Hausa Novels

Lu’u Lu’u 26

*26*

 

Suna kammalawa basu bi ta kan kwanukan ko gyara wurin ba suka koma kan gadon nan, tsakiyarshi suka haye suka tank’washe k’afafunsu hannayensu sark’e dana juna suna kallon juna, cikin nutsuwa da fara’a sarauniya Juman tace “Yanzu fad’a min, me kike son sani?”

Cikin nutsuwa tace “Mah, ina so nasan *wacece* ni?”

D’an murmushi tayi tace “Wacece ke kike tambaya Ayam?”

Jinjina kai tayi tace “E Mah, ina so na sani.”

Jinjina kai tayi ita ma ta nisa sannan tace “Ayam, ke ‘yata ce dana haifa a ciki na, kafin haihuwarki kuma malam Dhurani ya fad’a min ke mai baiwa ce da zaki zo bayan magabatan da suka shud’e masu irin baiwarki, na raini cikinki har na tsawon wata tara cike da kulawa da nuna miki k’auna, haka kuma mahaifinki na d’aya daga cikin wanda suka tayani kulawa da ke, haka muka ci gaba da rainonki har sanda cikinki ya isa haihuwa, saidai duk tattali da burin da muka ci na haihuwarki, haka ina ji ina gani sanda na haifeki ko wankan farko ba’a miki ba na mik’aki a hannun jakadiyata ta tafi dake.”

Da mamaki fal a fuskar Ayam tace”Me yasa Mah? Gashi dai a labarinki na fahimci Pah ma yana so na, amma kuma sai ake cewa wai yana son kasheni?”

Numfashi ta sauke a hankali tace “Ayam, lokacin da cikinki ya kai wata shida, wata ranar alhamis da ba zan tab’a mantawa ba jakadiyar sarki ta zo min da wata magana, lokacin da sarki mahaifinki yayi bak’i ta je sanar dashi, anan ta ji wata tattaunawarshi da malam Dhurani suna maganar cewa ke d’in da zaran an haifeki to su gaggauta kasheki, idan ya so sai su samu wata jaririyar su damk’a min a matsayin wacce na haifa, jin wannan labarin ya tayar min da hankali sosai, saidai ban k’aryata jakadiya ba saboda tsufanta da kuma wasu alamomin da suka dinga bayyana min a game da sarkin, wasu lokuta ya kan furta zancen zuci a gaba ya fad’i wata mummunar kalma a kanki, wasu lokuta kuma idan ya sha giyarsa cikin dare na nemi taimakonsa kan wani abu sai ya dinga fad’in *banzan cikina* yana surutai, hakan yasa na ci gaba da saka ido akan shi ina masa kallon biri yana min kallon ayaba.”

Nisawa tayi sannan ta d’ora da” Tunda na fara nak’udarki sarki Musail yake tsaye a kai na shi da malam Dhurani da wazirinsa Khatar, da k’yar ya fita ya bar likitar gidan nan da jakadiyarsa suka dinga taimaka min, k’arfe 11:59 na ji kukanki bayan k’akk’arfan nishin da nayi, wanda kukanki ya dira a kunnuwana tare da sautin bugawar agogo k’arfe 12:00 ta buga na sabuwar shekara, babban abinda ya firgita ni a lokacin shine yanda mahaifinki ya banko k’ofar d’akin yana son a dole a bashi ke ya rik’e, hakan ya k’ara tabbatar min da abinda nake zargi ya kuma tsorata ni sosai.”

Kallonta tayi ido cikin ido ta sake jinjina hannayen Ayam d’in dake hannayenta tace” Ayam, b’atanki ba shiryayyen abu bane kamar yanda kowa ke zato, a daidai wannan lokacin na rok’i jakadiyata Habbee data gudu dake zuwa wani wuri mai nisa, sannan na umarceta data nemi taimakon mijinta akan hakan, saida na kori jakadiyar sarki na c ta had’a min ruwa, lokacin likitar ma ta bar d’akin sannan na lallab’a Habbee, da k’yar ta amince dan abun bazata ya zo mata, bayan ta amince ne na samu damar mik’a mata ke bayan na sumbaceki, har zata bi ta wannan k’ofar da kike gani…”

Ta fad’a tare da nuna mata drower ta litattafai sannan ta d’ora da fad’in” K’ofar sirri ce a bayan nan d’in, wacce a d’akin sarki da iyalensa ake samunta saboda kaucewa farmakin magauta na bazata, to ta wannan hanyar Habbee ta fita dake a wannan daren bayan na d’aura miki wannan sark’ar wacce sarkin k’asar Khazira ne kawai ke d’aurawa wacce ya aura, sannan na bata kud’in da zasu kula da kansu har su kula da ke kanki ma, wannan ita ce Ayam d’in da kike son sanin wacece.”

