KUSKURE Complete Hausa Novel

NAWAL tace mama yarinyar Nan Tana neman kawo min raini kanwar bayana ,har Ni takema rashin kunya ,Ina fada Tana mayar min mama !?
Mama tace, hmmmm NAWAL ke Kika Fara Amman ko? Inba giyar wake Tasha ba yadda nasan ‘yan biyu b Fadi in fada tsakanin ku tun tuni ….
NAWAL t harareta tace ,mama wanan yarinyar dama duk dangin su b fitsarare kamarta ,shegiyar yarinya kawai haka take dama can wlh …
Mama tace ,a uzubillahi! Kar nasake ji kince d wani shege bare ‘yan biyu kalma mumuna Mara dadin ji haka? Kar kisake wlh inba hakaba zan Bata Miki wlh ….nasan ke Kika Fara kulata ….
Mama tace ‘yan biyu ku zauna meya faru?
Hassana zatayi mgn , ussaina t hanata d saurin bada ba’asi ,mama wlh tun shigowar gidan Nan tun daga salamar mu ,Taki amsawa sai d taga dama ,Bayan mun shigo ,ba kalon Arziki t barmu a tsaye Tana Mana wani kalon tuhuma ,hakan be Mata b t tmby mu Abun d y kawo mu cikin Iza ,ganin bamusamu fuska b muka Aiki Noor t kiraki ,shine tayi yunkurin Hana Noor din ,Nima n nuna ikona Akan Noor din t tafi kiranki ,shine Damme zan Hana Noor zuwa wajenta t zageni ,Ni Kuma dama b daga kafa kawai n Rama ,shine tacigaba d fadan maganganu daga baya ta daga hannu zata mareni ,natare sbd tsadar fuskata Dan Amarya nake Nan kusa ….
Mama sai d takusa dariya d mgn ussaina ,amnan t gimtse tace kinmin daidai Banga laifin ki ba ,ke Kuma NAWAL kici gaba d zubar d girma ,…
Bayan sun gaisa d mama ,mama tace NAWAL t kawo musu ruwa d lemu ,NAWAL t hararesu t amsa Amman mikewa t gagara ….
Ussaina tace ,mama ki barshi b sai d mukasha muka taho mungode d karamci mama ….
Sai hassana ta Mata bayani dama Noor suka kawo zatayi kwana biyu inji Yaya safwan g jayanta ,zamu koma …
NAWAL har ranta taji Dadi sosai Dan Haka t Dan saki Rai Amman ji take kamar ta shake ussaina….
Mama tayi musu godia har kudin mota ta basu ,sukaki karba ,tabata yabawa d Alkunya irin na yaran Ammy ….
Bayan sun fita ,mama ta dinga ma NAWAL fada sosai har ranta y sake bacci har Abban t y shigo y samu mama na Mata fadan Bata fasa ba Dan ganin shi …
Ganin fadan yayi yawa ,y tmby dalilin fadan , NAWAL zaton ta za’a goyi bayanta ,t Fara gayamai karya mama t gayamai duk yadda akayi harda Marin ussaina d zatayi ,daga kawo Noor zata kamasu d fada ,shima ganin Abun Arziki d sukayi n kawo Mai jika Dan yanason Noor musamman d suka rasa hannef ,yaba NAWAL rashin gaskia yamata fadan d dinga Jan girmanta g kanen mijinta nada ,haushi y Kara kamata ta tashi Rai a bace ta bar musu parlour ,suko suka dinga Jan Noor d Hira Tana musu surutu suna dariya kafin kanen NAWAL su dawo dg mkrt islamiya…..
“Bayan komawar su twins ,suka tarar d lefensu ,ganin anaso amusu ca d cewa kalo sukazo b kunya sai ussaina tayi dabarar Basu lbr yadda sukayi d NAWAL a gidan su sai kowa y dawo sauraron ussaina aku sarkin lbr ,sunata mamakin suna yabama ussaina d ta Mata haka ,ita dai Ammy fadan girmama nagaba ta Mata d nuna Mata girman hakuri Akan komai ,anata dariya……
Bayan sati biyu ,aka bugo invitation card n biki d kamu d dinner ,d duk wani Abu d zasuyi na bikin …
Ankon su Yana hanun su ,komai y Kamala na d’inkin Babu Abun d yake hanun tela ,sunyi dinki yafi kala 5 amaren kuwa y kusan kala 15 Alh y musu angwayen sun musu g yayunsu sun musu g lefensu b Abun d aka taba n sutura …..
“Anfara rabon iv hassana d Aishatu suna tafiya tare suna Basu rabon …
Ussaina d sufaya suna tafiya tare suna nasu rabon ,amota sbd cikin jikin su ,in sun gaji ma gida ake mayar dasu ,sai su nemi kawayen su suraka su ,Haka suketa rabon …
Acikin satin biyun d y rage biki ,kullin sai Aishatu d suffaya sunzo gidan Ammy ,Ammy n tausayin su musamman sufayya d suke samata Rai d haihuwa ,amman su ko ajikin su ,Dan yanzu sai nauyin ciki kawai Amman babu laulayi ,….
