KUSKURE Complete Hausa Novel

Bayan t d’auka taje ta cinye ,sai taji gdn kamar Alamar b mutane ,Dan t tabatar fitowa t sake yi t Fara duba d’akin su Noor b kowa har taje zata bud’e d’akin safwan ,sai t tuna wani Abu ,ta fasa ta dawo t koma k’ofan d’akin Indo tanata Kiran Haneef d Noor shirun da taji yayi yawa ne yasa ta bud’e d’akin domin masifa ,taga wayam b ko bera,tayi kwafa ta koma d’akin safwan afusace Tana Kiran su Nan ma Jin shirun yayi yawane yasa ta bud’e d’akin Koda ta shiga b kowa har toilet t duba baya Nan yaran ma basa Nan tsaki tayi t Kama tunanin inda suka shiga gaba d’ayan su ?
Fita tayi t tmby me gadi ,yace eh Alhaji yace min sun tafi gidan hajiyan tagwayen Nan “ta gane gidan su twins yake nufi ,tace d su Noor? Yace eh har baybay (bye bye) ta dinga min ,tace d Indo?
Ya sake cewa eh harda kakata Aisha Indo suka tafi Kinga ai kodan renon yaran ma tunda ko anan itake kula dasu …….be k’arasa ba ta daka Mai tsawa Mai cike d tsanar maganganun nashi tace ya Isa haka ,tabyr ka nayi ? Ka bani amsar tamby ta toh y isa haka ….,ta juya tayi tafiyar ta ranta y matsanaicin bacci …..
Itama shiryawa tayi ta fice tabar gidan d niyar komai ta tafasa ta k’one ,yayi duk Abin d ya Dace akanta ,Kuma wlh night duty b fashi yanzu ta fara Jin dad’in shi ma ………
*FANC SUNCE ANYA NAWAL*…..????????????????♀
[12/28, 7:04 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????
“`BY MAMAN SHAHEED“`
*KUSKURE* ????????♀_????????
( _’yar Aiki ko matar gida_)
_shafi na shatara_
Ya wuce d’akin shi Dan kwanciya …
Sai d yayi nisa yace musu sai d safe …..Indo ta zata d yaransa yakeyi Dan haka Bata tanka Mai ba” tadai bishi d ido…
Shi Kuma Jin shiru yasa shi juyowa yana kalon ta ….ita ko duk jikin ta ya Mata sanyi ganin Ashe da ita yake, cikin raunaniyar murya tace sai d safe dadyn su Noor kanta a kasa Tana wasa d hanun Noor ..
Ganin yanayin ta ,yasa y had’iye Abin da zai furta ,yace Allah y bamu Alkhairi kawai y sa Kai …..
Itama Basu Jima ba ,ta kwashe su suka koma d’aki bayan ta kakashe kayan wuta ,ta kaisu toilet sukayi fitsari sanan suka kwanta bayan sunyi addu’a.,..
NAWAL d safwan dai zaman doya d manja akeyi ,Wanda ita ta zaba musu hakan ,yauma a wajen aikin ta kwana tayi Tana bege d mararin gwarzon jarumin nata ga waya ta k’aura a tsakanin su, shi yayi fushi baya kiranta itama girman Kai y hanata Mai ladabi d ban hakuri ….
Indo ta tashi tun farar safiya ta kammala komai ta ajiye sanan ta taso su Noor Dan yi musu wanka su tafi school..
Bayan t gama dasu ne , around 7:30am ta umarce su d suje su gaishe da dadyn su ,haka kuwa sukabi umarnin Indo ,yayi ta sa musu Albarka sanan y rakasu har wajen school bus d’in su da kanshi ,yace in antashi suka dawo gida za suje masalacin juma’a in sun dawo sai ya kaisu gidan Ammy ko?
D murna Noor tace eh Dady har da aunty Indo zamuje ko? Indo n tsaye Tana kalon su kanta a k’asa ,gyad’a musu Kai yayi Alamar eh ….
Sanan y tafi kaisu ,kafin y shigo gidan Indo t had’a Mai nashi breakfast d’in ta barmai ,ta gudu kitchen taga yau ba fita zeyi ba Dan haka yau Akwai wasan buya tsakanin su Dan wani irin nauyi d kunyar sa takeji ga tsoro Wanda ta rasa dalilin tsoron…
Bayan y dawo daga Kai su Noor ,y ga alamun kayan Karin sa , y zauna y gyare cikin sa d kunun gyada na filawa d alale Mai kwai da hanta aciki yayi Kat sanan y nufi bedroom d’in sa dan komawa bacci ….
Itama indon gyara wajen tayi ta tafi kitchen ta gyara shi shima ,sanan ta zuba nata Abincin taci ….
Bayan t gama Bata d wani Aiki ,Dan haka tayi wankan ta ta gyara jikin ta dawo falo Tana kallon AREWA 24 Tana kalon Shirin akushi da rufi tanata hadacewa a kwanyar ta Tana cewa sai ta gwada insha Allahu…
Tayi nisa sosai cikin kalon ta kawai sai ga momyn su Noor ta shigo , wani muguwar harara ta jefama Indo , itace sallamar tata ….