A tare suka sauke numfashi inda Ayam idonta ke fitar da ruwa masu d’umi muryarta na rawa tace” Mah, kenan dai da gaske mahaifina yana neman rayuwata? To amma me yasa?”

Sakin hannunta d’aya tayi ta share mata hawayen da suka zubo tace” Kiyi hak’uri Ayam, haka ta ki k’addarar take, hak’ik’a a yanda komai ya fito mana mahaifinki yana son kasheni, kuma ba komai ya kawo hakan ba sai dan ci gaba da kasancewa a kujerar mulkinsa wacce babu komai a ciki sai tarin zalinci da tauye hakk’in jama’a.”

Marairaicewa tayi tace” To amma Mah ke ma kin yarda ina da wata baiwa wacce har mahaifina zai so kasheni saboda ita?”

Girgiza kai tayi tace “Ba zan ce komai ba a yanzu, saboda ban girma dake ba bare na fahimci me ce ce baiwarki, amma dai nasan akan haka mahaifinki ke neman rayuwarki.”

Kyab’e fuska tayi tace “To amma Mah, me yasa ba yar uwata bace aka haifa da baiwar nan? Tunda ita kuka fara haihuwa ko.”

Murmusawa tayi tace “Saboda ke ce ubangiji yake son gani a haka.”

A marairaice ta sake fad’in “Mah, su waye mutanen nan da suka fara fad’a min wacece ni?”

Da mamaki ita ma tace “Su wa kenan?”

Jim tayi alamar tana tunani sai kuma tace “Yawwa Bukhatir, sunansa Bukhatir a k’asar Egypt.”

Mamaki ne ya sake bayyana a fuskarta ta k’ank’ance idonta tace “Bukhatir ya had’u dake kenan?”

Jinjina kai tayi tace “E, wata safiya ce dana fito daga wanka saboda jin motsin da na ji, daga nan ban san me ya sake faruwa da ni ba tun buguna da akayi a kai sai bud’ar ido da nayi na ganni a gidansa.”

A hankali ta dinga gyad’a kanta alamar jinjina abun da kuma gamsuwa kafin tace” Tabbas zai iya aikata komai, fatana kawai Allah ya kareki daga sharrinsa.”

“Waye shi Mah?” Ta fad’a a sanyaye, d’an yak’e ta mata kafin tace “Ayam Bukhatir d’an uwana ne, mahaifina shi ne gaba da mahaifinsa, ni kad’ai ce ‘yar da suka haifa mace bayan shekarun da suka share a tare babu haihuwa, mahaifin Bukhatir mutumin kirki ne wanda mulkin yayansa baya gabansa, saidai Bukhatir tun yana k’arami yake sha’awar mulki, sanda suka haifeni sai ya yarda lallai idan na girma zan iya hawa kujerar mahaifina, saboda kuwa mu a wajenmu mace ma tana yin mulki sai idan bata buk’ata, bayan wani lokaci Bukhatir ya zo min da tayin soyayyarsa, amma ban karb’a ba saboda bai min ba, bana sha’awar mulki kuma bana son mai tsananin son mulki.”

Da mamaki Ayam tace” To Mah e yasa ya saceni ya kaini gidansa? Guduwa fa na yi bai sani ba, sanda na fahimci babu hankalin kowa a kai na na wa hadiman daya had’ani da su dabara na shige boot d’in motar bak’in da suka zo masa a lokacin.”

Girgiza kai tayi tace” A gaskiya ban sani ba, ban san dalilin da yasa ya saceki ba,saidai nasan lokacin da mahaifinki ya nemi aurena sun samu matsala har sukayi musayar yawu, watak’ila ko akan hakan yake son rama wani abu da aka masa.”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button