KYAWUNA JARAFTA TA 1-END

KYAWUNA JARAFTA TA Page 1 to 10

Idar da sallan tayi ta tashi tazauna akan gadonta tareda cire hijabin ta ijiye agefenta tana kallon yanda duk suke shiryawa agurguje, suna makeup abin na bata sha’awa dan ita mai kadai na shafawa gareta sai body spray, batada sauran kayan kwalliyan dasuke dashi kuma bata isa ta taba abinsu ba barinma masifaffiyan Hawwa nan. Daga Hawwan har Nana saka atampopi sukayi iri daya suka shirya tsaf gwanin ban sha’awa sanan kowacce ta zauna kan gado tana danna waya, sosai take kallon wayan dasuke dannawa, duk idan taga suna tabawa saita bata shaawa kaman taje ta karba amman tasan bazama su bataba, duk suna zaune ahaka kowa nawasa da wayanshi banda ita dake kallonsu kaman tasamu film aka bude kofa dasauri duk suka daga kansu suka kalli kofan, Abba ne yasaka lafiyayyan shadda mai ruwan toka da hula akanshi yana tsaye daga bakin kofa batare daya shigoba yakalli su Nana yace “kufito kugaida Abokan aikina da matansu” yana maganan yasaki kofan yay gaba duk tashi sukayi harda ita cikeda wani irin murna koba komi yau zataga wayanda bayan gidansu ba, hijabinta tadauka tasaka sanan tabi bayansu  Nana dasukai gaba batareda sun cemata komiba suka fito Abba na tsaye kan stairs yana jiransu su fito yagansu, hada ido yayi da Du’a dake nonnoke kai, ahankali yace “ke banda ke koma daki ki zauna” wani irin murmushi Hawwa tayi ranta fess jin ankorata, Gyadama Abba kai tayi ahankali cikeda mugun sanyin jiki tajuya ahankali tashiga daki tareda maida kofan tarufo daidai lokacin Hamad yafito daga dakin Mum dinshi, hada ido Abba yayi dashi yace “let’s go tunda kafito” shida Abba suka jera yaran kuma abayanshi har zuwa kasa. 

Abokanen aikinshi ne su uku da matayensu da yaransu kanana  suna ganinshi Babban cikinsu yace “what a nice family kakedashi HOD” dan murmushi Abba yayi yakaraso wajen yabasu hannu sukuma yaran suka shiga gaida kowa, Mami da Mum da Uwani suka shiga kawo abinci da kayan kwalama, ahankali Mami kebin kowa na falon da kallo saikuma tasauke ijiyan zuciya ahankali, daya daga cikinsu yace “wayan nanne kadai yaranka HOD”? Gyadamai kai yayi yace “eh” ahankali Mami dake kokarin bama matar abokinshi plate na snack tadan saci kallonshi saikuma tai murmushi tacigaba da serving while Abba yacigaba da magana yanuna Hamad yace “wanan shine first son dina Hamad he’s 30, yakaranta engineering” dasauri bakin sukace “like father like son” danshima engineering yayi yanzu shine HOD engineering department a BUK, murmushi yayi yace “yayi joining NDA yanzuma wani program yakeyi anan kano saisa yakenan, sai Aisha” yanuna Nana yace “muna kiranta da Nana dan tanada sunan Mamana, ankusa bikinta nan da bayan salla, sai Hawwa sai Du….” Shiru yayi dasauri saiya nuna Amal yace “sai Amal, Aneela, Asiya da Muhammad da Mudasir, yarana takwas” “wow masha Allah, nice family wlh, Allah ya rayamaka su kaga aurensu” murmushi Abba yayi yace “Bismillan ku mufaracin abinci” nan aka shiga cin abinci akai shiru, ahankali Hamad yatashi yay excusing kanshi yay sama binshi da kallo mahaifiyarshi tayi babu daman kiranshi sabida bakin dake wajen.

