KYAWUNA JARAFTA TA 1-END

KYAWUNA JARAFTA TA Page 1 to 10

Takai morethan 15min awajen kuka take sanan wani irin zuciya yadibeta ta tashi tai ciki ta kofan kitchen tabi Mami na kitchen tana kwashe abinci amman ko kallonsu batayiba tana kuka tawuce fuuu ta tafi falo tashiga Mum dake zaune tareda Hawwa suna magana ne sukaga shigowan Nana tana kuka sosai bamata luradasuba tai hanyar stairs dasauri Mum tamike tace “Nana ke lafiya gani nan anan, menene kike kuka haka”? dawani irin sauri tajuyo tadawo batai wata wataba tafada jikin Mum tazube sai kuka, daga Mum har Hawwa rudewa sukayi, Hawwa tace “Ya Nana menene fada kukayi da Muhsin ne” cikin kuka sosai tace “Mum Muhsin yace yafasa aurena wai Du’a zai aura” chak Mami datafito rikeda kula ta ijiye kan dinning ta tsaya dubus awajen tana mamakin mekuma yakawo sunan Du’a a zancen su. Mum dama tarude sabida yanda yarinyar ke kuka tace “Du’a kuma, ta ina Muhsin yasan wata Du’a dahar zaice miki zai aureta iyye, kinsan mekike fadi kuwa”? Mum tai tambayan sounding so confuse and shocked dan batagane kan zancen yartataba, cikin kuka sosai Nana tace “Mum bayan nadauki zobo naje kaimai ajikinshi naga Du’a suna hira haryanama tabamata gashi taciremai dankwali, kuma idan karya nayi kije garden tama barmai dankwalin ta har novel dinta awajen ma” cikin wani irin mugun zuciya jikin Mum har kyarma yake tashiga kwalama Du’a kira.

“Du’a! Du’a!!! ki sauko kasan nan dakanki kafin nazo dakin nan wlh dan na lahira zai fiki jin dadi” bude kofa tayi ahankali tashiga saukowa idanunta sunyija sabida kuka tashiga saukowa daga stairs hada ido tayida Mami dake tsaye a dinning tana kallonta kaman yanda itama take kallon Mami, kasa karasa saukowa tayi Mum tace “zaman lafiyanki shine ki amsa tambayan dazan miki batare dakinmin karyaba inba hakaba yau saina kusan nakasaki wlh, kin sauka kasa ko baki sauka kasaba”? kama jikin skirt din lace dinta tayi gam gam tsabagen tsoro tana kallon Mami tsabagen tsoro sanan ta kalli Mum tace “bayan nai salla shine ta window na leka naga su Aneela nawasa a compound shine nasaci hanya ta kitchen nafita, to naji muryanku a kitchen shine na kwasa da gudu sabida kada ku ganni wlh wlh ni bansan da mutum a garden ba tuntube nayi dashi zan fadi shine yataroni” fashewa da kuka tasakeyi sosai tace “wlh wlh ni banma sanshi ba Allah kuwan Mum” 

  Cikin wani irin bakin zuciya Nana tai inda take a stairs wani irin finciko gaban riganta tayi ta chakumeta tace “karya kike baki sanshi ba, kinji ina waya dashi jiya da daddare munyi zaizo yau saisa yau harda cin kwalliya haka sabida ki kwacemin wanda zan aura ko, baki sanshi ba ubanme mikikeyi ajikinshi”? Cikin kuka sosai tace “wlh Ya Nana niban shiga jikinshi ba hannuna yarike kuma inata kokarin na kwace yaki sakina, shine yazo zai tabamin gash……” wani irin kishine ya kwashi Nana tawani kaimata mugun duka abaki bata cire hannu ba sai jini bakinta tasake fashewa da kuka, kimarta Nana tashiga yi baji bagani Mum tace “yima shegiyar yar Aljanun mugun duka Nana, yimata jina jina, itada uwarta sunga kinyi miji daga gidan arziki shine aka turata tayomiki kwace tarabaki dashi, duniya inhar baka mutuba baka gama ganin abin kallo ba, kimeta da kyau kyan datake takama dashi ki chanza mata halitta” yanda Nana ke dukanta tana bubbugata da kome tasamu yasa tafara ihu tana mika hannu tana kwalama Mami kira dan bata iya fadaba bamatasan yanda zata fara dukan yartaba kwata kwata, ahankali Mami tajuya tacigaba da arranging dinning table din datake, kannensu dake wasa ihun dasukaji yasa duk suka shigo ciki suka cika falon, Aneela tafashe da kuka sosai ganin yanda ake dukan yayarta. 

