NOVELSUncategorized

KWARATA 93

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* ????
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_




                       *KWARATA*
      _{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ ????????

*ASMA’U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

                         &

*RABI’ATU AMINU MAMMAN DEE*



???? —— 91


             _Alhamdulillah_

_Alhamdulillah_
                             _Alhamdulillah_

       *_Assalamu Alaikum masoyana , suna na Jamila Musa wacce kuka fi sani da Meelat Musa , ina muku fatan alkairi maudu’in rayuwata ???? , zanyi matuƙar kewarku sosai , inajin wani iri a raina , jiki yai sanyi , idona shima zaiyi kewarku , yana muku bankwana da hawaye ???? , gaskiya ina matuƙar sanku yadda bazaku iya ganewa ba , hmmm , tou ina dai muku fatan alkairi a duk inda kuke a faɗin duniyar nan alfaharina , zan tafi׳ , sai kuma Allah ya sake haɗamu idan muna rabon sake haɗuwa a cikin sabon littafina mai taken ƁOYAYYAR SOYAYYA , KWARATA yazo , kuma zai tafi , Dikko da An mata suna muku fatan alkairi , ni kuma Jamila nake neman yafiyar duk wanda na mishi babu daɗi , wani ban ganshi ba , amma rubutu na yaje gareku , ina alfahari daku , kuma ina muku fatan alkairi , ina matuƙar ƙaunarku sosai da sosai , masoyana da mukeyin waya daku , wasu kuma cht da wanda Allah yasa na gansu ido² duk ta dalilin Dikko da An mata ina matuƙar ƙaunarku , Allah ya sadamu da alkairi gaba ɗayanmu , ngode ׳ da yadda kuka nunamin ƙauna , na barku lafiya……_* ????????



        Yaya janje , a , a , da gudu Papi yabi bayan Dikko yana kuka , kai nifa babu inda zanje dakai , ƙara faɗar janje yayi yana bin bayan Dikko da sauri dan taƙaita gudun saboda ya isko shi , a , a Dikko ya sake maimaitawa , bin bayan shi Papi yakeyi yana ci gaba da kuka , dariya Dikko yayi sosai yace tou zo muje , yayi maganar yana kama hannun shi , juyowa Papi yayi tare dayi ma Nabeela gwalo da tace Allah yasa kar a tafi dashi , murmushi Dikko yayi ba tare daya sake magana ba suka fita , yayi kyau sosai a cikin ƙananan kaya , riga jinin kare baƙin wando rufaffun takalmi suma baƙi sai baƙin agogo , Papi kuma manyan kaya ne jikinshi…..

       Dariya nayi tare da kallon Nabeela nace zakisha mamaki , tunda yayi waccan dariya lallai sai yayi ma Papi wani abu na mugunta , kuma zaki sha al’ajabi bara su dawo , dariya Nabeela tayi tare da cewa kuma nima in rama gwalon da yayi min da zai fita…..

       Gaban mota Dikko yasa Papi yana cewa ai dai zakaje ko ? Ya ƙara tambayar Papi , goge hawayen shi yayi tare da cewa Janje Yaya , yayi maganar yana kallon idon Dikko , tou zauna , zama yayi a dai² lokacin daya tashi mota ya fara tafiya , Ashiru dake tsaye daga gefe yace Mai gida ai ban san fita zakayi ba , ba tare da Dikko ya tsaya ba yace ai ba nisa zanyi ba , ya ƙarasa maganar yana ɗage gilashin gefenshi da ya sauke danyin magana da Ashiru ya fice daga gidan da gudu…..

