NOVELSUncategorized

TARAYYA 17-18

Page 17
Jikinta har rawa yakeyi gurin zuwa tasanarda mamani,
Da ace bawa nada ikon gudu Dan karan kansa ba sakasa akayi

to yau da bazata tafiyaba gudu zatayi domin ta isa gurin mamani da wuri tafada mata kyakkyawar rayuwarda tayiwa rumanah qwanqwasa. +

Tana isa babban kicin din ta sake nutsuwa Cikin girmamawa take gaida masu kula da bayin sakewa masarauta girki harta isa gaban mamani dake kwashe farfesun wani qatoton kifi ahankali sbd karya wargaje ahaka ake dorasa cikin inda za’a kaisa,
Murya qasa qasa cikin tsananin farin ciki tace, 1
Mamani a yau sultana ta ‘yanta ummu-rumanah sbd aurawa yarima maheer ita ataqaicema an ‘daura au…….. 1
Cak mamani ta kafe idonta akan fuskar nuratu ‘din babu alamar motsi atareda ita
Cikeda tsoro ta ta6ata tace,
Maman……..bata qaraba taga ta yanke jiki ta fadi cikin tsananin tsoro da fargaba takira sunanta da qarfi Wanda yasa masu kula dasu qarasowa da sauri suna tambayar abinda yasameta. 5
Girgiza kai nuratu tayi idanuwanta na cikowa da hawaye sai dai batasan mezataceba Dan tasan tsabar hassadace ta sumar da mamani. 12
Ruwa akace nuratu ta ‘debo sbd rikicewa ta ciko silver da ruwan masu tsananin zafi tana qarasowa ta zuba matasu amatuqar gigice mamani ta saki wahalalliyar ajiyar zuciya tareda bude ido ta tashi zaune jikinta na wani irin sililin zafi ta ‘dago ahankali tana kallon nuratu ta tuno da abinda tafada mata wani irin kuka ne ya kufce mata hadda shesheka ita shikenan rumanah ta mayar mata da burinta mafarki,
Ita sai yaushene bulama da iyalinsa zasu bari taringa samun abinda take burin samu,
Rumanah tasan duk burinta akan nuratu ne tasamu wannan matsayin amma ta shiga tsakaninta da burinta. 4
Wani sabon kuka tafashe dashi tareda miqewa tana qoqarin cigaba da aikinta sililin jikinma tuni baqin ciki yasa batajinsa ko kadan.
Saidai ita mamani kutti ayau tana rantsuwa dasai ta raba rumanah da duk wani farin ciki dazai shigo rayuwarta kamar yanda iyayenta su asma’u suka rabota da farin cikinta,
Hakama tayi alqawarin shiga tsananin ummu-rumanah da duk wani burinta kamar yanda ta rabata danata. 7
Jiki amatuqar sanyaye nuratu ta juya tabar sashen kicin din tana tunanin tabbas mamani bazata bari azauna lafiyaba saidai dukda tana mahaifiyarta bazata ta6a bari ta cutatarda ummu-rumanah ba koda hakan na nufin zasu raba hanya ne. 1
Cikin wani irin yanayi yashigo part din na sultana tareda Jakadiya dake biye dashi daukeda sadakin rumanah ‘din fuskar yalwace da farin ciki.
Suna shigowa dukkanin wainda ke palon suka miqe banda sultana da rumanah dake zaune cikin lullubi.
Tsayawa yayi batareda yakalli inda takeba
Ganin haka yasa sultana miqewa tsaye tareda riqo rumanah ta tayarda ita ahankali takawota gabansa suna fuskantar juna
Tanajin yanda dukkanin jikin rumanah yake rawa haka ta saketa tareda saka hannu ta yaye mata lullubin. 1
Kamar bazai kalli fuskarta ba ya bude fararen oily eyes dinsa akanta,
Karo na farko daya kalli wata mace a duniya yaji gabansa yayi mummunan bugawa ya ‘dauke idanuwansa ahankali cikin rashin kulawa yayi Jakadiya wani kallo a hanxarce ta matso tareda miqawa ummu-rumanah tray dinda yake daukeda sadakinta cikin tsananin girmamawa tace, 1
Allah yataimaki amarya ummu-rumanah ga sadakinki Allah yayiwa aure albarka. 1
Hannuwanta dake cikeda awarwaro da zobunan zinari ta ‘dago yana rawa sosai ta karbi tray din har lokacin kanta na qasa bata dago takalli kowaba.
