JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 35

dinsa, yyi rub da ciki saman gado…. Sae wajen takwas da minti goma Ahmad ya bar gidan bayan ya ga Abuturrab yayi bacci. Sha biyu da rabi na rana Ahmad ya dawo gidan ya tadda Abuturrab yana bacci har sannan, ya ajiye masa ledan takeaway din abincin da ya kawo masa, ya karasa yana kallonsa da kyau, lkci daya Abuturrab ya bude ido, ya dafe forehead dinsa yace “What’s the time, our flight is…” Da sauri ya mike xaune yace “Karfe nawa?” Ahmad ya rungume hannu yace “This is after 12” Abuturrab ya xaro ido yace “What????” Tashi yyi daga kan gadon yaji wani jiri ya

debesa ya koma, Ahmad yace “Look, don’t deceive ur self nd ur Airline Captain, ka tura masu text yanxu cewar baka da lafiya” Abuturrab yace “Ni nace maka bani da….” Rike cikinsa yyi da sauri, yace “I feel like throwing up” Ahmad ya karasa ya bude masa bandakin, da kyar Abuturrab ya tashi ya shiga bathroom din. Karfe shidda suka iso train station na rigasa, Salem na cikin mota yana jiransu, Ahmad ya bude front seat ya shiga, Abuturrab ya xauna bayan motar ya jinginar da kansa da seat, Salem na kallonsa ta madubi yace “How are you feeling now?” Abuturrab yace “Alhmdlh” Salem ya gaisa da Ahmad sannan ya tada motar suka bar station

din. Da magrib Aunty na tsaye kan Abuturrab dake kwance saman gadonsa with drip, tace “Ko wannan aikin naka ai ya isa yyi weighing dinka down, aiki babu hutu kullum mutum na sararin samaniya” Shi dai bai ce mata komai ba, tace “Toh Allah ya sauwake” daga haka ta juya ta nufi kofa ta fita, Aisha ce ta shigo dakin da cup din shayi ta ajiye masa tace “Ya jikin yaya?” Yace “Ummi fa?” Tace “Tana can daki” bai kuma cewa komai ba ta ajiye shayin ta fita. Umma ce xaune parlor tana kallon Ahmad da bai jima da shigowa gidsn ba, tace “Toh ya jikin nasa yanxu?” Ahmad yace “A’a da sauki nayi masa allurori kuma na sa masa drip” Umma tace “Ikon Allah, kuma yaya bata gaya min ba wllh, bari in kirata” Wayarta ta dauka ta

shiga kiran yayarta, Bude kofar parlon aka yi Jiddah ta shigo da sallama rike da qur’ani da takardunta, Ahmad ya amsa, ta karasa parlon ta duka kasan carpet a hankali tace “Ina yini?” Yace “Lafiya lau Jiddah, har kun gama karatun?” Tace “Eh, ya Aunty Ramlah?” Yace “Tana can gida ai, baku je bane?” Tayi murmushi tace “Aa bamu je ba” Umma tayi ma Ummi sallama bayan ta daga wayar, suka gaisa sannan tace “Yaya ashe Aliyu bai ji dadi ba” Ummi tace “Ehh haka aka ce min” Umma ta kalli Ahmad tace “Wai dama ba can gida yake ba?” Ahmad yace “Can yake” Umma tace “Toh baki shiga kin dubasa bane Yaya?” Ummi tace “Aa masu dubasa dai nayi, ni yace min bashi

da lafiya ne?” Umma tace “Aa yaya ai rashin lafiya daban ne, da kin shiga kin dubasa ai, nima ynxu Ahmad ke gaya min shi ya taho da shi daga Abuja ma” Ummi tace “Allah ya kara mana lafiya gaba daya” Umma ta d’an yi shiru sae kuma tace “Toh Ameen” sallama suka yi ta ajiye wayar, Umma ta kalli agogo dake nuna biyar da rabi sannan ta kalli Jiddah tace “Malamar ta tafi ne?” Jiddah tace “Ehh ta tafi” Wayar Umma ya fara ring ganin Ummi ke kiranta ta dau wayar ta mike ta wuce cikin daki, Ahmad na kallon Jiddah yace “Hope baki bukatar wani abu yanxu?” Ta girgixa kai tace “Aa ba komai” Yace “To ya karatun?” Tace “Alhmdlh” Yace “Kina dai ganewa sosai ae” Murmushi kawai tayi tace “Ina ganewa” yace “Toh ki dinga maida

hankali sosai pls kin ji?” Ta gyada masa kai, a hankali tace “Ina son in tambayeka wani abu” yana kallonta attentively yace “Toh ina jin ki Jiddah” Ta sunkuyar da kanta tace “Don Allah xaka iya kai ni can gidanmu in ga Baabarmu?” Sake baki yayi yana kallonta, can yace “Me xa kiyi ma baabar taku?” Cikin sanyin murya tace “Ina son xuwa in gaisheta” Ahmad ya girgixa kai yace “ko xaki je ba yanxu ba tukun Jiddah….” Tayi kasa da murya tace “To akwai wata Iyah a layinmu, tana min kirki sosai, baxan iya xuwa gaisheta ba ita?” Da mamaki Ahmad ke kallonta, can dai yace “A layin baabar taku?” Ta sunkuyar da kanta, Murmushi kawai yayi ya rasa abinda xai ce mata… Umma ce ta shigo parlon, tana kallon Ahmad tace “Idan anyi magrib sai ka kai ni can gidan in duba Aliyun” Ahmad yace “Toh Allah ya kai mu” kitchen ta wuce, Jiddah na kallonsa tace “Bashi da lafiya ne?”

