HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Yace Indo ma Dan momyn ku Bata Nan ne yasa take tayaku kwana ,ko kunaso ta tafi d’akin ta?

Da sauri Noor ta Kali Indo ta Kali dadyn su tace aa munfi Jin dadyn kwana d ita Dady Kar ta tafi Dan Allah ,kamar zatayi kuka ,murmushi Mai ciwo yayi da ya tuna da NAWAL yace ai bazata tafi ba daga yanzu ma kullin tare zaku dinga kwana kinji ko?

Da murna tace to Dady ,ta tashi daga gunshi ta tafi Tana janyo Indo wai tazo suyi Addu’a su kwanta ,Indo na k’ara mak’alewa a bango ..

Fahimtar haka yasa ,dadyn su Noor saurin yi musu sallama yabar d’akin ,ya fita daga d’akin yayi wata uwar ajiyar zuciya na samun Dan samun kariya daga shed’an da ya bijirema karatun d ya dinga Mai shida gabban sa ..

Indo ma ajiyar zuciya tayi ,d sauri taje ta murd’a key a k’ofan sanan hankalin ta y dawo jikin ta ,taja Noor suka yi Addu’a suka kwanta Abin su ,zuciyar Indo cike d tunani had’e da tambayoyin da Bata da amsoshin su …..

Hakan take ga dadyn su Noor ga TV Yana kallo amman abad’ini ba kallo yakeyi ba ,tuno abubuwan d’azu yakeyi d Kuma tambayar wai Mai zuciyar sa take nufi dashi ne?

Wani bangaren zuciyar sa tace ,shaid’anne yakeson gwada tunanin ka yake wasa da kwakwalwar ka …

Cikin baccin Rai yace Allah ya sawak’e ,nafi karfin ka shaid’an da izinin ALLAH sadai kaji kunya , haba ALLAH ya sawak’e min *lndo*? *Ni*? Shaid’an Allah y min tsari ,wata zuciyar Kuma tace da Aure fa a tsakanin ku?

Yace sai me ? Kai Allah ya kiyaye mu daga fad’awa kogin nadama , badan yayi da gaske ba da ranar kwana zaiyi Yana sak’a da warwara akan Al’amarin da ya Gaza gane manufar sa ……

 

Tun asuba d y fito sallah ,be sake fitowa parlour ba sai da ya gama Shirin fita tsaf Dan yau d wuri yakeson barin gidan ma …

Dan ko karyawa baida damar yi Dan sai y fara biyawa ta gidan Yaya Ahmad kafin y tafi office..

Dan ko yaransa baya tunanin zasu gaisa ,fanin Abin d zasuci har su tafi school yasan baida matsala Indo zata musu komai fiye da yadda mahaifiyar su zata musu ,Dan haka Yana gama shiri yasa Kai yabar gidan ….

Indo taji bud’e k’ofan parlour taji tashin motar sa ma, har ta lek’o ta window taga fitar sa daga gidan ,wani ajiyan zuciya tayi “tayi hamdala sanan ta Fara tashin su Noor don ta musu wanka ta shiryasu zuwa school..

Breakfast kuwa dama ta gama ,Dan cikin sand’a ta dinga shiga kitchen har ta Kamala komai …..

Bayan ta gama musu wanka ,ya shiryasu ta basu break suka k’oshi ta kaisu har wajen school bus d’in su da kanta sunata d’ago musu hannu har bus d’in ta tafi ..

Wani shak’uwa ne yake k’ara samun wajen zama ajikin Indo da su Haneef fiye d da , Dan yanzu Indo har ji take batason rabuwa d su Noor Dan sunada Nutsuwa ga saurin karban koyo Inka koyar dasu Abu Kuma suna Aiki dashi sunada dadin zama gashi yanzu sunfi girmamata bakamar da ba duk d da d’in ma basu tab’a ko hararar ta ba bare zagi ko cin mutunci ,Amman yanzu ta Lura d sunfi girmamata d sonta Dan haka ta saki jiki dasu take musu Abu tsakanin ta da Allah kamar yadda take musu a da …..

 

Shiko dadyn su Noor , bayan sun gaisa da Yaya Ahmad y zayane Mai komai game d aikin NAWAL d night duty d aka Bata ta karba Kuma ..Amman y boye Mai wasu abubuwa da suke sirri a tsakanin shi d NAWAL.

Dan basa boyema junan su damuwar su musamman yanzu d sukeda iyali gaba d’ayan su , sunfi neman shawarar junan su …

Hakuri Yaya Ahmad yaba shi , yace ya kyaleta inhar ba matsala ,aikin yanada kyau da Dadi Amman inkaga wani Abu d hankalin ka be gamsu dashi ba ko sabanin shari’ah zan tayaka yaki akai ,yanzun ma ba Ina goyon bayan Abin da tayi Bata aikata laifi bane aa ….