Sultana ta miqawa tray din batareda tace komaiba sbd bazata iya maganaba itadai duk yanda sukazo haka zata bisu sbd tasan wannan shine fate dinta.
Karba sultana tayi tareda sakin murmushin qarfin hali tace,
STORY CONTINUES BELOW
Allah yayiwa aure da rayuwaki albarka ummu-rumanah bulama.
Mayar mata da lullubinta akayi suka dunguma zuwa gurin sultan .
Acikin dubban taro aka gabatarda ummu-rumanah bulama amatsayin sabuwar matar yarima.
Jama’ar gari da wasu masarautun sun jinjina kyawu irin na ummu-rumanah sbd ayanda tarihin sarakunansu yake zuwar musu shigowar mace mai tsananin kyawu a cikin zuriar sarauta baya zamtowa alkhairi.
Ana gama gabatarwa aka mayarda rumanah gefenta tareda sabbin bayi da kuyangi goma.
Bayan angama shagalin sultana ta shirya dukkanin kayanta tareda sa jakadiya tasa ayi mata booking ticket na flight dinda zai tashi da dare zuwa Libya.
Wanka yayi yashirya cikin fararen qananan kaya transparent marasa nauyi shiyasa mur’dadden jikinsa yake kusan a bayyane sbd shi Sam bayajin damuwar komai sbd auren bai sakasa akansaba sbd yasan bazai ta6a takura kansa ya canza sbd waniba, baya buqatar wata mace arayuwarsa bayan suhailat so bayajin yanada wani  lokacin 6atawa gurin zama yana yiwa mata ciki saikace wani injin. 5
Damuwarsa ‘dayace barin sultana masarautar zai ta6a martabarta da qimarta a idanuwan mutanan da mineelik ke mulki dakuma mutanen masarautar mahaifinta.
Kwanciya yayi tareda lumshe ido.
Suhailat kwananta biyu bata fito part dintaba sbd nauyin ciki dakuma rashin son kusanta kanta da duk inda zataga ummu-rumanah kokuma zancenta sbd batason kishinta yafi qarfinta qarshe tayi abinda zata zubarwa kanta mutumci tabarwa kanta da ‘yayanta abin fa’da gashi maheer ma anyi mata iyaka da ganinsa sai baiwarsa tasamu ciki shiyasa ta kama kanta a part dinta tasamu ta haihu ta tattara takoma Georgia ko zata samu hankalinta yadan kwanta. 2
Zaune take a palo tana waya da mum ‘dinta cikin sanyin murya tace,
Mum inason nazo gida na haihu agurinku sbd nasan anan ne nida abinda zan Haifa zamu samu soyayya da qaunar yanda muke buqata….
Cikin rarrashi mum dinta tace,
Suhailat my dear kiyi hkr tunda kinsan a inda kike aure,
Idan kin haihu I promise to come by Allah’s grace my dear,
Kicire damuwa da tunanin komai sbd condition you’re in.,
Wen is your edd???
Saura sati hudu.
Ok akwai sauran time ma ashe?
Yes mum,
Mum can you just give me a minute I will call you back someone is here.
Aje wayar tayi tareda kallon Jakadiya data shigo daukeda kaya batai maganaba tagyara zamanta tana jiran jin mai zata fada.
Kai tsaye jakadiya tace,
Saqon tausar zuciya ne daga sultana na aure da yarima maheer yaqara ayau Allah ya sanyaya zuciyarki.
Kasa motsi tayi sai ido data kafe Jakadiya dashi,
Wani irin radadi da ciwo ya ziyarci zuciyarta da mararta alokaci ‘daya
Rintse idanuwanta tayi da sauri hawayen dasuka cikasu suka gangaro tayi saurin dafe mararta tareda fara qoqarin tashi sbd jin danshi nabin qafafunta.
Jakadiya ganin halinda tashiga da jinin dake gangarowa daga qafafunta yasa tayi saurin qarasawa gareta daidai lokacinda azaba da ciwon suka taso gadan gadan tasaki wani irin kukan azaba tana dafe cikinta sbd jin axabarda bata taba jiba gurin haihuwa.
