KYAWUNA JARAFTA TA 1-END

KYAWUNA JARAFTA TA Page 21 to 30

Hajiya tashigo dakin da asuba ganin wutan dakin A kunne, karasawa gaban gadon tayi, zama tayi atabaki bakin gadon tana kallon fuskanta, Du’a is just different! ahankali takai hannunta ta kwashe gashin daya sauka a gefen fuskanta, shafa gefen fuskanta tayi tana kiranta ahankali. “Du’a, Du’a atashi daga bacci asuba tayi” bude idanunta tayi ganin kakanta yasa taji kunya murmushi tayi dasauri Hajiya tace “na tabbata yau zata yalwatu da ni’ima a gareni, wanan kayataccen murmushi dakika gaisheni dashi Du’a, Masha Allah jikata is very beautiful, barakallahu fiki, tashi kiyi alwala kizo kiyi salla kifito kuyi sallama da Hamad yashirya zai tafi” gyadamata kai tayi Sanna tasauka daga gadon ahankali bathroom tashiga itakuma Hajiya tawuce tafita.

Saida tai salla sanan tafito sanye da hijabi, a falo tagansu suna zaune Hamad na rike da mug yanashan coffee, karasowa tayi ta tsugunna ahankali tace “ina kwana Grandma” “kintashi lpy Du’a ya kwanan Abuja” murmushi tayi tace “I love here Grandma, Ya Hamad good morning” “morning dama ke nake jira zantafi” yatashi bayan ya ijiye cup dinshi, Hajiya tace “sa takalmin ki kiraka yayanki” tashi tayi tasaka slippers din da Hajiya ke nuna mata sanan tabi bayan Hamad suka fita daga falon sauka suke daga matattakala kaman daga sama yace “ya akayi kika fada rijiya Du’a” dawani irin sauri takalleshi ta tsaya batare data cigaba da tafiya ba hakan yasa shima ya tsaya yana kallonta yace “answer me” murya chan kasa tace “Muhsin din Ya Nana ne yazo” dawani irin sauri cikeda mamaki yace “Muhsin”gyadamai kai tayi tabashi labarin komi iya wanda tasani, shiru yayi saikawai yay kwafa yace “muje” binshi tayi harwajen mota, sanan ya tsaya yace “be a good girl kinji, kinga yanda rayuwanki take kasancewa awajena maza so be careful kinji” gyadamai kai tayi shafa gefen fuskanta yayi yace “wuce ki koma ciki bye” waving hannu tamai tawuce shikuma yashiga mota yatada yabar gidan bayan security yabudemai gate.

Ahankali da sallama tabude falonsu tashiga, Hajiya na zaune kan kujera tanacin fruits dake cikin bowl akan cinyanta, ganin Du’a ta shigo yasa tanuna mata gefenta tace “zoki zauna anan Du’a” murmushi tayi takaraso wajen tazauna, bowl din tanuna mata tace “zaki sha fruits”? gizgiza mata kai tayi tace “na koshi” murmushi tamata tace “karki damu nariga namiki friends sunje kano ne but maybe tsakanin yau ko gobe zasu dawo zaki gansu yanmata kaman ke zadan su girma miki but I’m sure u will like them” murmushi tayi tace “thank you Grandma” murmushi tamata sanan tace “yanzu abinda ke mind dina is school, banso kishiga secondary school dan kinyi girma saidai lessons, koda wasa bazakiyi rayuwan kullen nan dakikayi agidan ubanki ba, don’t worry I will think of what to do akanki, yanzu dai zansa driver na yadauke ki Razika zata biki kije saloon ama gashin nan lafiyayyen gyara ko amiki kalba ko kitso duk wanda kikeso, sanan amiki gyaran farce right” gyadamai mata kai tayi tana murmushi, Murmushi itama Hajiya tayi tace “answer da naki stop nodding head be acting like a big girl okay” murmushi tayi sosai wanan karan tace “okay Grandma” “good girl, jeki shirya kiduba wardrobe dinki akwai kaya awajen kisa daga nan” harzata gyadamata kai saida sauri tace “Tom” wuce wa sama tayi Grandma tabita da kallo harta bace mata.

