KYAWUNA JARAFTA TA Page 11 to 20

Saukowa Mami tayi taci sabon kwalliya Mum tabita da harara tace “kidaiyi kigama gobe zan karbi girkin” serving Abba tayi sanan tazauna gefenshi tana bashi duk wani abu dayake bukata.
???? KYAWUNA JARABTA TA ????
✍️M SHAKUR
Free page
EPISODE 6️⃣
Bayan sallan isha’i Abba baima dade da dawowa daga masallaci ba shida Hamad dasu Muhammad ba mai gadi yayi sallama izini Hamad yabashi yashigo, shigowa yayi har gaban Abba yace “barka da hutawa Alhaji, kanada baki, sunce wai Alhaji Ibrahim mai tabarau ne” kallon Abba Hamad yayi yace “Baban su Muhsin ne Abba” tashi Mum dake zaune afalon tayi ta kalli su Muhammad tace “yara kuwuce mutafi sama Abban ku yay baki” binta yaran sukayi sukai sama, kallon mai gadi Abba yayi yace “kamusu iso” Maigadi yawuce yatafi, Hamad yakalli Abba dayaganshi anatse yace “Abba yaya zamuyi idan dagaske Muhsin yake”? Murmushi Abba yayi bai bashi amsaba yace “just stay here and learn, duk randa bani kaine zakai making decision akan kannenka mata” gyadama Abba kai yayi daidai lokacin mai gadi yay sallama yabude kofa yashigo dasu hakan yasa Abba da Hamad suka tashi don agaisa, wasu Manya manyan attajirai ne su uku sai Muhsin dake taredasu kana ganinsu you don’t even need an explanation kasan masu hannu da shuni ne, hannu Abba yamika musu cikeda girmamawa suka gaida dan mahaifin Muhsin ne Alhaji Ibrahim maitabarau sai kannenshi guda biyu Alhaji Isyaka Maitabarau sai Alhaji Mubarak Maitabarau, sosai Abba yagaisa dasu cikin mutuntawa yasa suka zazzzauna Muhsin shima ya gaida Abba cikeda girmamawa ya amsa, Hamad ma yagaidasu suka zauna cikeda girmamawa, shigowa Uwani tayi takawo drinks da ruwa sanan tawuce falon yay shiru.
Gyaran murya Mahaifin Muhsin yayi yace “To bari mufara da kalamai mafi kyawu wato da Sunan Allah Mai Rahama Maikuma Jinkai, Alhaji kaganmu agidanka da dare haka kuma unannounced ko, bawani yakawomu nan ba sai wanan yaron” yanuna Muhsin dake gefenshi da kanshi ke kasa, sanan yakara sauke ijiyan zuciya yace “wlh Alhaji idan nace namasan ta yanda zanmaka bayanin nan kafahimta tonamaka karya amman bari nafara da tantance gaskiyan lamarin kafin nakoro bayani” yay dan shiru kafin yanisa yakalli Abba kaman yanda shima yake kallonsu yace “Alhaji wai dan Allah kanada y’a mai sunan Du’a ne? Danni wayanda muka sani shine wanan Baban dan naka wato Hamad, Aisha, Hawwa, Amal, Aneela, Asiya da Muhammad da Mudasir, dan Allah katabbatar min da gaskiyan lamarin nan kanada y’a mai sunan Du’a ne wacce duk bamusanta ba”? Shiru Abba yayi yana kallonsu kaman bazaice komiba danhar dagakai Hamad yayi yana kallonshi sanan yadan nisa yace “eh inada y’a mai sunan Du’a” ahankali Baban Muhsin yace “to Alhamdulillah, nasan banida wanan hurumin dazan tambayeka maisa baka taba ambato mana itaba ko wani abuba dan nasan kanada dalilinka nayin hakan, daman tabbatarwan kawai ita nake bukata tunda yanzu ka tabbatarmana kanada y’a mai sunan Du’a toga dalilin da yakawomu wurin ka da daddaren nan” ya sakeyin shiru sanan ya numfasa yace “shi so hallitan ubangiji ne, danhaka so gaskiya ce hakama ki, Alhaji d’ana yazo gidanka jiya sai cikin iko irin na Ubangiji yaci karoda yarka Du’a kuma Allah ya jarabceshi da sonta ainun aranshi danyau haukace mana kawai ne baiyiba ga kannina nan katambayesu kaji, yace shiyabarma Nana duka abubuwan dayamata amman yafasa aurenta dan baya sonta Allah yahadashi da Du’a ita yakeso itakuma yakeson Ya aura inhar ka yarda zaka bamu” tunda suke maganan Abba yake kallonsu babu ko kyafta ido, yakai kusan minti biyar ahaka baice komiba dakin tsit kakeji sanan yay gyaran murya yace “to Alhamdulillah naji dadi yanda kukazo kukasamen, shi gaskiya dayace koda batada dadin ji, naji dadin yanda kuka sanardani gaskiya batare da kwana kwana ba ko kuma boyeboye ba danhaka nima zan sanardaku gaskiya Alhaji” yay maganan cikin mugun hikima da ilimi sanan yace “it’s very okay idan danku Muhsin yaji bayason y’ata bazai aureta ba shi aure daman yagaji haka ko anyi ana rabuwa, amman gaskiya itace bazan iya bama Muhsin wacce yaji yakeso dinba wato Du’a” dasauri Muhsin yadago kanshi yakalli Abba idanunshi sunyi jaaa sosai.