Dakinsu Du’a yabude yashiga tareda maida kofan yarufe sanan yajuyo ya kalli gadonta, a kwance yaganta tarufa da hijabinta, ajiyan zuciya yasauke aboye sanan yashigo dakin yace “Hey Duudo look what i got for you” shiru tayi kaman tana bacci taki motsi, ahankali yasa hannunshi yakama kafafunta yadagasu sama sanan yazauna abakin gadon sanan yasaukar da kafafunta kasan gadon tareda saka hannu yaja hijabin data rufe fuskanta dashi, dasauri ta yunkura zata juya fuskanta kawai yadagota yace “come here Du’a” sata yayi ajikinshi kaman jira take ta kankameshi sosai sai kuka, ko kadan baiyi attempting hanata kukan ba, duk kanninshi babu wanda yakejin tausayinta yake kuma so kaman Du’a sabida tafi kowa rauni, he don’t care about kalaman da family su suke fadi akanta ana cewa itaba yar Abba bace, mayya ce, yar aljanu ce bla bla bla, all he knows is Mami da Abba suka haifeta and she’s his little sister kuma yanason kanwarshi sama da tunanin kowama.

Cikin kuka tace “Ya Hamad ni wlh inaso namutu” dasauri yacirota daga jikinshi yace “ke are you crazy? Karki kara fadin haka” bayan hannunta takai tana share fuskanta tace “Abba bayasona, Mami bata sona, Mum ma batasona, Kaka ma batasona, kaga ni kadai Abba ya tsana ayaranshi, yakorani nakoma daki dazu, kuma kaga yace yaranshi 8 yacireni daga cikin yaranshi, kullum ina kulle adakin nan kaman mayya, dama Kaka tace ni mayya ce ni aljana ce, sabida ni kadai aka haifa daban bana kama daku does that means am a witch ko aljana eh Ya Hamad? Ya Hamad bakacemin kananan ranan da aka haifeni ba kuma kace Mami ta haifeni maisa su Aneela dasu Muhammad da Mudasir kadai takeso eh? Ya Hamad babu asibitin dake chanza kalan fatan mutum ka kaini naje nakoma kalan yan gidan mu sabida Mami na da Abba su soni nima eh Ya……..” hannunshi yadaura akan lips dinta yace “ya isa haka listen to me all abubuwan nan dakikaga Abba da Mami nayi bawaidan basa sonki bane sunayine to protect you, Du’a tun kina primary school ansha ayi attempting ayi raping naki nasan lokacin kina yarinya ba lallai kituna ba, but kin tuna lokacin dakike JSS 2 abinda teacher ki da Abba ya kulle yamiki ko” runtse idanunta tayi dakarfi alamun ta tuna, hakan yasa ahankali yakai hannunshi yakama hannuwanta guda biyu yace “listen to me, Abba is only trying to protect you, Abba bai tsaneki ba” ahankali cikeda raunin murya tace “amman yana kunyan ya nunani amatsayin Babana” tai maganan tana kallon Ya Hamad kurii da manyan idanuwanta dayasa yakasama mata karya dan to some extend all abinda take fadi gaskiyane, ahankali kawai yajawota jikinshi ya rungumeta yakai hannunshi yashafa gashinta murya chan kasa ta yanda dagashi sai ita sukeji yace “kin tuna abinda nake yawan fadamiki” gyadamai kai tayi ahankali ajikinshi hakan yasa yace “fada inji” murya chan kasa hawaye nabin kuncinta tace “Du’a kome kikaga yana faruwa arayuwanki Allah yasan dake, jarabawanki ne, karki kaucema Allah karki butulcemai, bake kikai kanki ba Allah ya yoki, love yourself, kiyi imani da Allah kikuma dage da addu’a watarana sai labari my beautiful little Duuudo” suka karashe maganan atare hakan yasa takara kankameshi, murmushi yayi sanan yacirota daga jikinshi, handkerchief yaciro daga aljihunshi yace “now let’s wipe those tears no more kuka okay” gyadamai kai tayi tareda murmushi yan kananun white teeth dinta suka bayyana, sharemata fuskan yayi tass sanan shima yamata murmushi yace “idan bakin nan suka tafi zan dauko miki sababbin novels din dana sayomiki kinji” gyadamai kai tasakeyi, kumatunta yaja yace “idan kika sake kuka saimun bata” dasauri tace “bazan sakeba” “kinci abincin dare?” Girgizamal kai tayi, tashi yayi yace “bari naje nakawo miki saiki bani labarin wayan nan novel din” gyadamai kai tayi yawuce yafita yana murmushi, Allah yamata brain, english novels yake sayomata dasukakai 1000+ pages cikin 2days tagama kuma tsaf zata bashi labarin novel din, abinda yataimaka mata da english ma kenan.