Jikin Indo yayi sanyi ,Amman saboda k’arfin Hali tace aunty Ina kwana ! Tsaki tayi tace d ban kwana ba Kya ganni?
Ina yarana ? Murya n rawa tace sun tafi school tun d’azu..
Tace barin Gaya Miki daga yau sai yau in Kika sake shiga tsakani na d yarana ranki zaiyi mumunan baci Kuma in Kara ganin muna magana d dadyn su Noor ki tsaya awajen batare d kin bar wajen ba wlh sai na Bata Miki Rai cikin masifa d hargowa takeyi dadyn su Noor na jiyo ta daga d’aki itako atunanin ta baya gidan Dan bataga motar sa ba motar d Dan Bala yake kaisu unguwa ce kawai a compound d’in gidan tasa Tana wajen gyara ….
Shiko Don Kar y karama Indo laifi kamar yadda yasa taketa kumfar baki ,yasa be fito y kulata ba so yake sai ta shiga room d’inta zaije ya fetse ta tas..
Sai d ta gama ma Indo masifa son ranta ,Indo ranta y mugun bacci ,har zuciyar ta ta karye d zatayi kuka , wani sashi na zuciyar ta yace Mata karkiyi kuka ki yi asarar hawayen ki akan wacce batasan amfanin ki atare da yaranta ba uwa ubu kima d sanin hak’ok’in yaranta d na mijinta bare ke Mai Aiki ,adad’e anayi sai gaskia sannu Bata Hana zuwa sadai adad’e ba’aje ba ki Dena damuwa d damuwar ta Sam ki zama macce Mai ra’ayin kanki Kuma Mai ak’ida Mai kyau ,Dan haka Indo taji wani k’arfin gwuiwa yazo Mata Tama cire damuwar acikin ranta ta ba banza ajiyar ta hofi ta d’auka …
NAWAL Bata saurara ba saida tayi Mai isar ta sanan ta shige d’aki duk azaton ta safwan baya gdn ,batasan motar sa gyara Yaba d’an Bala ya kaimai ba ,shi Kuma Yana gida Yana sauraron ta ….
Bayan ta shiga d’aki, Indo tayi wucewar ta d’akin ta itama ranta fes Dan ta d’aura aniya daga yau duk wani buragadon momyn su Noor yadena Bata Mata Rai tunda ita tayi nisa Bata Jin Kira matsalata kawai ta sani Banda ta wani itama ta daina sa damuwa aranta balle ayima Inna asarar ta wlh …..
NAWAL bayan ta fito daga wanka ji tayi an bud’e k’ofan ta an shigo …
Afusace ta juyo d niyar masifa atunanin ta Indo Ce ,sai tayi tozali da safwan ,sai ta maida makaman rashin mutuncin nata ..
Sai d ya gama kare Mata kallo ya tabe baki yace kin gama masifar? Kin gama fad’an naki Mara dadlili ? Kiji tsoron Allah NAWAL kin canja kwata2 kidinga Aiki kina sanin hukuncin Allah acikin sa saiki zauna lpy a Rayuwar ki ….
Cikin huci d baccin Rai ,tana nuna kanta take cemai “yanzu dadyn su noor kana nufin bansan hukuncin Allah aduk Abun da nakeyi ba ? Me ka d’aukeni JAHILA ko MAHAUKACIYA ?
“Kafad’a ya d’aga yace d’ayan biyu duk Wanda Kika Kira kanki dashi ,Yana zare Mata ido kamar zai duketa ,tsorata d yanayin sa da tayi yasa ta fasa k’arasowa inda yake Kar Rana ta kubce safwan ya daketa da ya daki Auren sa kuwa take fada cikin zuciyar ta …
Aiko ta inda yake shiga batanan yake fita ba Dan haka ya dinga surfa Mata masifa kamar ze cinyeta ….
Haushi da takaici gashi yafi karfin dokuwa acwajen ta , ganin Akan fad’a d zagin da Tama Indo ne yake Mata masifa yasa ta fita daga d’akin afusace zuwa d’akin Indo…
Shigarta keda wuya ,ta rufe Indo da duka tako Ina har Tana had’ata da bango wai zata had’ata da mijin ta ,Indo sai tare duka takeyi idon ta girmizizi babu Alamar hawaye …
Ihun Indo d y jiyo yasa ya biyo ta ganin ta rufe ‘yar muntane d duka yasa ,ya janyo ta ,Aiko ta kwace tace wlh sai ta illata yarinyar Nan …
Ya wani d’auketa d gigitacen Mari yace baki Isa ba wlh sadai ki illata kanki ta hanyar da Kika zabanma kanki wacce a tunanin ki Tana billewa Alhalin ba inda zata kaiki sai tashar nadama ..