KYAWUNA JARAFTA TA Page 21 to 30

Wuraren magrib likita abokin Abba wanda shine likitanta tun tana yar karama yazo yadubata allura yamata sanan yabata magunguna Abba ya sallameshi yatafi.
“she’s alive! she’s alive I can feel her pulse” sama sama takejin maganganun nan kaman a eco saikuma chan tabude idanunta sukai clocking da nashi……tarrrr tabude idanunta daga baccin datake tanabin inda take da ko’ina na dakin da kallo, ganin tana dakinsu kan gadonta ne an lullubeta da bargo, mafarki take kenan, mutumin data bude ido tagani dazu yacirota daga cikin rijiya tagani yanzun nan amafarki, ahankali ta yunkura ta tashi zaune ta jingina da bango tana kallon ko’ina ganin gari yama soma wayewa, saukowa tayi daga gado sai alokacin taga wani jibgegiyan akwati da batasan daga ina yazo ba baka kwara daya atsaye gaban wardrobe dinsu, bathroom dinsu tawuce tashiga wanka tayi da ruwan zafi sosai tana karajin karfi ajikinta sanan tafito daga wankan daidai lokacin Mami nabude kofan dakinsu tana shigowa hada ido sukayi da Mami ahankali ta sunnarda kanta kasa tana tuna all maganganun data gayama Mami jiya suna dawomata fresh a memory dinta kasa motsi tayi itama Mami tadauke kai tawuce wardrobe wasu kaya taciro mata tajuyo ta ijiyesu kan gado tace “ki shirya kiyi salla bari naje nakawo miki breakfast”.
Fita Mami tayi daga dakin itakuma tashiga shiryawa agurguje sanan tahau kan dadduma tai salollin dake kanta saida tai azkar sanan ta tashi ta cire hijabin tazauna akan gado, bude kofa Mami tayi tashigo dauke da tray na abinci sanan takaraso cikin dakin ajiye abincin tayi kan side drawer gadonsu sanan tadawo tazauna ahankali kan gadon kusada Du’a da kanta ke kasa har lokacin dan wani irin kunyan Mami taji tanaji, murya chan kasa tace “Mami ina kwana” shiru Mami tayi tana kallonta batare data amsa ba saikuma gently takai hannunta kan fuskarta ta tallabo habarta hakan yasa tadago idanunta ahankali takalli Mami, murya chan kasa Mami tace “Du’a” ahankali tace “Mami I’m sorry Kinji” murmushi Mami tayi tace “shiiii I want you to listen to me” gyadama Mami kai tayi, Mami tadan numfasa tace “all abubuwan dakikaga nida mahaifinki namiki badan mun tsaneki bane saidan we are all trying to protect you Du’a, Du’a nasan kinsan wanan abin dan nasan kinsha jin yan uwan Abban ku nafadi, dana haifoki babu kalan maganan da ba’a fadiba akanki, ance ke ba yar Abba bace, naje na nemi ubanki nahadaki dashi, ke mayya ce ke yar ruwace” shiru Mami tayi tana sauke ijiyan zuciya sanan tace “Du’a akwai many things which u don’t know kuma banmason kisani, I fought mahaifinki, we fought hard muka samu yan uwanshi da Maman shi suka barki kika zauna agidan nan left to them koranki sukaso ayi” Mami tasakeyin shiru sanan ahankali takai hannunta tadaura kan kumatun Du’a dake kallonta ahankali tace “Du’a you are special! tun ranan damuka haifeki mukasan hakan, you are special saisa kikaga muna boyeki, Du’a ke dabance! muna boyeki ne cus munyi tunani ta hakan zamu iya kareki and protect you, but u got it all wrong kin zaci mun tsaneki ne amman bamu tsaneki ba, kintuna abinda yafaru dake a JSS2 dayasa Abba yahanaki fita at all kinaso yakara faruwa dakene” girgixa ma Mami kai tayi dasauri hawaye nacika mata idanu. Ahankali Mami tasauke ijiyan zuciya tace “nakira Mama, Grandma dinki tariga tasan komi dama, yanzu da safen nan Hamad zai kaiki chan wurin ta a Abuja harsai komi nagidan nan ya daidaita, I think kema is best for u, your childhood has been terrible, kin taso cikin kyaran kowa is high time kije inda nasan u will receive d best care batare da an kyareki ko an ware ki ba, kinason kije wajen Mama na ko” ahankali ta gyadama Mami kai hawaye na zubomata, hannu Mami takai tashare mata hawayen tace “nasan namiki laifi, I’ve wronged you in so many ways just to please yan gidan nan but bazan karaba, nina daukeki na raineki for 9 months I can never hate you, abinda nakeso dake is take very good care of yourself, kizama yarinya mai wayau da basira, know when u are in danger and when u are not, kidage da addu’a, ki rike Allah danshi kadai ya isarmiki, I want you to be a good girl, karki sake kima grandma dinki ko any of your uncles rashin kunya kinji Du’a, I know u are in a good hands this is the first time dazaakije wani wuri da hankalina ya mugun natsu, now eat your food saiki fito ki gaida Abban ki kuyi sallama bari nakai jakan I waje” gyadama Mami kai tayi Mami ta tashi jakan taja tawuce tafita daga dakin, shiru Du’a tayi Allah ma yasan har cikin ranta tana farin ciki zatabar gidan nan sabida tasan yanda Maman Mami kesonta lokacin tana yarinya idan