HALIN GIRMA 41-45

“Tafiyar ce Babana?”
“Eh wallahi, na zata ma fa baki tashi ba.”
“Wa? Ka manta da wuri nake tashi, kwana biyu ne da kafa ta matsa min bana samun bacci sosai da daddare sai na rama da safe.”
Kafar tata ya matsa mata
” Har yanzu tana ciwon?”
” Ta warke yanzu ai.”
” Allah ya kara sauki.”
” Amin.”
” Idan naje sai mun tashi dawowa gaba daya, ina fatan abun da nayi ya dace.”
” Kayi abinda ya dace, kuma ka farantawa mahaifi ka da zaka cika masa burin sa, Allah yayi maka albarka ya baku zuria dayyiba, inaso na goya yan jikokina a bayan nan nawa.”
” Dukka ma zamu baki Ammi ta, halak malak. ”
” Um um dai Babana, kar kayi alkawarin da ba zaka cika ba. ”
” Da gaske nake Ammi. ”
“Toh shikenan Allah ya kawo mana masu Albarka. ”
” Amin ya Allah. ” Ya amsa yana mikewa
” Ammi zan wuce, ayi mana addu’a. ”
” Allah ya taimaka ya bada sa’a, a gaida min da yata kafin tazo, zan kira na sake dubata idan ka sauka. ”
” In sha Allah Ammi ta. ”
Bin sa tayi da kallo har ya bace wa ganin ta, ta sauke ajiyar zuciya tana jin soyayyar tilon dan nata, tana alfahari dashi, daya ne tamkar da dubu yana mata biyayya daida gwargwado.
Be samu ganin Bubu ba, dama sun riga sunyi sallama tun jiya, dan haka kai tsaye mota ya shiga, karo na farko zaiyi tafiya cikin rakiyar tarin fadawa ba sojoji ba, wani daban yaji, gargajiya sosai da al’adah irin ta gidan sarauta. Shi kansa shigar da yayi kenan, shiga irin ta Yarima me jiran gado, a dan kwana biyun da yayi har ya saba da saka kayan , yana kuma jin dadin su dan suna sake fito da kamalar sa.
Tun daga airport ya fara cin karo da abinda ya tsana da sarauta, yadda ake kokarin kaiwa kasa wajen gaishe shi, har ga Allah baya so kuma dole zai san yadda zai ya hana irin wannan gaisuwar. Basu jima da zuwa ba jirgin su ya tashi zuwa birnin na Kano, in da ya tanadi kalolin soyayyar da zai bajewa sahibar tashi, kafin ya dawo ya karbi sha’anin mulkin da baya jin zai rage masa wani abu daga cikin irin rayuwar da ya tsara musu, sai dai yasan dole sai ya dinga raba lokacin da mutane, amma haka zai yakice ya dinga yin abinda ya dace.
***Tun da taga komai ya gama haduwa sai abinda ba za’a rasa ba, sai ta bar musu sauran aikin su karasa ita kuma ta haye sama don yin wanka ta shirya tarban mijinta. So take ta burge shi sosai, duk da ita din ba gwanar kwalliya bace amma zata kokarta, sannan zata cire kunya ta rungume mijinta taji dumin jikin sa sosai.
Wanka tayi ta sake wanke bakin ta tas, sannan tayi amfani da mouth freshner me kamshi ta kuskure bakin sannan ta fito tayi zaman shiryawa a gaban mirror. Ta dan dau lokaci tana shiryawar duk da ba wani make up tayi ba, amma tayi kyau ainun. Kayanta da ta turara akan kabbasa ta dauko ta saka, sannan ta sake bin jikinta da turarurruka masu sanyi da dadin kamshi. Samun kanta tayi da yin murmushin yadda ta fito tayi fes, sai taga har wani fari kamar ta kara tayi fresh da ita.
Zama ta cigaba da yi a saman nata tana dakon zuwan sa. Waya ta dauko da nufin kiran Mummy sai taji karar zuge gate din gidan, ta fasa ta tashi da sauri tayi wajen window ta daga tana kallon motocin da ke shigowa suna samun matsuguni a cikin gidan. Motar da yake ciki ta zubawa ido, a hankali ya zuro kafarsa cikin takalmin sa da akayi da zallar fatar damisa, daga yanayin takalmin nasa ta gane irin shigar dake jikin sa, tun kafin ma ya gama fitowa ta gama wassafa yadda kayan suka karbe shi.
Kamar wanda aka ce ya daga kai zuwa saman, sukayi ido biyu tana leken sa, da sauri ta saki labulen sanda ya kashe mata ido daya gami da murmushin sa me tarin bayanai a cikin sa.