Abba yacigaba. “Alhaji kai mahaifine haka nima mahaifine, yanzu wani yazo yana tareda yarka har a kusa bikinsu sai yaga kanwarta yace yafasa aurenta kanwar yakeso zaka yarda kabashi”? Abba yamai tambayan shiru Baban Muhsin yayi yakasa amsa tambayan, Abba yace “duk wani abinda zai raba kan y’ay’ana ko family na bazan taba yinshiba, gwara afasa auren gabadaya da inbaka wata, dan haka I am sorry idan maganata ko amsata bata kuma dadi ba amman bazan iya baku auren Du’a ba, as for kayayyakin dakuka kawo duka in sha Allah zamu aiko muku dashi, Allah yasa hakan ne yafi alkhairi”
Kafinma Baban Muhsin yayi magana Muhsin ya rarrafa da gudu zuwa gaban Abba, kneeling yayi yahade hannayenshi biyu muryanshi narawa kaman wanda zai fasheda kuka yace “Abba Abba wlh wlh wlh na rantse da Allah bawai dan cin mutunci ko toxarci kodan inci zarafin Nana nai hakaba, wlh kawai Abba azuciyata naji bana sonta wlh tunda nasa Du’a a idanuna nake so ko kulkewa nayi saina ganta, Abba kataimakamin dan Girman Ubangiji” tunda yake maganan daga Abba har Hamad kallonshi sukeji, ahankali Abba yasa hannayenshi yakama hannun Muhsin dayake rokonsu dashi yace “Son kayakuri kotayaya zaka roken I don’t think I can risk my family for this, I can’t stand naga kan family na ya rabu sabida one bad decision dazanyi ba, bazan iya baka Du’a ba, it’s final” to Abba biggest suprise kawai yaga Muhsin yafashe da kuka sosai, daura kanshi yayi kan cinyan Abba cikin kuka yace “Abba wlh idan baka bani Du’a ba zan iya mutuwa dan Allah kayakuri, I am sorry if I hurt you sabida nace banson Nana….”
Iyayenshi kasa koda motsi sukayi, sunsan Abba made the right decision dankosu basuso sunzo ba mugun so da gatan dasukema Muhsin dinne yasa sukazo su gwada luck dinsu.
Ganin yanda Muhsin ke kuka yasa zuciyan Babanshi yafara breaking shifa baida wanda yakeso kaman Muhsin aduniyan nan, kallon Abba yayi yace “Alhaji name anything dakakeso wlh zan maka indai zaka bama dana Du’a dinan dayakeso, kaga wlh zan iyasa acireka daga matsayin HOD dinan abaka Deen na BUK gabaki daya, idan bakaso zan baka aiki akasan waje, wanan gidan na chanza maka nabaka lafiyayyen gida anan GRA kano, mota kudi koma mekakeso just name it zan baka inda zaka hakura kabama yarona wacce yakeso kaganshi nan shikadai gareni kataimakamin please” sake tashi Muhsin yayi daga jikin Abba fuskarnan nashi hawaye ya wankeshi yahade hannayenshi yana kallon Abba, dan murmushin manya Abba yayi yace “I am happy da position da dukiyan da Allah yamin a rayuwa bana bukatan kari, nariga nayi maganata idan babu matsala zan haura sama inada y’a mara lafiya naduba, Hamad you can see them off okay” gyadamai kai Hamad yayi Abba yatashi, sosai Muhsin yafashe da kuka, kanin Baban Muhsin Alhaji Mubarak yatashi yay wajen Muhsin yace “Kato dakai kana kuka, ga matanan agari kaman ledan pure water kodaga kasan waje kakeso kayi aure Babanka zai auromaka tashi mutafi” kintashi yayi saifada sukayi da gaske suna dagashi sanan suka fitardashi daga falon Hamad yatashi yarufe kofa jikinshi a sanyaye.