         Suna fita muma muka zagaya can bayan gida ina taya Nabeela aiki zatayi baƙi , gidan ne gaba ɗaya aka firgita , yasa ana ta rosheshi , nidai a ganina asara ce kawai dan wallahi gidan ya haɗu iyakar haɗewa , kuma banga abinda yayi ba , duk komai na gidan da aka fitar tsohon namu kenan , yaranshi ne suka kwashe su , ni ɗakinshi ma nafi tausayi dan Allah ya sani an daddaƙe ma kuɗi rai a ɗakin Dikko , anyi masa haɗuwa ta haɗaɗɗin haɗewar masu haɗuwa , can baya ma da akayi gidan anyi surutunshi sosai kuma har yanzu ba’a gama surutun ba , yanzu kuma wane irin gini za’ayi…… ? Aikin baizo wurinmu ba shi yasa bamu tashi ba , amma dai duk an fitar da komai na gidan su Ashiru sun kwashewa “yan uwansu , ba komai a gidan muma goruba road zamu tafi a daren yau sai an gama aiki zamu dawo , aikin da nake taya Nabeela baida wani yawa , amma kunsan yadda jiki yake , shi jiki sabo ne dashi , idan an horashi da wahala da ita zai horu kuma idan harma bakayi abun wahalar ba bakajin daɗi , idan ya saba da hutu tabbas baya iya ɗaukar wahala , shi yasa “yan gayu ashe muke ganinsu kamar sun raina mana hankali , to ba haka abun yake ba , saida na shiga fagen na gane haka , nima dai yanzu bana iya sakin jiki inyi aikin nan kamar jakkar ci rani , idan kuwa nayi aiki mai yawa sai nayi jinyar gajiya…..

Bare dama akwai masu aiki maza da mata , kuma duk wani ma’aikaci , daga direbobi , masu shara , masu girkin abincin da ma’aikatan gidan ke ci , masu gadi , masu ban ruwa wa fulawowi har masuyi musu aski su gyarasu idan sun zame daga tsarin da ake sansu , gaba ɗaya a gidan suke zaune , suna da wurinsu daban , kuma a gidan ake basu abinci kuma albashi ake basu duk ƙarshen wata , amma shi Dikko bayacin abincin gandu , namu mukeyi daban ina da mai aiki ta daban amma baya san abinci masu aiki sai ni zanyi idan yana gari , kuma masu aiki basa gyara masa ɗaki , ko yanzu da bana lafiya shi yake gyarawa ya goge komai fes kamar mace , ya iya gyaran gado idan har yayi miki gyaran gado zakisha mamaki , baya san ƙazanta ko kaɗan , da nace masa Nabeela cewa yayi a , a , dan iyakarta palonshi bata taɓa shiga bedroom inshi ba , nidai da nazo amma ban sani ba ko a zamanin Jiddah tana shiga ba , saida muka gama abinda mukeyi Nabeela tasa aka kwashe komai aka kai a motar ta , sannan muka taho dan komawa ciki.

     Da gudu ya shigo gidan a dai² lokacin da mu kuma muka bayyana gaban fuskar gidan , tun kafin motar ta ida tsayawa cak ya kashe motar ya fito , tunda nake da Dikko ni ban taɓa jin waƙa a motarshi ba sai yau , ya wani ƙuro volume , buɗe hannuwan shi yayi ya nufo inda muke tahowa yana wata “yar munafukar rawa , daga ni har Nabeela dariya mukayi , rumgumeni yayi tare da ƙyalƙyalewa da dariya ya raɗamin wai Papi ya girma , cikin rashin fahimta na leƙa ta gefenshi naga Papi ya fito daga mota yana cewa ban nuna muku , dariya Dikko ya sakeyi sannan ya sakeni yana cewa yanzu zai cire wando ya fara kuka , ya faɗa yana nuna ma Papi yayi rawa , tsalle Papi ya farayi yanayin yadda Dikko keyi , murmushi Dikko yayi tare da kallon Papi ayyo ah² wayyo yana murmushi , sakin jiki Papi yayi yana ta rawa , saida Dikko yaga ya shagala yana rawa , ya koma mota yai tafiyarshi.

      Nidai ban gane girman da Papi yayi ba , kuma ni kwata² raina bai kawomin kaciya Dikko yayo ma Papi ba , saida muka shiga ciki yaci gaba da cewa ban nuna muku abinda Yaya yayi min , ya faɗa yana rumgumer bango , duk babu wanda yayi ma Papi magana , bayan Nabeela ta fito wanka yace mata , yayinya joki in nuna miki , cire wando Papi yayi , Nabeela tana zuwa , yayi dariya tare da maida wandonshi yace baci gani ya faɗa yana mata gwalo , kowa fita harkarshi yayi muka ci gaba da abinda ya shafemu , shi kuma sai murna yakeyi , saida ya fara shan azaba ya cire wando , muma bamu sake shiga sabgar shi ba kuma bamu sake kallonshi ba , allura tana fita Papi ya fara ihu….