Gaban mirror ta koma ta sake fesa turare sannan ta shafa khumra me kamshi a tafin hannun ta, ta dauki flat shoe me kyau ta saka ta sauko k’asa. Tana saukowa yana shigowa falon. Tsayawa yayi a kofar ya toge ya bud’e mata hannayen sa, cikin sanyin ta, ta tafi zuwa gareshi, ta fad’a jikinsa ya rungume ta yana jujjuyasu a wajen, kamshin turaren ta na ratsa kofofin hancin sa.
“Ya Allah, ashe haka nayi kewar ki?”
“Um… Barka da zuwa yallabai.”
Tace tana dago kanta daga jikin sa
” Barka dai gimbiyar Muhammad.”
” Muje ciki?”
” Bismillah… Ladies first ”
ya matsa yana nuna mata hanya, yana so ya more kallon tafiyar ta. Bata kawo komai ba tayi gaba ya bita yana murmushi, a tsakiyar falon suka yada zango.
“Wash.” Yace yana taro ta jikin sa, ta zame tana masa dariya
“Wanka ko lunch?”
“You.” Ya kashe mata ido, dariya kawai tayi, ta je ta kawo masa lemon kwakwa da tayi masa yayi sanyi sosai ta zuba masa a glass cup ta dan russuna ta mika masa, ya hada da hannun ta ya rik’e tayi yar kara
“Auw, sorry baby.”
Ya saki hannun ta zame shi tana marairaice fuska kamar zatayi masa kuka.
“Sai na rama.”
Ta koma ta kawo kayan abincin ta jera masa a wajen, ya mik’a mata hannu ta daga shi, ta noke tana durkusawa da nufin zuba masa, rigar ta da akayi wa dinkin V-shape daga wuyan ya kalla yana cije lips dinsa.
“Bismillah.”
Tace tana dagowa, ga mamakin ta sai gani tayi ya zuba wa kirjin ta ido, kunya ce ta kamata ta daga da sauri, ya waske yana zamowa
“Kayan nan yayi miki kyau”
Kin kallon sa tayi, ya dauki spoon din ya fara cin abincin yana kunshe dariyar sa.
“Ya jikin naki?”
“Alhamdulillah, da sauki. Yasu su Ammi?”
“Lafiya lou, suna gaida ki, tace zata kira ma ta sake duba ki kafin muje.”
” Ayya, na samu sauki ma ai.”
” Naga alama ai, har wata kiba kika kara da kyau, musamman ta nan…”
Ya nuna chest dinta da idon sa, kau da kai tayi tana hararar sa
” Kai ko?”
” Me nayi? Daga fadar gaskia? Allah baki gani ba.”
” Uhummm.”
” Da gaske fa nake, komai masha Allah.”
Murmushi kawai tayi, dan ta lura jan magana yake so yayi, aikuwa ya cigaba da yi zuzutawa kyaun da tayi. Ita ma kanta tasan tayi kara wani irin kyau na ban mamaki. Sai da ya gama tas ya shanye lemon kwakwar nan sannan ya kama hannun ta suka haye saman, su Ummimi suka zo suka tattare wajen suka gyara aka saka turaren wuta.
Manage muna biki ne
2/27/22, 23:33 – Buhainat: *Hafsat Rano*
_Halin Girma_
*45*
***Washegari suka tashi cikin farin ciki da annushuwa. Yana shiryawa a gaban mirror ya kalle ta ta cikin mirror din tana ajiye masa kayan da zai saka yace
“Maganar school dinki, transfer zamu nema zuwa adamawa.”
Tsayawa tayi da abinda take ta kalle shi
“Komawa zamuyi chan?”
“Yes, zamu koma gida, zan ajiye aiki na, na karbi Bubu.”
Wani gingirim taji maganar, ta tsaya a wajen sakato tana son ta fuskanci zancen. Gabanta yazo ya tsaya yana murmushi
“Kina mamaki?”
“A’ah, ban gane bane I’m confused.”
Dariya ya saka
“Don’t be, ki shirya you are soon to be the wife of his royal highness!”
Wani shock tayi cike da mamakin
“Zaka karbi mulki?”
“In sha Allah, shine burin Bubu, zan cika masa burin sa kamar yadda yake so.”
Da baya ta koma ta zauna a gadon kanta na mata wani iri. Matar sarki fa? Ta Yaya zata iya? Taya zata fara? Bayan bata san komai cikin sha’anin irin wannan ba, dafa ta yayi ya mik’ar da ita tsaya yana mata dariya
“Look at you, bafa yaki bane, normal ne kawai.”
“Bansan komai ba ai, ta yaya zan fara? I’m nervous.”
” Karki damu kinji? Muna tare ai.”
” Allah ya taimaka ya bamu sa’a, Allah ya bamu ikon yin adalci da aikata daidai.”