Ganin abin yayi muni sosai yasa Jakadiya bada umarnin aje atahoda masu karbar haihuwa sbd tanasa ran qila haihuwarce.
A gaggauce aka kirawosu suka kamata aka shiga daki da ita nan Jakadiya taje ta sanarda sultana
Cikin qanqanin lokaci masarauta ta ‘dauka labarin haihuwar da za’ayi saidai kuma masu karbar haihuwar sunkasa sbd jini take fiddawa har lokacin ruwan haihuwarta basu fasheba gashi tafara fita hayyacinta. 5
Cikin gaggawa jakadiya taje tasanarda sultan abinda masu karbar haihuwa sukace na za’a iya rasa ran suhailat da abinda yake cikinta.
Jin haka sultan dayace kar asanarda yarima sbd karyaqi tarewa da rumanah yau amma jin za’a iya rasa abinda za’a haifa yasa yace asanarda yarima yayi gaggawar bata taimako sbd bayason arasa abinda ke cikin sbd basusan ko meneneba.
Lokacinda ya isa yaga halinda take ciki ransa yayi mummunan 6aci sbd ganin irin jinin data zubar sbd baqin ciki kai tsaye ya fitarda wayarsa yakira khaleefa kai tsaye yace,
Khaleefa ina buqatar tickets na jirgin dazai tashi acikin daren yau.
Yana kashewa ya matso gefenta ya zauna tareda riqo hannunta ya share mata zufa da handkerchief dinsa cikeda kulawa sbd ganin nata yana qara muni.
Fita yayi ya nufi part dinsa ya shirya luggages dinsa ya canza kaya.
Cikin qanqanin lokaci aka shiryasu amah.
Koda khaleefa yasanarda sultan buqatar maheer
Kallonsa sultan yayi yace,
Ka karbo musu ticket shida
Shida mahaifiyarsa da matansa tareda ‘yayansa.
Jin haka khaleefa yaje yayi yanda zaiyi ya karbo guda shida ‘din koda ya dawo harsun gama shiri tuni jakadiya taje bisaga umarnin sultan ta hadawa ummu-rumanah kaya cikin wasu kyawawan akwatina marasa girma sosai guda uku tasakata ta canza kaya zuwa doguwar Riga baqa suka fito.
Sam baisan abinda yake faruwa aka dauki suhailat dake kwance kamar gawa aka saka mota suka nufi airport.
Sultana da rumanah taredasu amah kuma suka shiga mota ‘daya suka Mara musu baya.
Suna isa Sam bai lurada rumanah ba aka dauki suhailat akai cikin jirgi da ita yabi bayansu sultana da yara tareda rumanah da jikinta ke sanyaye suka rufa masa baya.
Amatuqar sanyaye take sbd wannan shine karo na farko data taba fitowa daga cikin masarautar tun duk tsawon rayuwarta.
Ganin yanayin suhailat dakuma ummu-rumanah yasa sultana yanke shawarar qin zuwa Libya binsu zatayi sbd batasan wani irin riqo su maheer din zasuyiwa rumanah idan basa ganin idon kowa duk da tasan ba ruwan maheer da ganin idon kowa akan alamarinsa.
Suna shiga jirgi a darare ta zauna kusada sultana tana kama jikinta kanta a sunkuye har jikin ya daga sama ta rintse idanuwa tareda  qanqame jikinta.
#mamuhgee
Page 18
Tun acikin jirgi aka fara bata taimakon gaggawa jinin ya tsaya amma Sam bata farfadoba koba’a fada masaba mmatsayinsa na likiti yasan ba lallaine abinda ke cikinta ya rayuba musamman dasuka duba cikin ya daina motsi,
Adduarsa da damuwarsa itace suhailat ta tsira koda za’a rasa babyn ne. +
Su amah dake taredasu sultana tuni sukai bacci
Sultana takalli rumanah da har lokacin bata iya gano yanayinda ta kar6i aurenta da maheer, farin cik kokuwa sabanin hakan saidai Sam yanayin sanyi na rumanar yakasa saka tagane yanayinta.
Cikin kulawa da sanyin murya takira sunanta.
‘Dagowa tayi takalleta tareda amsawa cikin sanyin murya kafin ta sunkuyar dakai.