Suma mazajen hankalin su a kwance tunda sunsan kulin suna tare d Ammy ,iya d hidaya d wata d aka samo sune suke komai n gidan Ammy Bata yadda su shiga kitchen tun suna naci har sun hakura , ussaina ko tuni tace sun Dena shiga kitchen sai na gidan su ,g gyaran jiki d aketa musu d gyara in nd out din su ,komai tsaf !
Shiri y kankama ,biki saura kwana 4 su , Aishatu d sufaya sun dawo gidan Ammy gaba daya sai angama biki zasu koma ,duba d nauyi d sukayi yasa mazajen su hakura badan sunaso ba …
Noor tuni t dawo gida ,gayata biki har su maman NAWAL tayi Alk’awarin zuwa Kuma harda NAWAL inzata Zo!
Aunty zainab d su nawara d su mama d Inna hardasu a anko ,safwan ne y siyo y bama Aishatu taje takai musu ,nawara harda n ‘yan Mata duk d ciki y rage musu rawar gaban hantsi ….
Aunty zainab tanata gudanar d sana’ar t sun Saba sosai d mlm mamman hafeez ,har bashi Yana Bata ,ta siyar t kawo Mai kayan shi har kayan shi sun Fara kasa sakamakon ciniki d yakeyi ,har y bama Saleem y sake Mai order dg saudiya d taimakon abokin shi ustazu hambali ….
Tun mgn Aishatu d Nawara d aunty zainab t tabayi shikenan suke yawan tmby ta Ina yaranta ? Kulin tace suna lpy a dakunan mazajen su ,tun Yana zaton tanada Aure har y Gane Bata d aure ba Kuma ita ta fad’a Mai ba ,duk d haka y yaba d kamun Kai irin na aunty zainab ,ba ruwanta d surutu barkatai ga Nutsuwa ,gashi b yadda za’ayi ta kirashi a waya tamai maganar Abin d be shafi kasuwancin su ba ,shima Haka mgn sana’ar su ko Kaya kawai sukeyi su kashe wayar ,ita Bata tab’a tunanin baida iyali bama duk zamanta da shi ,Bata nemi sani ba Kuma Dan ba Abin d ya shafeta bane …..
“Zuwanta n karshe take cemai ai bazatazo sati Mai kamawa ba ,sbd Akwai biki a gidan dangin mijin Aishatu ta zasuje karyajita shiru g cikon kudin shi a hanun ta …
Yace ai ba komai ,shima gagarumin biki ne dasu na yayan sadeeq zai zama ango cikin satinan Dan Haka Basi d zama Dan ko shago bazasu fito ba ,aunty zainab tace a babban bikine shikenan ma sai wani satin kafin Nan duk mungama hidimomin biki , ALLAH y Sanya musu Albarka Baki dayansu cikin Aure ,y amsa d Allahummah Amin …..
Su Aishatu anata fama gida y Fara kacamewa gidan Ammy ,sun koma side din d su safwan suke hutawa d Yaya ,Dan su samu su sake ita d su sufayya d amaren ,Ammy CE tace su koma can ,shima parlour harabar wake d dakuna 2 na saukan bakin Alh angyara sbd ‘yan uwan shi d zasuzo ……
Yau gidan y dinke Baki duk sun gama zuwa wasu sai gobe dake gobe ne kamu ……
*Maman shaheed*????
[2/27, 2:51 PM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????.
BY
“`MAMAN SHAHEED“`
*KUSKURE* ????????_????????
( _’yar Aiki Ko Matar Gida_)
_shafi n sittin d biyu_
“Yau ne kamun su twins ,gidan y cika d Baki ,Ammy d taimakon su suffaya , Aishatu d mazajen su sun gama tsara komai na birgewa d kayatarwa ….
Tun wuri aka Fara ,sha’ani ,yamma nayi ‘yan Mata d amare aka Fara Shirin kamu ,Bayan angama tsara wajen ko a kasar India sai Haka , Suma masu tulun ciki sufayya d Aishatu ,ba’a barsu a baya b wajen tsara kwaliya Cikin doguwar Riga ,sunyi kyau dama manza beauty ce mai kwaliyar tasu ,Dan Haka t tatso musu kyau iya kyau ,waje ya d’au harama ,Baki sun Zo sosai har dangin Ango har su ,nawara d aunty zainab sun karaso , Aishatu nata murna ta musu kyakyawan masauki ,tare d yalwatasu d kayan motsa Baki ….
Sha’ani yayi kyau ,ansha Al’ada d gargajiya ,ancashe an malkwashe ,masu ciki dai sai juyi suke b karya jiki ,har taro y watse …