HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 41-45

“Je kace ya shigo wai.”

“Hankalin ki ya dawo jikinki kinji? Wannan rawar kan ta mecece? Anya ma yaron nan haka ya barki kuwa?”

“Mamaaaa.”

“Ba wasa nake ba, ki nutsu ki dawo nutsuwar ki wannan rawar kan babu abinda zata jawo miki sai raini wajen namiji, kayi biris da harkar namiji ma amma be fasa gasa ka ba, ina ga kana rawar kafa akansa? Daga cewa gashi sai ki mike kina barin jiki ke me miji ko? Toh ki shiga taitayin ki.”

“Mama ai ba laifi bane, tunda shi din miji na ne.”

“Inyeee Zeenatu?” 

Ta fad’a cike da mamakin Zeenat din, sallama yayi a kofar, kafin ya shigo sanye cikin shadda sabuwa kar, sai kyalli take da kamshi, cikin ido suka kalli juna da Mama, ta kauda kanta haushin shi na tike ta, sai ta ga ma kamar da gayya yake wani irin murmushi.

” Mama ana gaishe ki.” Zeenat tace jin Maman bata amsa gaiswar Bashir din ba

” Lafiya lou, ya gida.” Harara ta watsa wa Zeenat din ta dauke kai kamar bata gani ba, sai ta tashi tsam ta tayi hanyar barin wajen tace

” Ku gaida gida.”

” Mun gode Mama

Yace yana hayewa kujerar, tashi Zeenat tayi tabi bayanta dan yi mata sallama, ya bita da kallo yana kara bararrajewa a saman kujerar.

   Suna shiga Mama ta turnuke ta da fad’a, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, tayi mata tatas saboda bakin ciki, karshe tace ta bata waje. Sallama tayi mata bata amsa ba, sai ta tsaya taki tafiya tana kallon Maman

” Uban me kika tsaya kina yi anan? Ko jiranki zai yi? ”

” Naga kina fushi ne, kiyi hakuri dan Allah ko na hakura da tafiyar kawai tunda naga kamar bakya so. ”

” Inji uban wa nace bana so? Yadda ma kike rawar kafar nan ko bana so zaki hakura ne? ”

” Eh. ” Ta daga mata kai

” Ke ni karki rainan hankali, wuce kibi mijinki Allah ya bada zaman lafiya. ”

” Amin. ” Ta amsa hakan ya sake tike Maman. Ta juyar da kanta sai da Zeenat din ta fita sannan ta zauna cikin rashin sanin abinda kuma ya kamata tayi. Gashi dai a karshe abinda tayi ta yi akan Zeenat din duk ya tashi a banza, gashi ta rasa damar ta a wajen Abba wanda ba zata taba dawowa ba, karshe kuma yar ta zabi mijinta akan zaman gidan nasu.

   

***Da dan gudun Amaani da Amaan suka tare shi, kamar sun sanshi tun da dadewa, kamar sun saba dashi. Yana da son yara ko dan saboda be haifa da yawa bane, Amaani sak Fatiman sa sai dai ita bata da hayaniya da kwarafniya irin ta Amaani din, kamar yadda mahaifiyar su take haka take itama a nutse tun tana karama har kuma girman ta.

  Su suka jagorance shi zuwa ciki, ya zauna yana tuna shekarun baya da ya kasance a same wajen, a lokacin da yazo su kayi magana da Alhaji, kamar a lokacin komai yake faruwa. 

   Turo kofar da akayi ne ya sakashi waigawa, itace dai a shekarun baya sai dai girma da ya soma kamata, duk da haka ba zaka taba bata shekarun ta ba, balle har ka kawo ta ajiye budurwa kamar Iman din, kullum cikin gyara take tsaf. Ko a baya yasan yayi missing mace kamar ta, sai dai a yanzu sam be zo da wasa ba, da gaske yake wannan karon sai dai duk abinda zai faru ya faru. Babu gudu ba ja da baya!

“Sannu da zuwa.” Tace tana zama a chan nesa da kujerar da yake kai. Sannan ta gaishe shi ya amsa yana satar kallon ta, shiru suka dan yi kafin ya sake bijiro mata da maganar da ta sakashi tasowa gari i gari zuwa Abujan, a tsammanin sa sai sun kai ruwa rana zata amince, amma sai ta bashi mamaki matuka, yadda kai tsaye tace Allah ya zaba musu mafi alkhairi. Da farin ciki ya baro garin na Abuja, ya dawo ya tarar da Mama bata da lafiya, ya tausaya mata tunda shi mutum ne me tausayi, har ma ya saka Habib suka kaita asibiti in da aka ce dole ta rage tunani saboda jinin ta da ya hau sosai, aka rubuto mata magunguna suka tattaro suka dawo gida.