     Yana taɓa kaciya , Nabeela ta fara dariya tana ɗaukarshi a waya , tana cewa da nace karka je ba sai da kaje ba ? Yanzun nan zan tura Momy ta gani , nima abun dariya ya bani sosai , iskancin Dikko saishi , kullum abunshi gaba yakeyi babu alamar sauƙi , Nabeela daina video tayi ganin Papi yana halbe² a ƙasa yana cewa nama ɓata da Yayan nan , rumgume Papi tayi suka ci gaba da kuka tare ,

      Duk daɗewar da Dikko yayi waje harya dawo daga Papi har Nabeela basu daina kuka ba , da nace masa me yasa yayi haka baiga Papi ƙarami bane ba ? Kallon Papi yayi tare da cewa gobe ma idan ka biyoni ƙaro maka zanyi , cikin kuka Papi yace kuma na fata dakai , ai nine na ɓata dakai shi yasa naje na kaika akayi maka , miƙa hannunshi yayi tare da cewa zo muje , maƙale kafaɗa Papi yayi yana harararshi cewa kuma saiya faɗawa Dady , murmushi Dikko yayi tare da cewa tou jeka fa faɗa masa , yayi maganar yana fito da wayarshi yace bara kaji ma in kira Dadyn ya ƙarasa maganar yana kara wayar a kunnenshi.

      Bayan wani lokaci ya fara magana a waya , Dady ga Papi zai kawo ƙarata yayi maganar yana ba Papi waya , cikin disashshiyar murya Papi yake faɗawa Dady abinda Dikko yayi mishi , bansan abinda Dadyn yace masa ba , ajiyar zuciya Papi ya sauke sannan yace to , shiru yayi , bayan wani lokaci Papi ya sake sauke ajiyar zuciya yace to , ajiyar zuciya ya ƙara saukewa ya faɗi Nabeela , ɓata fuska yayi ya taɓe baki yana ajiyar zuciya , bayan wani lokaci kuma yaba Nabeela waya , bayan ta gama tabani waya nima na gaishe shi , yamin sannu da mai jiki , bayan mun gama gaisawa nima nayi masa addu’a kamar yadda naji Nabeela tayi , sannan nabawa Dikko waya , fita yayi daga ɗakin yana magana a waya.

      A gaggauce muka shirya muka bar gidan , saida muka biya ta wurin Momy , tayi faɗa sosai da abinda Dikko yakai Papi akayi mishi , ta kuma yi addu’a Allah yasa a fita lafiya , anjima zata aiko Ashiru wurin Papi , bamu wani daɗe ba muka wuce goruba mu dukanmu , shi gidan an gama aikinshi , kuma babu abinda ba’a saka ba , komai na gidan sabo ne katakal , har kicin ma anyi mishi tsari mai kyau babu abinda babu. Abundai , sai Allah sabunanni……

    Satinmu biyu a goruba road , gaba ɗayanmu bamu da wata damuwa , rayuwar mukeyi cikin farin ciki , amma tunda wannan satin ya kama Nabeela da Papi basa tare dani saboda asabar ta gaba ake zaɓe suna can gidansu , mijin da zata aura kuma an tsayar da ranar aurensu ne idan yaci zaɓe za’a haɗa da murnar cin mulki da kuma shagalin ɗaurin aure , idan akayi rantsuwa kuma amarya zata tare a gidan gwamnati kenan……

     Ni yanzu gaba ɗaya na daina gane kan Dikko , ya burke bansan abinda yake damunshi ba , saidai idan na buƙaci ganinshi zaizo ne ya bani haƙƙina da zaran kuma ya gama zai kama gabanshi , da nace masa wai ina yake zuwa yanzu sai yacemin shi bazai zauna gida ba tunda ba mace bane shi ,

      Abun ya dameni sosai , dan haka na kira Rabiya na faɗa mata kai tsaye , haƙuri ta bani tare da cemin in bari idan aka gama zaɓe zata zo , Inna dana kirata nace mata shawara na kirata muyi cemin tayi idan dai ya shafi Dikko karma na fara faɗa mata.