Juyawa Mum tayi takalli dining ganin Mami tajuya tacigaba da arranging dinning abinta yasa tai wani irin murmushin mugunta tace “barka mata shegen rigan nan dataje tana kokarin kwacemiki miji dashi kannenta suganta taji kunyan duniya” wani irin bugata da tiles Nana tayi jikake kum Nana tawani juyarda ita tawani yage zip din riganta tanajan rigan zata ciremata, rike rigantayi tana kuka sosai tace “Ya Nana yakuri, Mamiii” tasake kwalama Mami kira dan mugun kunya take aganta, Mum da ranta fess dan tadade tanason gumama Mami amman tarasa ta yanda zatayi saiyau Allah yabata dalili mai kyau tace “fizge rigan duniya da kannenta suga abinda take boyewa, haka akema yan iskan yara masu son kacema yayyinsu mazajen dazasu aura, fizge rigan kannenta suga nonuwan marasa fasali” fizge rigan Nana tayi tayar Mum tace “yara ku kalleta kumata woyiiii” su Muhammad sukahau woyiiii dan basusan meke faruwaba yarane, throw pillow kan kujera taja takankame tana boye kirjinta, Nana tawani sake dauketa da mari tahau ruwan cikinta tana nausa daidai lokacin Abba da Hamad suka shigo dakin, shiru yaran dake woyi sukayi jikake dakin kaman andauke wuta sai muryan Du’a da baima fitowa da kyau tana kiran Mami Mami take, awani irin zuciye Abba yay wajen wani irin dago Nana yayi tsaye sanan yakai mata lafiyayyen mari Pau!!!!!! 

Dasauri Mum tace “idan duka zakayi Alhaji ni zaka daka danni nasa Nana tama shegiyan makiran yarinyar nan duka tacire mata riga kannenta sumata ihu” wani irin kallon Mum yake kafin yabi kowana dakin one by one da kallo sanan idanunshi suka sauka kan Mami dake dining tana arranging kula cikin kakkausan murya yace “Zainab kina nan wajen kina tsaye zasu kashe Du’a can’t you intervene, wani irin banzan hali ne wanan” juyowa tayi takalli Abba idanunta sunyi ja sosai cike da tsananin kunci tace “Dadyn Hamad mekakeso nayi eh? mekakeso nayi? Ya zanyi da raina?Tun ranan dana tsugunna na haifo wanan yarinyar duniya nake shiga bala’i kala kala? Babu kalan shairin da ba’a yimin ba kan haifo yarinyar nan, tunda na haifi Du’a  ban kara samin kwanciyan hankali ba, kome yasameta ita tajama kanta kahanata fita waje ubanme yakaita garden? Gasu gatanan idan suka kasheta kaga kowama yahuta daman tun ranan dana haifota tazamema kowa kashi a wuya ankasa taunata, ankasa fitoda ita, ankasa hadiyeta, nima nagaji I am tired of everything, I’m tired” kawai saiga kuka yazo mata dasauri tabar dinning din tawuce sama tabude dakinta tashiga abinta.

Juyoda kanshi Abba yayi yakalli Mum da Nana dake kuka itama yace “kuwuce kuje kujirani adakina” wucewa sukayi sama, sanan ya kalli yaran yawani daka musu tsawa yace “to your room dukan ku” dasauri kowa na falon ya watse, Abba yajuyo yakalli Hamad yanunamai riganta yace “bani riganta” wucewa yayi yadauko rigan shikuma Abba ya tsugunna yatallabota zuwa jikinshi yana kallon fuskanta yanda goshinta ya kumbura ga bakinta jini, gefen fuskanta yay ja sosai, bashi rigan Hamad yayi Abba ya karba sanan yakama hannunta yasamata rigan kafin yarufe mata kirjinta dashi sanan yaja throw pillow data rufe kanta dashi ya yar sanan yasamata dayan hannun rigan yadagota zai  saka mata zip tafashe dawani wahalallen kuka sosai ahankali Abba yace “ina ke miki ciwo”? Cikinta ta nunamai, daga riganta yayi yakalli cikin ga alamun naushi nan duk sunyi jajja, Hamad dake tsaye kansu yace “Abba bazamu kaita hospital ba kuwa what if tanada internal bleeding” girgiza mai kai Abba yayi yace “get me a towel and hot water da rob” wucewan kitchen yayi dasauri yakawo ruwan zafi da towel.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button