***Bayan sun gama waya da daddare zasuyi sallama yace ta shirye shi gobe yana nan dawowa, reaction dinta kadai ya gamsar dashi yadda tayi kewar shi. Yana jin yadda take farin ciki ta cikin wayar sai dai kara irin tata ta hana ta nuna masa, a hakan ma ya gode dan yasan ya chanja ta sosai daga auren su zuwa yanzu. Sauran chanjin kuma sai a hankali zata saba da kalolin soyayyar sa masu tsayawa a zuciya.

   Neman baccin da take yi tayi ta rasa, ta tashi ta sauka daga gadon ta bud’e wardrobe dinta, ta hau duba kayan da take ganin ya dace ta saka, sai data dau lokaci tana zaba kafin ta tsaya akan wani hadadden lace wanda dinkin sa ya fita sosai. Murmushi tayi ta fito dashi ta ajiye a gefe ta hada da set of jewelries da zasu dace da lace din sannan ta kwanta tana lissafa kalolin girke-girken da ya kamata ta tarbi mijin nata dashi, da haka bacci ya dauke ta bayan ta gama hada komai a cikin kanta saura kawai girkawa gobe idan Allah ya kaimu.

   Kasancewar tana cikin zumudin dawowar sa yasa ta tashi da wurwuri, ta duba kitchen na abubuwan da zata bukata wajen girkin wanda babu ta bawa Ummimi sautu suka je da driver suka sissiyo, sannan suka shiga aikin tare da sauran ma’aikatan dake kula da kitchen din amma kuma Itace akan girkin sai dai su taimaka mata da dauko wa da mikowa.

2/26/22, 19:09 – Buhainat: *Hafsat Rano*

      _Halin Girma_

            *44*

***Da wurwuri yaso tahowa amma sai case din Kamal da Kilishi ya tsaida shi, sosai Kamal ya tada hankali a gidan tun bayan da ya tantance ainihin shi din waye, ya kuma gano wambai ne Mahaifin sa. Baki daya Kilishi ta nemi kwanciyar hankalin ta ta rasa, gashi har lokacin bubu be ce ga hukuncin ta ba, sannan ita kanta Laila ta birkice mata, babu Moh kamar yadda ta kwallafa rai, ga bakin cikin cin amanar da Samha tayi mata ga kuma abinda mahaifiyar ta wa mahaifin ta.

   Takanas taje ta samu Bubu ta roke shi akan ya barta ta koma karatun ta dan zaman ta anan din komai zai iya faruwa,da farko be amince ba sam, yace mata be yarda ba tayi hakuri ta kawo miji aure zai mata. Sanin bata da wani tsayayye da zata nuna yau yasa ta samu Moh ta roke shi cikin kwantar da kai tace ya rokar mata Bubun ya barta. Ko da ya samu Bubun da magana shima fafur yaki, sai da yayi ta masa magiya sannan yayi masa alkwarin duk wani abu da ya faru shine zai dauki responsibility din, a haka yayi convincing Bubun ya amince yace ta koma din,amma da sharadin idan yaji wani abu mara dadi ko mara kyau toh fa shi zai kama da laifi kuma dole ya karbi aurenta. 

    Godiya tayi ta zuba masa kamar ta rungume shi haka take ji, har gobe tana son sa, ba kuma ztaa daina son nashi ba, zatai ta hakura for now tayi concentrating akan karatun ta, ta samo ta kammala shi kafin tasan kuma me ya kamata tayi kuma anan gaba. Akalla idan tayi nisa da gida zata manta abinda Kilishin tayi da dan lokaci ta kuma samu damar mantawa da Moh din shima na wani lokaci hankalin ta ya kwanta ta nutsu waje daya.

   

***A daki ya tarar da Ammin tasa, wanka tayi ta gama shiryawa kenan zata fito ta yi breakfast ya shigo, ta bishi da kallo har ya zauna a k’asa wajen tumtum din da take hutawa idan tana dakin, ya tankwashe kafafuwan sa sannan ya gaishe ta cike da ladafi. Kusa dashi ta zo ta zauna tana amsawa, tasan sallama yazo yayi mata tun jiya dama ya sanar da ita komawar tasa yau ba kuma zai dawo ba sai ya gama da chan din, sannan yazo a shiga bikin nad’in nasa, wanda tun yanzu Bubun ya soma aikewa da goron gayyata dan taro yake shiryawa na ban mamaki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button