Rumanah karki sakawa ranki sbd maraicinki da zamtowarki baiwa duk wannan abin yake faruwa dake
Jarabawar ubangiji ce dakuma qaddararsa Wanda tuni ya qaddaro miki hakan,
Na tabbarda Allah zai haskaka rayuwarki sbd kinrugumi qaddararsa da dangana.,
Ina taredake rumanah,ke amanace agurina bazan taba bari ki cutatuba matuqar inada zarafi da ikon hanawa,
Naso kubutar dake daga wannan rayuwar ta hanyar ‘yantaki sbd ki haramta ga yarima saidai bansan hakan zai qarasa hargitsa komaiba sai kuma Allah yayi yanda yakeso bamuda wani ikon hanawa saidai rumanah qaunar danake miki bazata sa nayi sonkai a wannan al’amariba
Yanxu ke ba baiwace kinada iko da ra’ayin kanki matuqar bakya son wannan auren nayi miki alqawarin zansaka maheer yasakeke zan mayardake masarautar iyayena ki rayu cikin aminci da kwanciyar hankali.
‘Dagowa tayi takalli sultana
Duk wannan alamarin hawaye ko ‘daya bai taho mataba sbd tariga ta rumgumi kome yazo da Wanda zaizo amma yanxu wasu irin hawayene suka ciko fararen idanuwanta takalli sultana ta sunkuyar dakai tareda rintse idanuwanta cikin sanyin murya tace,
Ta yaya zan bude bakina agabanki ammy nace banason zama acikin zuriarki,
Har abada ammy kece mai zartarda hukunci akaina nabisa koda ‘yanci koba ‘yanci bazan cewa aa ga duk hukuncinda zai fito daga bakinkiba,
Ni baiwace sai yanda akayi dani haryanxu ni baiwace agurinki banida zabi sai Wanda kuka zabarmin. 1
Lumshe ido sultana tayi cikeda tausayin rumanah batason takurata amma zasu bawa wannan auren dama basusan abinda Allah ya tanada acikinsaba.
Shiru suka sakeyi kowa da tunanin dayakeyi aransa.
Qarfe hudu na asuba suka isa,
Gida aka wuce da sultana da rumanah tareda yara shikuma maheer tuni motar asibinsa tazo sukai asibiti cikin gaggawa sbd yasan ma dole cs zasuyi mata.
Suna isa gidan sultana ta fito motar da kanta tasaka password na securityn gate ‘din gidan sbd tasani.
Shiga sukai driver yayi parking suka fita yashigar musu da luggage dinsu har first palon dake qasa kafin ya aje keys din motar ya wuce dama drivern dake kaisu amah school ne.
Da gudu su amah suka nufi bedroom dinsu bayan Mac driver yakira Carolina a waya yace sundawo tadawo itama tace gatanan zuwa shiyasa suke murna sbd sunason Carolina tana kula dasu sosai.
Lafiyayyan babban bedroom din dake gefen nasu amah sultana tace rumanah ta shiga kafin itama ta wuce Wanda yazamto kamar nata idan tazo.
Jan kayan sultana tayi tabita dasu tashigar mata har dakin ta ta ajesu kafin tafara qoqarin gyaran dakin sultana ta dakatarda ita da cewa,
Rumanah kibarshi kiyi sallah tukuna.
Ba musu tace to tareda ficewa taje dakinta
Kasancewar batada kwadayin babbar rayuwa yasa duk tsaruwa da haduwar dakin bata tsaya wani kalle kalleba ta shiga bathroom tayo alwala tana fitowa ta bude akwatinda takesaka ran zata samu abin sallah tasamo doguwar Riga da gyalanta ta nada ta fito taje dakin sultana taga inda take kallo tana sallah takoma ta tayarda sallah.
STORY CONTINUES BELOW
Bayan tagama ta cire rigar sallar ta zauna shiru tana qara bawa sultana lokaci kafin ta miqe takoma ‘dakinta tayi knocking ahankali kafin tabude tashiga cikin ladabi da girmamawa tace,
Ammy barka da safiya.
Kai kawai ta daga mata sbd gajiyar da rashin bacci dake tareda ita amma bata iya kwantawa matuqar ba gyara mata dakin akayiba aka canza bedsheets sbd ankwana biyu ba’a cikinsa duk da komai nanan lafiya klau ba’a cewama babu mutane acikinsa sbd babu ta inda iska zaishigo bare yayi qura.
