KYAWUNA JARAFTA TA Page 11 to 20

koda Abba yatafi sama dakinsu Nana yabude yashiga, bin kowa nadakin yayi da kallo Nana na kwance kaman mara lafiya idanunta a lumshe sai Hawwa ce idanunta biyu, tana ganin Abba tace “sannu da zuwa Abba” gyadamata kai kawai yayi yakalli Du’a dake barci har lokacin sanan yajuya yafice yakoma dakinshi, ko zama baiyiba Mum tabude kofa tashigo dakinshi, juyowa yayi yakalleta sanan yazauna akan kujera yana ganin idanunta kadai yasan taji duka maganganunsu a falo dan idanunta sunyi ja kaman ma hardan kukan bakin ciki tayi. zama yayi kan kujera yana kallonta, daurewa tayi tahadiye abinda ya tsayamata arai tace “yakukayi dasu Alhaji” jaridan shi dakekan table yadauka ya gyara zamanta akan hannunshi sanan ya kalleta yace “idan Allah yakaimu gobe duk wani abu na gidansu Muhsin ki tattarasu tass zansa azo adauka amayar musu” wani irin faduwa da rawa gabanta keyi dan babu kalan burin dabata dashi akan auren Nanan ta da Muhsin, finally yarta zatai rayuwa gidan masu kudi shine tashi daya kaman aradu zancen aure yamutu, daurewa tayi tace “does that mean babu zancen aure? Ba za’ayi auren Nana da Muhsin ba kenan?” bude jaridanshi yayi zaifara karantawa yace “eh babu zancen aure, Allah yabata wani mijin nagari” yay maganan tareda gyara zama kan kujera yana karatun littafin shi dakyau sosai take kallonshi jitake kaman tarufeshi da duka tsabagen bakin ciki, wai ace anfasa auren yarsu 26yrs finally year student din yarsu, yarinyar dayasan tanason Muhsin dinta yau all of a sudden amman this guy is still acting kaman it’s nothing, jitayi idanunta sunjuya sama wutan bala’i nacimata zuciya tajuya fuuu tafice ko tsayawa kulle mai kofa batayiba tana fita tacikaro da Hamad daya hauro sama zaizo yaduba Du’a, idanunta kadai yagani yasan ba lafiya hakan yasa yajuya dasauri zai koma dasauri cikin mugun ihu tace “dan ubanka wlh katafi saina tsinemaka albarka agabanka aka fasa auren yarka bakai komi dan taimakon lamarin ba dawonan” juyowa yayi ahankali sanan ta shiga kwalama yaranta kira. “Amal Asiya” dasauri suka fito daga dakin su harda Aneela yar Mami, jin ihun Mum tasa Mami itama tafito, kama hannun yaran tayi tawani irin tura kofan dakin yaran, yanda kofan yay mahaukacin kara yasa Du’a ta firgita sosai ma tabude idanunta, shigowa Mum tayida Hamad da Amal da Asiya, sanan ta kalli Nana da Hawwa daduk ita suke kallo tace “Nana saurareni kiji anfasa aurenki, Muhsin har kuka yake yakama kafan ubanki yana roka abashi wanan yar Aljanun” tanuna Du’a, dasauri Hamad yace “Mum please stop all this bahaka ake handling situation like this ba sokike zuciyan Nana yabugu eh”? Cikin bakin masifa Mum tace “buguwa na nawa kuma” tasake juyawa takalli Nana da kallonsu kawai take kaman gunki tace “Nana Muhsin yace bazai aureki ba yanzu haka ubanki yace ahada komi nasu harda akwatin dasuka kawo naki amaidamusu abinsu gobe dasafe” kokarin yunkurowa take tatashi tasauko daga gado kawai jiri yadebeta ta yanke jiki zata fadi dawani irin sauri Hamad yatareta yace “Nana Nana” juyowa Mum tayi takalli Mami data tsaya daga bakin kofan tana kallonsu kawai saitaikan Mami shakumo Mami tayi tace “wlh saina kasheki duk abin nan dake faruwa dadi kikeji yarki ta kacema y’ata miji har celebration kike kikaji Babansu daki kina cinshi da rana tsaka” ganin Mum ta shako Mami yasa dasauri Hamad yasakinma Hawwa Nana yatashi daga Du’a har duka yaran kuka suke. “Hajara!!!” Abba yakira Mum da mugun karfi daidai lokacin da Hamad ke cire hannunta daga wuyan Mami datahau tari sosai, Abba cikin fushi yace “tattara yinaki yinaki kibarmin gidana” wani kallo tamai tace “naji zan barmaka gidanka amman wlh saidai nabar gidan da daddaren nan da yarana duka dan bazan taba barinsu da wanan yar Aljanun dakuke raina agidan nanba dansaita hana yarana aure” cikin fushi Hamad yace “Mum wai what is all this eh haba Mum? Auren Nana has nothing to do with Du’a kawai Allah ya kaddara ba mijinta bane, kidena kiran Du’a yar aljanu, Mum this isn’t right mekike koyama su Hawwa ne, haba Mum haba” nuna kanta tayi tana kallonshi tace “ni kake gayama magana Hamad eh” saikuma tafashe da kuka tace “kana gani sabida Du’a anfasa auren kanwarka sanan kace babu ruwanta ba laifinta bane, kanwarka tasami miji gidan arziki gidan hutu kasan gwalagwalai nawane aka samata a akwati eh, har mota ya siyama Nana ranan da aka kaita yace zai bata yarinyar chan tai amfani da tsafin jikinta ta kwacema kanwarka miji kace kaza kaza, nagode Hamad” tashi tayi ahankali tana kuka sosai tawuce tashiga dakinta, zama dirshan Mami tayi akasa takife kanta akafafunta, ahankali Abba yatako yashiga dakin Nana yakalla da Hawwa ta yayyafama ruwa ta farfado sosai take kuka shiru kawai yayi saiyajuya, Du’a yakalla data farka itama tana kuka sosai tana goge idanunta da bayan hannu, fice wa kawai yayi daga dakin. Ranan banji akwai wanda yayi kyakkyawan bacci agidan ba.