Ahmad yace “Ehh amma da sauki” Tana kallonsa tace “Nima xan iya bin ku in gaishesa da jiki?” Ahmad yace “Sai yanda Umma tace” Bata kuma cewa komai ba, bayan few seconds ta kallesa taga kallonta yake, murmushi ya sakar mata, ta sunkuyar da kanta tana murmushin ita ma sannan ta mike tace “Xan kai kayan karatuna daki” Yace “Toh Jiddah” Tana fadin haka ta yi hanyar dakinsu. Da magrib kamar yanda Umma tace ta shirya don xuwa duba Abuturrab tare da Ahmad, Jiddah ta rasa ta yanda xata ce mata ita ma tana son xuwa ta dubasa, ganin Ahmad ya fita kafin Umma ya fito ta bi sa da sauri ta riskesa a waje tace “Yaya don Allah xaka tayani gaya ma Umma, ni ina jin tsoro” Ya wara ido yace “Aa nima ba ruwana sai dai ki gaya mata

da kanki” Jikinta yayi sanyi, a hankali tace “Toh” sannan ta juya ta koma cikin gidan, Umma ta fito parlor da hijab da jakarta tana kallonsu Maimoon dake parlon tace “Kar dai ku bar ruwa ya cika yyi ta xubewa….” Maimoon tace “Umma ni ma xata da mu xa ku je mu duba yayan muma?” Umma tace “Ba cewa kika yi kina da Hadda ba” Maimoon tace “Toh shkkn sai kun dawo” Safiyya dai na xaune tana danna wayarta, Umma ta nufi kofa Jiddah ta bi ta da kallo, a hankali tace “Umma sai kun dawo” Umma tace “Yauwa, kema kiyi karatun ki duk da dai ba kallo kike ba na sani” Jiddah bata ce komai ba har Umma ta fita parlon… Umma na shiga mota Ahmad ya kalleta yace “Umma na xata da su xa mu je can gidan su duba Aliyun, daxu Mumy ta

tambayeni nace xan taho da su….” Umma tace “Toh ai ni baka gaya min ba, kuma sai a bar Huraira ita kadai a gidan?” Ahmad yace “Toh shkkn” Xai tada motar Umma tace “Bari su fito din dai” Wayar Safiyya Umma fa kira, tana dagawa tace “Safiyya wai yayanku ku fito mu tafi tare” Tana fadin haka ta katse wayar, Tun da suka fito outside gate din Ahmad ke kallon Jiddah sai dai ba ga expression da yake expecting gani a fuskarta ba, ita da Maimoon suka shiga bayan motar sannna Ahmad ya kunna motar suka bar layin…. A kofa gida yayi parking, Safiyya ta sauka sannan jiddah ma ta sauka, su Umma ma suka sauka duk suka shiga gidan, Ummi ce xaune parlor

tare da Hajja, Hajja na cewa “Tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin irin haka ba wllh sai a kanki…” Sai kuma tayi shiru tana amsa sallaman Umma, Umma tace “Sannu Hajja” Hajja tace “Yauwa sannu, sai kika ji Aliyu ba lafiya ko?” Umma tace “Eh wllh” Hajja tace “Toh mu ma haka muka ji, ashe wannan yaro Ahmad ne ya tafi ya dauko sa a Habuja rai a hannun Allah, ni dai dama nace wannan halin da ya tsiro ma kansa ba halinsa bane, ashe bashi da lafiya ne bawan Allah” Umma tace “Allah dai ya basa lafiya, yana dakinsa ne?” Hajja tace “Ehh yana can an kara masa ruwa, kai har makota babu wanda bai shigo dubasa ba amma uwarsa ta ki shiga ban san dalili ba” Umma dai bata ce komai ba ta yi hanyar dakin Abuturrab, yana xaune

hannunsa rike da bowl din farfesun hanta, Aunty ma na xaune dakin tana cewa “Idan ka ci wllh xaka ji dadin bakinka, sannan kar kaji komai ni da kaina na maka sai da na tsaftace shi” Aunty tace “Aa sannu da xuwa Hajiya Ramlah” Umma tace “Yauwa sannu ya mai jiki?” Aunty tace “Aa yaji sauki wllh, ai da ma baku wahalar da kanku kun fito ba, jiki ai da sauki sosai” Umma na kallonta tace “Xuwa duba d’an nawa ne wahal da kai?” Aunty tace “Aa wai naga dare yayi ne ai…” Umma tace “To ba wahal da kai bane, d’a na ne halaq malaq” Aunty dai bata ce komai ba, Umma na kallonsa tace “How are you feeling now” Ya sunkuyar da kansa yace “Alhmdlh da sauki” Aunty tace “Nace maki ai da sauki” Umma ta kalleta tace “Naga shi ma yana da

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button