    Har akayi zaɓe aka gama ni bansa Dikko a ido ba , kuma Allah ya basu sa’a sun sake ɗagewa sama , wanda Nabeela zata aura shima yaci , duk shagalin da akayi banje ba Dikko ya hanani zuwa , Nabeela bataji daɗi ba kwata² , Momy ma taji babu daɗi da tace azo a taho dani cewa yayi idan dai shine yake aurena ya hanani zuwa idan kuma aurena ba a hannunshi yake ba tou inje , Momy da kanta ta haɗani da Dady a waya nayi mishi murna ,

      Shagalin sake komawa a mulki banje ba , amma na ranar da aka ɗaura auren Nabeela naje , kuma tun safiyar ranar ina wurin Momy , kayan da zan saka Momy ce da kanta tayi minsu , duk abinda ya kamata itace tasa akayimin nima dai na fito kamar sahun “ya “yanta tunda ina da kyau na mai burgewa da baka gajiya da kallona , kuma banda irin wannan duhun kan na ƙauyanci , suna ta nunamin ƙauna da soyayya daga ni har Papi ,

     Hmmmm , anyi wani irin shagali daya zo ma al’ummar jahar Katsina baƙo , ɗiyar gwamna ta auri gwamna , manyan mutane daga jahohi da dama sun samu damar halattar wannan gagurumin ɗaurin aure , wanda aka tara dubun² mutane , ni ina nan zaune a bedroom in Momy saman gado zaune kusa da Rabiya , abun duniya duk ya dameni , dan yanzu ko wayata Dikko ya daina ɗauka idan na kirashi saidai ya turo min text , wai idan wani abu nake so daga gareshi in mishi a rubuce basai na wani dameshi kira ba , kenan idan bani na buƙaceshi ba shi baya buƙatata ? Me hakan yake nufi tou……?

      Lokacin da za’a tafi wurin shagalin party , yanzun ma Momy ce ta bani kayan da zan saka da mai kwalliya ta kuma tsaida Rabiya wurina dan ita tana fama da jama’a , idan dai mutum ya gitto wurin ya gani zaice masha Allah , wasu daga ahalinsu Dikko basu sanni ba , idan akace wacece Rabiya zatace matar Dikko ce , ko abokan wasa daa suka fara jana da wasa Rabiya cemin tayi kar in koya musu , basu da mutunci. Duk yadda dangin miji zasu soki idan dai baki da power wurin miji kin zama katin ɗaurin aure ,

      Jiddah tana cikin tawagar “yan gidansu , kuma hada Mardiyya Hafsa da Mom inta suna tare da Asma’u amma banga Amisty ba , nidai duk jina nake a takure , Papi kuwa yana liƙe da Nabeela tana fama da hidima amma yaƙi tafiya wurin kowa sai wurinta , duk yadda Momy taso su Ashiru su fita dashi Dikko cewa kar wanda ya ɗauko shi wai su barmin ɗa na can , nidai bansan abinda ya faru ba tsakanin ni da kuma Dikko , amma kuma na fahimci kamar Momy da Dikko akwai abinda yake faruwa.

