KYAWUNA JARAFTA TA Page 11 to 20

Leka rijiyan dukansu sukayi Bala yace “kace ya iya ruwa sosai ko” gyadamai kai Sharif da kirjinshi ke dukan uku uku yayi yace “eh ya iya amman baitaba shiga rijiya ba” wani irin salati duka gidan aka dauka, wata mata cikinsu takalli Bala tace “incedai ka kira mahaifinta ka sanarda su inma barin ikaran nan subaro sutaho fa dan wanan yarinyar inhar ta rayu to Allah yace kawai kwanan ta nagaba ne” ahankali Bala yace “nariga na sanar dashi” “jama’a Qulhuwallahu kafa bakwai” nan aka fara karatu fa, ganin yayi kusan 2min a ruwan ruwan ma yadena motsi yasa dasauri Sharif ya tsugunna yana leka rijiyan. “Asad Asad can u hear me are you okay? Asad” kana ganinshi kasan hankalinshi atashe yake, kusan 20sec dagama kiranshi saigashi yawani bullo da kanshi daga ruwan yay ihu yace “I got her!” dasauri daga Sharif har duka yan gidan sukahau hamdala, dasauri Sharif yace “what about u are you okay Asad” yana kokarin janyo Du’a kanta yafito daga ruwan gabaki daya yace “we will talk about that when am up there” cirokanta yayi daga ruwan sanan yadaura kanta akirjinshi ya rungumeta ahaka, igiyan dake waist dinshi ya shiga warwarewa sanan yadaura shi kan waist dinta duk acikin ruwan dan kansu ne kawai ke sama sanan yace “Sharif I don’t know if she’s still alive but she is unconscious, na daura igiya a waist dinta, ni zan dingabin matattakala while am holding her kukuma kunajan igiyan waje am I clear” dasauri Sharif yace “yes Asad sanan yatashi dasauri yarike igiyan tagaban Bala yakama ta bayanshi sanan yacilla matan ragowan igiyan yace kuyi layi ku kama igiyan mujawosu waje, duka rike wa sukayi Sharif yace “give us go ahead we are read Asad” hawa matakala daya Asad yayi yana rungume da ita har lokacin sanan yadago kanshi yakalli sama yace “pull us Sharif” jawo igiyan suka shiga yi yana rikeda ita yanabin matattakala har sukakai sama Tsugunnawa Sharif yayi yamikamai hannu da taimakonsu yafito rikeda Du’a akan kafadan shi sanan ahankali yacirota daga kafadarshi ya shinfidar da ita akasa sai alokacin yamaga fuskarta yanda yake kallonta haka kowadake compound dinan ke kallonta, Uwani ce ta rarrafo tana kuka sosai tace “mun shiga uku mun lalace Bala ta mutu jibi yanda takara haske, Innalillahi wa innailaihi raji’un” ahankali Sharif dake gefen Asad yace “Asad tamutu ne”? “I dont know” Asad yabashi amsa atakaice yana dauke idanunshi daga kanta, yace “let’s go” dasauri Sharif yace “check ko she’s alive common Asad, are you this heartless” wani mugun kallo yama Sharif zaiyi magana wata yar tsohuwan dake cikinsu tace “bawan Allah matsamata ciki in ruwa tafito tanada rai idan baifiĀ
to ba ba rai” kaman bazaiyi ba saikuma ya matsa inda take kwance dasauri Uwani ta matsa hannunta ya kalla saikuma yakai hannunshi yakama hannunta yana duba pulse dinta bai sami pulse a hannun ba sai uban sanyi da hannunta yayi kaman kan kara, hakan yasa ya ijiye hannun yakai yatsunshi biyu kan jijiyan dake gefen wuya anan yasami wani very very weak pulse dasauri yazare hannunshi yace “she’s alive” “Alhamdulillahi Rabbil Alameen” yan gidan suka fadi hannayenshi biyu yasa akan cikinta yashiga matse mata cikin da karfi yana kallon fuskanta sai chan ya tsaya yakalli Uwani dake gefensu tana kukan murna ganin tana raye yace “bude bakinta kihura mata iska aciki” dasauri Uwani tazo bude bakinta tayi tahura iska ciki yace “ya isa” daina wa tayi shikuma yacigaba da matsa mata cikin, ruwan gashinshi nabin fuskanshi har zuwa hanci, amman shiru saida yasa Uwani tahura mata iska harsau uku amman shiru hakan yasa Sharif yace “common kai kasan komk nakan harkan ruwa, ka asalin this thing ba kahura mata iskan dakanka mana, let’s help the poor girl” ko kallon Sharif baiyiba yakalli Uwani yace “sake huramata” dasauri tsohuwan tace “bawan Allah kayakuri dan Allah kataimaka mata tafarfado hankalinmu duk ya kwanta inda mahaifiyar ta na nan datakusan mutuwa dan Allah kataimakama marainiyan yarinyar nan da iyayenta basu anan” kaman ya kurma ihu yakeji amman yadai daure da kyar dan matsowa wajen kanta yayi yana kallon pink lips da dan karamin bakinta dazai daura nashi akai, kaman wanda ke tsoro yakai bakinshi gently yana kallon fuskanta yadaura kan nata ko mugun sanyin da jikinta yayine yake shiga nashi oho jiyayi jikinshi yadauki wani mugun sanyi daurewa yayi ahankali yahuramata iskan bakinshi zuwa cikin nata kaman wani magic tarrrr yaga tabude idanunta dasukai wani masifan haske sai cikin nashi suna kallon juna saikuma wani uban tari datayi white tana kallonshi duka ruwan daya taho daga bakinta sai nashi dawani irin mugun sauri yacire bakinshi daga nata yaciro kanshi yajuya yana wani irin kakarin amai babuma wanda ya lurada shi sai wani irin ihu da hamdala da duka mutane keyi na ta farfado tana uban aman ruwa aka zagayeta, ganin yakasa aman yasa ya yunkura zai tashi jiyayi an kama hannunshi gam dasauri yajuyo yakalli hannunshi gani yayi Du’a dake amai sosai tarike hannunshi gam tana kallonshi har lokacin da idanun nan nata da kaman bata hayyacinta, dasauri yajanye idanunshi dagakan hannun yakalli fuskanta idanunta kadan suka budu amman shi take kallo saikuma jikinta yafara bari tana kakkarwa, fizge hannunshi yayi daga nata dasauri yana yarfewa danjjn hannun yayi kaman ya sandare yakalli Uwani dake kanta yace “ku chanza mata kaya ku rufeta shes cold a kaita asibiti” sanan yawuce wanshi batare daya kalli Sharif ba yace “wlh nakai mota baka zona saidai kadawo gida da kafa” dawani irin gudu Sharif yatashi yabishi abaya yana kara waigen Du’a da aka zagaye, mota suka shiga Sharif yaja motan da gudu.
Agaban wani gida mai kama da mansion sukai horn bude musu akayi suka shiga, Sharif na parking yabude mota yafito yana attishawa, daidai wata kyakkyawan mata tana sanye dawani hadadden lace tafito kana ganinta kaga mamanshi sabida kamanninsu tana ganin dan nata ta tsaya turus tana kallonshi ganin yanda yay sharkap daidai nan shima Sharif yafito yana murmushi dasauri takaraso wajen tace “what on earth happen daka jike haka son” ranshi abace yace “lemme shower Ammi” yay wucewan shi, tabishi da kallo saikuma tajuyo takalli Sharif dataga yana murmushi tace “maiya faru yaji ke haka Sharif kaima jibi yanda kai daka daka kaman kai wasa a mud”? Dan dariya yayi yace “aikin Allah mukayi Ammi” aikin Allah? ta maimaita gyadamata kai yayi yace “Ammi we just saved a girl dabadan muba data mutu arijiya wlh, Asad yacirota daga rijiyan nikuma na ciro both Asad and the girl, nima bari naje nai wanka” shima yawuce yabar Ammi awajen baki bude.
Share this
[ad_2]