Zanin gadon tafara yayewa daidai shigawar Carolina dakin nan ammy takalleta cikin turanci tace takawowa rumanah new bedsheets.
Da sauri ta karbi na hannunta data cire taje takawo wani fari qal sbd kusan gidan basu cika amfani da kowane kalar bedsheets ba kamar fari.
Karba tayi ta shimfida tafara gyaran dakin sbd Carolina taso karba tace tabarsa ita kanta sultana tafison aikin rumanah sbd itace kawai ke mata aiki yayi mata yanda takeso.
Tsaf tagyara dakin ta wanke toilet ta kunna AC da burner nan take dakin ya canza ta fice.
Tana fitowa taga Carolina nata aikin gyara koina an kunna duka ac ac da fridge fridge ta bude store ta debo ruwa da drinks ta jera ako wane frudge harna sama inda dakunansu maheer da suhailat suke
tuni gidan ya dauki sanyi da qamshi masu dadi
Itadai dakinta tashiga tayi wanka tasaka doguwar Riga baqa ta dawo ta zauna bakin gado tana jiran sultana takirata asata aiki sbd ita tafi sabawa da aikin wahalar Sam zama guri daya ko Hutu bata saba dashiba.
Sultana bayan takira maheer bata shiga itadasu amah bacci suka kwantayi cikin nutsuwa sbd agajiye suke sunsaba da Hutu su Sam jikinsu bayason gajiya.
A asibiti duk yanda sukaso ganin ta haihu da kanta abin ya gagara sbd taqi farfadowa duk wata allura sun mata har naquda suka qwaqwalo mata ta hanyar fasa mata ruwan haihuwa amma shiru shiyasa suka shiga emergency theater da ita kai tsaye sbd suna gap da rasata Dan tuni suka gano babyn ya dade da mutuwa.
Bashine yayi mata cs din ba doctor Edward yayi mata shiyasa haryasamu damar zuwa office dinsa yayi amfani da wayar office dinsa yakira sultana yasanarda ita halinda ake cikin.
Zama yayi tareda jingina bayansa jikin kujerar ya lumshe idanuwansa
Kwanakin nan he is in so much stress daga wannan sai wannan kansa har Sarawa yakeyi sbd baisaba da irin wainnan damuwarba.
Cikin ikon Allah anyi komai lafiya aka kaita dakin hutawa Dan har lokacin bata farfadoba,
Lokacinda duba gawar babyn saida yaji mumman faduwar gaba tareda dafe goshi kafin yasaki boyayyar ajiyar zuciya sbd ganin namiji ne,
Yana son duk abinda matarsa zata Haifa masa sbd jininsa ne saidai bazaiso ta haifi namiji ba yanxu sbd bazai iya bari uwar ‘yayansa ta fada cikin harkar sarautar mineelik ba shiyasa ya godewa Allah Dan shikadai ne yasan meyasa yayi hakan.
Saidayaga komai yadaidaita jiran farfadowar suhailat kawai akeyi ya nufo gida.
Driver yakira yazo yadaukesa.
Yana isowa babu kowa a palon qasa sai Carolina dake aikin girka abinci a kitchen yawuce sama kai tsaye.
Komai Carolina tagyara a saman tundaga bedroom dinsa harna suhailat da palonsu.
Tubewa yayi ya shige bathroom ya shiga bathtub dinda tuni Carolina ta hada masa ruwan wanka cikinsa masu zafi kasancewar ya dade baidawoba yasa suka zama masu ‘dumi.
Lumshe ido yayi sbd jin nutsuwa tafara jikarsa.
Ya jima kafin yayo wanka yafito ya shirya cikin kayan bacci masu laushi ya kwanta cikin gadonsa dake daukeda pillows masu laushi kusan guda takwas tareda shigewa duvet ya lumshe lazy eyes dinsa.
Sai qarfe goma sha ‘daya su ammy suka tashi nan kowa yayi wanka yafito palo breakfast.
Batareda sultana ta kalli Carolina tace taje takira rumanah.
Knocking qofar tayi kafin tashiga.