       *_Uhum baya da ƙura kenan_*


      Anyi shagali na wuce ni na rubutashi , kowa ta ƙiyasta yadda hankalinta da tunaninta zai iya ɗauka , ɗiyar gwamna ta auri gwamna , ga gidansu amarya da kuɗi ko ba mulki su dama attajirai ne wanda kullum kuɗin nasu kamar aiko musu su akeyi , caf lallai , neman suna ba banza ba , ga wani ya tafi nema amma ya rasa ranshi bai samo ba , su Dikko tun ba a waye da sanin amfanin a sanka ba sukayi suna kuma aka sansu , sun nemi kuɗi kuma sun samu tun ba’asan amfanin kuɗi ba ,  rabon da naga Dikko harna manta sai yau a wurin party , yayi wani irin wanka na tashin hankali , yasa wata irin sheɗaniyar shadda akayi mata ɗinki “yar ciki wando da babbar riga , gemun nan yasha gyara sai ɗaukar hankali yake , yana tauna cingom a hankali cikin salo mai ɗaukar hankalin duk wanda ya kalleshi , yayi׳ , ya haɗu iya haɗewa , ya burge , yayi kyau harya gode Allah , wallahi an tara duk irin mutanen da baku tunani wurin shagalin nan , amma na rantse muku da girman Allah babu kamar Dikko a wurin , ya haɗu iya haɗuwa yaci taro , yaba maza azaba kuma yaƙi barinsu su huta , duk wani mai kucakin gayu a wurin ya kama kanshi , yana gaba su Ashiru na biye a bayanshi , yana tafe yana jin kanshi kamar zai tashi duniya…. Su Ashiru na biye dashi ɗauke da wasu irin ƙattin jakukkuna biyu , tunda ya doso wurin yake ɓata rai , mutane sukaci gaba da darewa suna buɗe mishi hanya yana wucewa , daya wuce sai abi bayanshi da kallo.

      Rabiya dake tsaye kusa dani tajani muka tunkaro hanyar fitowa , wai dan kar in gani , hmmmm , hankalin kowa ya koma wurin Dikko tunda ya shiga inda ake rawa , ya kafe kanshi yaci gaba da ɓara mata kuɗi , makaɗa suka ruɗe , duk wani mawaƙi da aka tara wurin nan ya daina waƙa sunan Dikko kawai yake kira ana mishi kirari , da kuɗin hannunshi ya ƙare sai a miƙa mishi , DK kawai suke kira , dakel aka fiddoshi daga wurin dan bashi da hankali akan ɓarar da kuɗi , idan zai kwana a haka baya gaji kuma bazai daina ba , zaiyi ta zubawa ne baya gajiyawa , haka kuma idan zai bayar yake kyauta maisa ɗimuwa. Wace ce  ita…………………???

       Nace muku banda labarin Bello ko Dady ko ? Babu ruwansu dani , dan tunda Dikko ya gwagwaɗa musu layi akaina , yace musu ko ciwon kai nayi ko naji an kira sunansu bacci a bacci yayi musu rantsu kashe su zaiyi , tou wannan dalili yasa suka fita sabgata….

Mardiyya
Jiddah
Amisty
Hafsa
Saude
A ` e
Tawagar gidanmu , su tuni na siya musu gida kuma har yanzu basu daina harkar bariki ba , danbe da duk wata harkar iskanci…..

     Ummu Affan , ita mijinta a saketa , Abbu Afsar wato { Alaji } wanda da Dikko ya tafi dani Babana ya ƙafe ? Wanda ya siya min rigar birthday ? Ya kula da Baba ? Tou har yau ni banda labarinshi , kuma ba abinda ya dameni da sanin halin da yake ciki.

     Yazeed

      Wace ce Dikko yayi ma liƙe a wurin party…… ?

       Mu koma baya……

       Gyara zamanshi yayi tare da cewa bara na baku labari , a london na haɗu da wata “yar tasha , tunda ta shigo jirgi kawai tayo wurina ta zauna……

        Dikko yace ai ban shanyu ba shi yasa zanyi ma Perpy wata Momyn ,

   Ashe ni ina tunanin Yusra ƙawar Sadiya matarshi data rasu ne , abinda yasa tace ita maza basa burgeta bata samu irin tsarin da take so ba , shi kuma yace kamar wani sakarai haka ya kalleta , 

      Ya ɓoye labarin , haukata ya hana na barshi naji yadda labarin yake na tsaya wani kishin banza da wofi , duk yadda Dikko yake tsaye akaina ? Kuma “yar uwarshi ke tsaye kaina , soyayyar mu da Dikko zakuyi tunanin akwai wata bayan An mata……..?

      Wane sakaci nayi ne ? Me na rageshi dashi ? Meye yarinyar daya kakkaɓe idonshi ya mata liƙe take masa , Dikko baya zina ya akayi wata macen ke riƙeshi waje har yakai 3 dare bai dawomin gida ba ? 

     Jamila Musa gareki…….


