakat, kowa ya ganshi yasan yana cikin farin ciki mara misaltuwa, yanayin sa kadai zaka san ba karamin murna yake da auren ba, su kuwa basu san harda murnar hawan jinin da ya tabbatar zai kama Mama, dama ita hassada ga mai rabo taki ce, idan kuma zaka gina ramin mugunta toh ka gina shi gajere baka san ko kai ne zaka fad’a ciki ba.

****Mama babu zama tun da taga yamma tayi ta tabbata suna hanya ko sun kusa zuwa, tayi nan tayi nan duk farin ciki ya hana mata sakat, karar tsayawar manyan motoci a kofar gidan ya saka kowa nutsuwa aka hau sake gyara wajen, kowa ya zauna ana dakon shigowar su.

   Gate din gidan me gadi ya bud’e da sauri, aka shigo da motocin da akwatunan suke ciki, sauran aka bar su a waje saboda babu wajen da zasu shiga dukka.

   Sauke akwatunan aka fara yi a harabar wajen, kafin su gama sauke su dukka guda talatin da shida, sai baskets din suma. Boxes din da Anty Faty tayi masa magana akai suka riko kowacce mace ta rik’e daya a hannu dama yan kanana ne, matan da Mama ta wakilta da idan sun zo su tare su ne suka karaso kowanne fuskar sa dauke da fara’ar suka tare su sannan suka yi musu jagoranci zuwa ciki, Mama na zaune an sha lullubi da kayan alfarma suka shigo, ta bisu da kallo ta kasan Ido, mata ne hamshakai wanda suka amsa sunan su mata, hutu da jin dadi ya kama jikin kowacce kai ba sai an fad’a maka ba. Rawar jiki jamaar Mama suka fara su a lallai an zo wajen su, dangin su Abba na gefe sun zama yan kallo, akwatunan aka dinga    shigowa dasu Mama ta hadiye wani yawu me karfi, cikin al’ajabin uban kayan da ake ta shigo dasu, gaba daya ma sai ta bata lissafi suka dinga yi mata gizo, kamar ta tashi ta hau bubbudasu taji, wani farin ciki na ziyartar ta. Duk gaishe gaishen da ake tsakani bata wani fahimta saboda yadda ta tafi tunanin kalar hutu da gatan da Zeenat zata shiga, gashi alamu sun nuna dangin mijin nata masu karamci ne, basu da nuna kyama ko wulakanci ko kadan.

“Baki ne daga gidan sarki, mun kawo lefen dan mu, jikan Maimartaba sarki, sannan d’a ga sarkin Adamawa Alhaji Ahmad Santuraki,Ina mahaifiyar amaryar tamu take?”

Mama tayi firgigit sanda taji wata cikin matan na tambaya, murmushi ta yi tana sake kama kanta ita a dole akwai surkutar nan. Aunty Faty ce ta tashi tsam, ta isa gaban Maman ta mika mata akwatin hannun ta, dake dauke da hoton Moh da Iman da ita kanta Iman din idan ta gani zatayi mamakin yadda ya same shi, hoton yayi masifar kyau zaka rantse tare suka dauka, yana sanye cikin shigar babbar riga da rawani, yayi wani murmushi da zaka kalla ka sake kalla. Wani irin shock Mama taji lokacin da ta karbi akwatin a hannun ta hoton da yake jiki ya shiga cikin idon ta ya aikawa da kwakwalwarta sako a take.

“Wannan itace kyauta ta farko ga yar mu Fatima, akwai sauran kyaututukan da bazasu kirgu ba, amma dai ita wannan din ita ce zamu iya cewa ja gaba ga sauran.”

Kamar mutum mutumi haka Mama ta dinga kallon matar da take mata wani yare da sam kwakwalwarta ta gaza dauka balle ta fassara mata abinda matar take cewa. 

“Wadannan kayan kad’an ne daga cikin abubuwan da muka tanadawar Fatima, in sha Allah ba zata taba dana sanin amincewa da dan mu Muhammad ba.

” Dan sarki jikan sarki kuma sarkin gobe idan me dukka ya kaimu.”

 Wata mata tace daga gefe, duk suka amsa da in sha Allah.

  Guda aka saka a wajen, gudar da Mama taji kamar an saka allura ne ana chacchaka mata a tsakiyar kanta, kokarin sakin box din hannun nata take, wata kanwar su Abba da take lura da ita tuntuni ta taso da sauri ta karbe tana ma yan uwan Maman kallon banza. 

“Masha ALLAH, lallai mun ga Halin Girma da karamci na wannan babban gida, mun kuma tabbatar da yar mu ta shiga hannu na gari”

Ta fad’a bayan ta koma wajen zaman ta, ta kuma mikawa wata babba a dangin box din. Murmushi matan sukayi dukka, sannan aunty Faty tace

” Sai a bude kayan ko?”

Da karfin guiwar su dangin Abba suka tashi, aka fara bud’e box din farkon nan, kowa ya shiga mamaki, mukullaye ne wajen guda uku na mota, sai mukullin gida da takardun su, sai kuma wani babban set of gold masu girman gaske. Wata irin guda da tafi ta dazu aka sake saki, jira ya soma dibar Mama, ta kasa gane komai sai hajijiya da take ji kamar zata kayar da ita daga zaunen da take, me yake faruwa? Me yake shirin faruwa. 

   Daya bayan daya aka dinga bud’e kayan, tun mutane na irgawa har kowa ma ya gaji aka zuba ido ana kallon tarin dukiya, dukiya me sunan dukiya, dangin Abba da Mama ta dinga dagawa kai sai suka zama kamar sune kawai a wajen, farin ciki suke dama kowa yaji haushin abinda Maman tayi a dan tsakanin gabatowar bikin, sai kuma yadda ta dinga yada habaici a ranar da za’a kawo kayan wanda suka tabbatar dasu take shiyasa suka ji haushin ta sosai, amma yanzu da haka ta faru sai suka hau murna suka dinga yin abu da gayya dan su kara haukata Maman.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button