Bai wani dadeba yadawo dakin da bowl na hadadden pepper soup da cow head, kafinma ya iso ta tashi tsaye dasauri tace “Ya Hanad kaman pepper soup ko” bata plate din yayi yace “mayyan nama kawai” dan tana balain son nama tun tana yarinya, murmushi tayi takarba dasauri tazauna tashiga ci ya tsaya shikuma yana kallonta, she looks so happy hakan made him so happy, dan yarinya ce da dawuya kaga she’s happy saisa anytime she looks happy happiness dinta is infectious sai kawai kaji kaima ka kamu da farin ciki. Juyowa tayi takallai tana tana naman kaman wata yar baby looking so adorable ganin ita yake kallo yasa tamikamai last piece na meat din tace “zakaci” hararanta yayi yace “marowaciya sai yanzu zaki bani to banci” dan dariya tayi tace “yakuri bari naci wanan gobe saimuci tare, Ya wai yaya ake dafa nama ne”? “Har yanzu ba’a barinki ki shiga kitchen?” Gyadamai kai tayi tace “ba Kaka tahana ba” gudun karta tunakomi dan yanzun nan kuma tahau kuka tasa yace “zan sayo nama saina koyamiki a kitchen din side dina” sosai tashiga jin dadi tana tauna namanta bude kofa akayi dasauri dukansu suka waiga, Mum ce fuskarta amurtuke, wani mugun kallo tama Hamad tace “mena gayamaka? Zokabar dakin nan” tai maganan tareda nunamai kofa, tashi yayi ahankali batare dayamata gaddama ba yazo yabita gefenta yafice, shigowa dakin tayi tazo har gaban gadon Du’a data sauke kanta kasa tana rikeda bowl din pepper soup din data cinye tace “ke bazakiji da bakin jinin ki kinemi yanda zakiyi ubanki yama yarda cewa ke yarshi ce ko yadinga lissafawa dake cikin yaranshi kina nan kina nema kisama dana bakin jininki ne, sabida kinga yanda ubanku keji dashi first son dinshi ga ilimi ga kyau shine zaki biyo tanan, to ta Allah batakiba bakar mayya kawai, kijechan kiji da kanki, na tsani uwarki amman naga matsalan da haihuwanki kesata ciki wlh har tausayamata nake, wayama sani ko wani aljaninne yadura mata cikinki dan naji ance tayi aljanu datana gida da kyar namijin dare yamabarta tai aure” ahankali tashare hawayen daya zubomata sharr babu abinda ta tsana irin adinga kiranta da yar aljanu ko mayu, Mum tasake wurgamata mugun kallo tace “wawiya dakikiya kawai babu abinda tasani sai zaman daki, kannenta ma sunfita iya karatu sunfiki iya komi Babanki yamaidake gidahuma  yaryar aljanu kawai” wanan karan fashewa da kuka tayi sosai takai hannunta tadaura kan fuskanta tana kuka, murya chan kasa ta yanda Baza ajiba tace “niba yar aljanu bace” da sauri Mum dake tsaye kanta tace “me kikace Du’a? Mayarmin da magana kikayi? Did you just talk back at me eh?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button