      Jama’a duk wanda ya kalli labarin nan yasan tuni na yankeshi , naso kuyi haƙuri kubi labarin yadda yazo min , ba labarin zamu kalla ba darasin ciki zamu ɗauka , amma sai kuka firgitani , idan kunyi nazari shi labarin rayuwarka yasha banban da labarin shaka tafi , ba ƙirƙira bane ba da zan rubuta muku yadda kuke so ba , kowa da yadda Allah ya rubuto mishi jarabtarshi , kuma babu wanda ya isa ya goge ƙaddar rayuwarshi a yadda tazo ,

     Maganar lalurarshi , yace Ashiru yaji da komai , kuma duk Dady baisan anayi ba , bai faɗa masa ba saboda baya so Dady ya saki matarshi dan kar Momy tayi baƙin jini , meya faru bayan Mustapha yakai Ashiru wurin daya ce nan ne asirin yake ? Ya aka ƙare ne ? Ina Al ‘ Ameen ? Ya mutu ko yana raye ne ? An dai buga mishi lamba haka Dikko ya faɗa tunda bashi nan baisan abinda ya faru ba , Al ‘ Ameen daya fita daga inda Dikko ya tsareshi ina ya tafi ? Me yayi bayan ya fita ? Meya faru ? Koma dai miye idan ta amince zakuji ya warke ko yana tare da matsalar ne………….?

      Duk mai imani yasan akwai jarabta , ni naso na rubuta muku yadda duk zamu ƙaru gaba ɗayanmu , naso kuji yadda Sultana tayi rayuwarta a gidan Dikko dole ta nan zamu warwaro matsalolinmu ,  mu fahimta inda muke da gyara kuma mu gyara , amma sai kuke cewa bana san Sultana ina bata wahala , bayan bani bace na ɗora mata ba , wasu kuma sai suke zagin Dikko , wasu Sultana , wasu kuma niɗin suke zagi babu gyara babu dalili , daga gyara kayanka ai bai zama sauke mu raba…..?


     Nidai ina san insan yadda kissa da kisisina da kuma kwarkwasa take , tafiya magana kallo da dai sauransu , mi ke kawo yawan mace²n aure ? Tou idan mai labarin ta yadda zaku jini , salon labarin zai dawo muku da wannan tambarin….. ????????


         *KWARATA RETURN…*

  _{Ƙalu bale gareku matan aure….}_


*SAINA AURI DK*

      


     Labarin zaizo muku a kyauta ne kamar dai yadda wannan yazo , bana siyarwa bane ba , 


    Ga dai .

*JIDDAH*
*MARDIYYA*
*HAFSA*
*YUSRA*

         Kowa a cikinsu saita auri Dikko , su suna waje An mata a cikin gida , gadai Yusra tana riƙe Dikko yana kai 3 na dare yana waje , shi baya zina tou dame take riƙeshi wanda har yake tafiya wurinta yabar matarshi ? Me ta iya wanda Sultana ta raga mishi ? Sultana zata yadda kuwa wata ta shigo ? Koma dai miye idan ta amince zaizo a cikin sabon labari mai taken.


*KWARATA RETURN*


Alhamdulillah jama’a , Jamila tana godiya sosai , sai Allah ya haɗamu a sabon littafina in Allah ya yadda ????????

*ƁOYAYYAR SOYAYYA…*


     Gasuwa ta musamman gareka *IBRAHIM MUSA QERAU* { Alhajeje } ngode sosai da ƙoƙarin da kayi mana , muna godiya sosai daga kai har mutuminka Mai gida DK , ngode׳ sosai. 


    Godiya gareku “yan uwana , ngode sosai da irin taimakon da kukemin , wurin ganin kun tayani yaɗa wannan labari , ngode sosai da ƙauna Allah ya daɗa zuminci. ????????

*SA’ADATU* {{ AUNTY MUSA }}
*HAWWA MUSA* {{ F JIDDAH }}
*RABI MUSA* {{ MRS USMAN }}}


BISSALAM.

      MASOYANA ???? na barku lafiya , ina matuƙar kewarku cike da maraicinku……. 


       *RUƘAYYA MATAWALLE* , ina godiya da kyautar rake…… ????




26/12/2019 ????????



Daga alƙalamin 



*JAMILA MUSA QERAU…*  ngode ׳ Allah ya sake haɗamu da alkairi.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button