Karfe 7:30 Abba yasauko kasa Mami ce kadai a dinning tana hada kayan breakfast, bamataji tafiyanshi ba dan aiki take amman tayi mugun nisa a tunani, binta yayida kallo saikuma ya ijiye jakan aikinshi kan kujera yataka har zuwa dinning Mami bataji zuwan shi ba, hannunshi yakai yakama nata firgigit tafarka tareda juyowa bin fuskanta yayi da kallo idanunta ja da alamun tasha kuka, murmushi takakalomai sanan ahankali tace “ina kwana harka sauko” bai amsa gaisuwantaba yace “tunanin mekike”? kaman bazatai magana ba but ganin yanda ya tsareta da idanu yasa tace “tunani nake kodai mu aika Du’a wajen Mama nane” tsareta yayida mayun idanunshi ya dayasa kawai taji tacigaba da magana tace “Dadyn Hamad understand me kaga sabida Du’a gabaki daya gidan nan babu lpy, Nana tabani tausayi Allah kadai yasan what she is going through wlh is not easy karasa masoyinka, look at Mamansu ga Hamad, in order for peace to rain ni ina tunanin mukaita wajen Mama tai zamanta achan har Allah yasan yanda zaiyi da ita, daga saukanta kasa jiya jibi kalan trouble datajawo” murmushi yadan mata yace “fitanta so daya yajawo wanan matsalan idan muka kaita wani wajefa da bamanan, kinmanta komi ne tun yanzu”? Ajiyan zuciya tasauke takasa magana, murmushi yayi yace “bani abinci inada meeting by 8” gyadamai kai tayi tashiga serving nashi abinci, abincin yashiga ci wayanshi tafara kara ajiye cokalin abincin yayi sanan yatura hannunshi cikin aljihu yaciro wayan ganin mai kirannashi saida kirjinshi yadan buga amman yadaure yakai wayan kunne zaiyi magana aka katse shi.
wani sharp muryan tsohuwa ce kemagana ta wayan. “nasan yau litinin ko ubanme kakeyi kowani kalan aiyyukane kakeyi kabarsu Shafi’u ka tattaro iyalinka tatas banda wanan yar Aljanun kutaho Ikara yanzun nan” tana maganan ta katse, ahankali yazame wayan daga kunnenshi yay jimmm yana kallon Mami da ahankali tace “Kaka ce?” gyadamata kai yayi yace ” jeki shirya yara kowa yafasa zuwa school Ikara zamu yanzu” bude kofa akayi Ahmad yashigo yanasanye da kayan sojoji kafinma ya gaida Abba Abba yace “Ahmad get ready we are going to Ikara” shi kanshi Hamad din baikara fadin wani abubu, saukowa sukaga Mum tayi taci gayu itada yaranta da Nana da idanunta sukai ja sosai tace “mudai mun shirya” ahankali Mami tabi ta gefenta tai sama kaman zata shiga dakinta saikuma tabude dakinsu Du’a ta shiga, zaune taga Du’a kan gado, duka kumburin da fuskanta yayi sun sabe dan dama nan da nan ciwo ke warke wa ajikinta sai idanunta dasuka kumbura sosai, ganin Mami tashigo dakin yasa tabude baki zatamai Mami magana dasauri Mami tajuya tafita dakinta tashiga tadauki hijabi sanan ta tattaro kansu Muhammad da Aneela suka fito, a falo suka sami kowa Abba yace “mutafi” juyawa yayi yakalli Uwani data fito daga kitchen yace “ki kulada Du’a ki kaimata abinci sama zamuje kauyen Ikara” gyadamai kai tayi tace “Allah kiyaye hanya agaida Hajiya” fita dukansu sukayi Mami tadan juyo hada Pido tayida Du’a data fito daga dakinsu ta labe asama idanunta sun cikoda kwalla, Sakai tayi tafice dasauri.