sukaje gidan kaman zata cinyeta, koba komi bazata kara ganin Muhsin ba, mugun mutum, koba komi idan baiganta ba zai hakura ya auri ya Nana, Hawwa zata huta da hararanta kullum Mum ma tahuta babu wanda zai kara kiranta yar aljanu, and at the same time yau saitaji wanan bakin cikin da kunci na haushin Mami dayakeji dukya fita daga zuciyanta sabida fir the first time Mami ta zaunar da ita tamata bayanin abinda bata taba mataba kenan. hannu tamika tadauki tray abincin ta abincin taci bama tawani ci sosai ba ta ture ta ijiye, shigowa dakin Mami tayi takalleta tace “tasoto muje kiyi sallama da mahaifinki” gyadama Mami kai tayi gabanta nafaduwa hijabinta tasaka sanan tabi bayan Mami suka fito, Abba na zaune akasa yana karanta jarida hangita yasa ya tsayar da karatun yana kallonta harta karaso, dan nesada shi ta tsugunna ahankali tace “ina kwana Abba” “ya jikinki akwai abinda ke miki ciwo”? Abba yamata tambayan bayabo ba fallasa wanda idan tasabo tasaba dan Abba naturally he’s not that kind of a friendly father dake wasa da yaranshi, gyadamai kai tayi ahankali tace “babu ko’ina Abba” gyadakai yayi cikeda gamsuwa yana kallonta, batare data dagokai ba tace “Abba kayakuri bazan kara abinda nayiba” ahankali yace “l know” dagokai tayi ta kalleshi, hannu yasa a aljihu yaciro bandir nayan 200 20k yace “zo” tashi tayi ahankali takarasa gabanshi karba tayi ahankali tace “nagode Abba” “Allah kiyaye hanya, jeki Hamad na jiranki a mota ta” hakanan batasan mesaba kawai taji kuka yazo mata dasauri tajuya tana daura hijabinta kan fuska Abba kuma yabita da kallo, fita tayi daga falon, Mami ta biyota abaya rikeda hadadden kula na abinci.
Hamad na tsaye gaban motan sienna Abba yaga fitowanta yana kuka, murmushi yayi yabude mata gaban motan tana karasowa tashiga ta zauna, karasowa itama Mami tayi tana murmushi tace “bazakama kanwarka magana tarage kuka ba tadauka yarinya ce ita” murmushi yama Mami baice komiba, Mami ta ijiye mata kulan akan cinyanta tace “ga abinci inkinji yunwa kici naga baki waniyi break da kyau ba and stop crying” gyadama Mami kai tayi, tashi tayi takalli Hamad tace “kutafi Allah kiyaye hanya” rufe kofan yayi sanan yazagaya yashiga yatada motan yaja Mami namusu bye bye suka fice daga Gate din. ajiyan zuciya Mami tasauke ahankali tace “Allah ya azurtaki da farin cikin rayuwa Du’a, I love you so much y’ata, zan dinga miki addu’a kinji Du’a”
???? KYAWUNA JARABTA TA ????
✍️M SHAKUR
Free page
EPISODE 1️⃣ 2️⃣
Sosai Hamad ke zuba gudu akan titi, har cikin ranshi he is happy for Du’a na barin gidansu datayi, bini bini yake kallonta yanda saibin hanya da komi take da kallo kana gani kasan bata saba fitowa ba, dan juyowa yayi yakalleta ganin yanda take kalle kalle yasa yay dan murmushi yace “iyye basaban ba yau anfito waje” juyoda kanta tayi takalleshi washemai baki tayi tana murmushin nan mai tafiyar da imanin mutum tace “Ya Hamad rabon dana fito waje wlh harna manta nafi shekaru” murmushi yamata yace “this is a chance da Allah yabaki, remember abinda nafada miki duk wanda yadogara ga Allah to Allah ya isar masa, cikin sauki tashi daya Allah yacireki daga kuncin gidan mu, so babu abinda yagagari Allah muddin ki kayi imani, just always thank Allah kinji and be a good girl” gyadamaikai tayi kaman mai tunani tace “Ya Hamad nifa nama manta kamannin Maman Mami fa Grandma, tun ina karama da Mami ta taba zuwa dani ban kara zuwa ba, saidai muyi magana awaya, su Aneela ne suka santa” dan murmushi yayi hankalinshi nakan hanya yace “grandma dinki is one of the nicest person I know in this world, tanada kirki gatada son mutane, duk naje Abuja sainaje na gaidata, you are so lucky to have her as grandmother” shiru Du’a tayi kaman tana tunanin maganan shi saikuma chan ta kalleshi tace “Ya Hamad maisa kai u are different agidan mu? baka biyema su Mum da Ya Nana, kafisu kirki duka” yana kallon hanya still yace “let’s say sabida ni namiji ne I see life differently daga yanda mata keganin life, and Abba yabani tarbiyan da nakan iya banbance right from wrong” murmushi tayi takalli kulan kan cinyarta tashiga budewa name ne soyayye da Irish da plantain. “bani nama naci” turo baki tayi tadauko nama daya takai tasamai akan hannunshi dayake bata, murmushi yayi ya wurga abaki yana taunawa yace “wow girkin Mami always taste different” nama daya itama ta dauka tamaida kulan tarufe sanan tahauci tanamai hira kadan kadan harta cinye sai bacci, kallonta yayi ganin yanda take bacci yasa yay murmushi gabgarawa gefen hanya yayi yay parking Sana yadan taso yasaukar mata da kujeran sanan yakoma mazaunin shi yatada motan yana bata wuta.