Kwance take amma ba bacci takeyiba tana ganin Carolina ta tashi zaune tana jiran jin mezata fada.
Sanarda ita tayi ana kiranta ta juya ta fita.
Saukowa tayi gadon ta gyara hular doguwar rigarta data zame sbd gashinta da baya daure ga tsancinsa ta nufi qofar ta fita.
A palon ta tararda sultana zaune cikin doguwar rigarta mai tsada kamar koyaushe saidai duka sarqoqin kai dana wuya na sarauta datake sawa ko yaushe acan nan babu ko daya ajikinta saidai sarqoqin qafarta da bata rabuwa dasu.
Sosai tayi kyau cikin simple shigar shiyasa rumanah tasaki fuskarta da wani qayataccen murmushi ganin kamar hankalin sultana din ya kwanta ta qaraso gabanta tareda durqusawa cikin girmamawa tace,
Barka da tashi ammy.
Itama murmushi tayi cikin sakewa tace,
Rumanah abinci zamuci nace kifito kuma kisaki jiki nan gidan mijinki ne su amah yanxu tamkar ‘yaya suke agareki saiki ringa kula dasu kema.
Girgixa kai kawai tayi kafin ta miqe ta nufi Carolina dake jera abinci a dining room tana zuwa ta sakar mata murmushi tareda karbar mata tray din samosas dake hannunta itakuma ta dauko sauran kayan suka nufi dining suka aje kafin taje tasanarda ammy angama komai.
Saidatayi serving ammy da duk abinda tasan tana breakfast dashi sbd ko acan itace tasan komai na abincin ammy.
Su amah kuwa Carolina ce tasan me sukeso ita tayi serving dinsu fammah ma abaki Carolina din ta tsaya tana bata sbd tasaba mum dinta ke feeding dinta idan tanan.
Harzata juya ammy tasata dawowa ta zauna a takure sbd rashin sabo acan tasaba layi sukebi abasu abinci suje susamu guri su zauna suci.
Cikin tsananin sanyi take cin abincin ammy na lureda ita takyaleta sbd tasan zata saba ahankali.
Itace tafara miqewa ta nufi hanyar kicin Dan taya Carolina gyaran kicin din dakuma girkin lunch.
Bayan su sultana sungama ita takwashe  komai tagyara gurin sbd itadai idanma batayi aikiba batajin dadin jikinta.
Sultana palo tazauna kallon wani Arabic progm yayinda su amah sukai dakinsu Dan kallon cartoon.
Bata gane maganar Carolina itama bata gane tata amma suna kwatanta ganewa ahaka suka fara aiki suna qoqarin sabawa da juna.
Sai qarfe ‘daya da rabi yatashi daga barci
Ya bude idanuwansa dake cikeda bacci ya kalli agogon gefen gadonsa yaga time ya lumshe ido  ya tashi zaune ya sauko gadon ya nufi toilet yayi brush yayo alwala yafito yayi sallah azahar yana gamawa ya tube harzai shiga wanka yadawo yayi amfani da wayar bedroom din yakira wayar palon qasa
Carolina dake kicin ta nunawa rumanah dake yanka fruits pancake dindata zuba ta fita da sauri.
Tana zuwa ta dauki wayar cikin girmamawa tace,
OK sir”””bayan tagama sauraran abinda yafada.
Aje wayar tayi harta juya sultana ta tambayeta abinda yace ta fada mata cewa yayi akai masa breakfast dinsa sama maida kallonta ga TV tayi tace takirawo mata rumanah.
Tana zuwa tace,
Ammy gani.
Rumanah ki hada breakfast a tray kikaiwa maheer sama.
Yawu ta hadiye ahankali tareda gyada kai ta wuce Dan hadawa.
Sanyi jikinta yayi amma ammy tafi qarfin komai agurinta,
Shirya komai tayi a tray mai kyau ta fito palon ammy ta nuna mata hanyar zuwa sama ta juya jikinta nafara rawa tana qoqarin saita kanta.
Harta fara hawa sultana tace,
Rumanahh.
Cak ta tsaya numfashinta na fita da sauri ta juyo.
Idan kinje karki tsaya palo kikai masa har cikin bedroom dinsa. 5
‘Daga kai tayi ahankali ta juya tacigaba da hawa.
#Mamuhgee.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button