Kawai dai banaso ace kun Sami matsala ne da matarka daga Fara aikin ta kasan Akwai ‘yan bani na iya sa’idawa Ana ruwan kudi suna cin bashi , tunda atarihin Auren ku ba wani Abu d ya taba giftawa a tsakanin ku na rashin dad’i ko Akwai?

Safwan ya girgiza Kai ,yace sai wanan !

Yaya Ahmad yace to Ina Mai baka hakuri ka Dan daga kafa ka auna tunanin ta wanan y wuce d next time ta sake maka irin haka to kaga ya zama ganganci kana da right da zaka Hana aikin ma gaba d’aya ,Dan yanzu kaga Nima sufaya ai ta Sami Aiki Amman na hanata ….

Safwan y katse shi d cewa Yaya angwancin ne har yanzu baka gama …..

Kafin y karasa Yaya Ahmad y takwabi bakin sa suna dariya ….

Yace Mara kunya kaga Ina ,ma wasa ko ….

Kawai dai wlh ta Sami shigar ciki ne nikuma banaso a wahalar min da baby na shiyisa ….

Sukasa dariya ,safwan yace a Yaya kace Haneef y kusa samun k’anwa ko k’ani Yana Sosa k’eya …..Yaya Ahmad yace kwarai Sosa k’eyar ka da kyau , kana mun munafurci wai kana Jin kunya na , Alhalin gulma ne ,safwan y sunkuyar da Kai Yana cewa Allah Yaya Ina kunyar ka kagama ko had’a ido na kasayi dakai ….

Aiko Yaya safwan ya kamo wuyan sa yana d’ago fuskar sa wai sai ya kalesa sunata kyakyata dariya …..suna haka Amarya suffayya ta fito ta gansu kamar masu kokuwa sunata dariyar su …safwan nacewa Dan Allah Yaya kabarni …

Suffaya CE ta dakatar dasu da cewa , Abun na kokuwa ne Bari nayi gidan Ammy Dan Kiran su twins suzo su raba Dan Ni karku karasa Ni ….

Aiko Yaya ya sake safuwan Yana dariya …

Shiko safwan cewa yayi ,tab! Mu karasa gawar da ba tamu ba kuwa ,ko da yake wanna gawar tamu ce halak malak ,gaba daya suka sa dariya …

Safwan ne y Mike Yana gyara rigar sa Yana cewa Yaya duk ka Bata min kwaliyata …..da sauri Yaya Ahmad d’in yace barin zo na gyara maka to !

Da sauri safwan y Kara gaba Dan barin parlour , SUFAYYA ce tace au ba sallama ma kanina?

Juyowa yayi yace sorry yayane y firgitani ,Nabarki lpy Allah y inganta Mana yana ma Yaya Ahmad gwalo d signal…..

Itako sufaya kunyace ta kasheta atsaye , ko rakiya Yaya Ahmad bemai ba yasan y gudu b tsayawa zeyi ba ..

SUFAYYA ce tace Kai Amman kunban kunya wlh , Yaya yace kunyar me Ni Kuma na baki,?

Tace inbaka fada Mai ba ya za’ayi ya sani , farfesa ?duk zaka gama fesani a gari…..

Bata k’arasa ba y rungumota suka zauna Kan kujera ,Yana ce mata ,ki fahimce ni d kyau ,tsakani na d safwan ba boye2 abokanai ne mu ba ‘yan uwa na jini ba kawai Muna ba junan mu shawara bama boye ma junan mu komai kisa haka aranki uwa d’aya uba d’aya yafi karfin wasa…

Cikin so d k’aunan zumunci irin nasu ,tace ai tun b yauba tun shigowana cikin ku bayan munyi Aure na fahimci haka ,Kuma kuna birgeni Danni Banga haka daga gidan mu ba kasan mun Sha wuya wajen kishiyar maman mu ..

Yace duk kin sanar Dani komai ,Amman yanzu fa ba kun girma ba Kuma komai ya wuce ,har Yaya nazifi y kwatan muku ‘yancin ku , ita Kuma taga karshen ta har t roki mama yafiya ta dataga mutuwa ,kin Mata kin Gaya min komai ?

Suka yi murmushi ,tace hakane ban boye maka komai ba daga gidan mu , yace to ki bar komai a yadda ya wuce Dan Abin d y wuce baya dawowa ..

Tace hakane Habibi na ,insha Allahu n barshi ….daga Nan suka Lula duniyar Amarya d Ango ….

*********

“Bayan momyn su Noor ta dawo ,Indo t gaishe ta ta had’a Mata break taci tayi Kat ,sanan t tambayi Dady su Noor d su Haneef .

Duk Indo t Bata amsa d shi y fita office su Kuma sun tafi school ,tace toh taci gama d Kai Loma Abin ta..

Bayan t gama ta tafi bedroom d’inta Dan wanka ta huta ..

Kafin ta tafi ,Indo ta tambayeta zataje gdn Inna ta gaishe ta sai yamma zata dawo intakamala Abincin Rana yanzu tunda yau Alhamis Kuma ba islamiya …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button