Wardrobe din dakin tabude hadaddun karyane wanda mostly abaya ne, dogayen riguna kala kala daban daban, ahankali tadaura hannunta kan wani baki fitodashi tayi daga leda tana kallon rigan kaman Grandma ta aunata shiryawa tayi cikin rigan saikuma dagudu tai wajen madubi tana kallon kanta yanda taga tayi kyau ko Nana su bata taba ganin tasaka doguwan riga mai tsada nan ba, murmushi tayi tadaura dan kwalin saman tadauki hijabinta akai tasaka tafito tasauko kasa Hajiya na ganinta tace “ina gyalen abayan Du’a” dasauri tace “nadaura akai Grandma” dan dariya Hajiya tayi saikuma ta mike tace “zokiga” karasowa gabanta tayi Hajiya ta yaye hijabin dan kwalin ta warware sanan ta gyaramata parking gashin, takalli Razika dake wajen tace “he daukomata handbag a dakinta Razika” da sauri tai sama, taimata rolling gyalen saitai kaman wata balarabiya, saukowa Razika tayi da jaka mai kyau, Hajiya ya karba tabata tace “perfect oya kutafi to driver na waje yana jiranku” takalli Razika tace “stay by her side, saikun dawo, bye Du’a” juyowa Du’a tayi tamata waving hannu alamun bye sanan suka wuce suka fita sai murna take basabamba, mota suka shiga direban yajasu.

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

            ✍️ M SHAKUR 

Free page

EPISODE 1️⃣4️⃣

Bini bini direban Hajiya dake sanye da uniform ke kallonta tamadubi, hakan yasa Razika takalleta, ganin yanda take kalle kallen hanya tana murmushin nan dake karamata wani kalan kyau nadaban yasa Razika tace “is this ur first time a Abuja Du’a?” juyowa tayi tazubama Razika mayun idanunta dakesa mutum yaji wani kwanciyan hankali harzata gyadamata kai ta tuna maganan Hajiya hakan yasa tace “eh” murmushi sosai Razika tayi tace “Abuja ai nada kyau, nima Hajiya tadaukoni daga kauyen mu takawo ni nan, sanan akwai lesson teacher dake zuwa mana karatu duk asabar da lahadi, Hajiya nason yara, kinga tunda nake a Abuja bantaba ganin yarinya mai kyau kaman keba” dan murmushi tayi saikuma tadauke kanta tamaidashi kan titi tana kallon motoci dan kunya takeji taji ance tanada kyau bamataso adinga cemata haka, ahankali tace “thank you” “yauwa munkawo” Razika tafadi ganin driver yay kwana yashiga wani babban Plaza, parking yayi hakan yasa Razika tace “sauka muje” bude kofa tayi ahankali tafito tana kallon wajen yanda akwai mutane kowa na shiga da fita abinshi, ko yanda takebin mutanen datake gani da kallo ne yasa taga suna kallonta itama oho dasauri tarike hannun Razika gam data fito tace “muje” tana rikeda hannun Razika suka wuce suka shiga wani hadadden saloon dake nan first floor, ma’aikatan suka taso suna gaidasu kafin Razika tamusu bayanin me za’amata nan aka shiga yi mata gyaran gashin.

“inje insiyomana ice cream a wanchan shagon Du’a” ta tambayi Du’a da ake wankema gashi, murya chan kasa tace “eh” tashi Razika tayi tafice daga saloon din daidai angama wanke ma Du’a tulin gashin aka nannade mata gashin da towel matar tace “tashi muje dryer” tashi tsaye tayi tawuce taje tazauna ana sliding kofan saloon din aka shigo, juyowa tayida sauri tazaci Razika ce, wani Alhaji tagani yaci babban riga milk na shadda dake kyalli da akalla zaikai 60yrs baki dashi mai kyau ga gemu kadan tareda wata mata kana ganinta kaga yar duniya ga hujin hanci akan hancinta guda uku tana rikeda jaka tana taunan cingum tana sanye dawasu kaya dabasu da maraba da babu ajikinta, suna shigowa masu aikin suka taresu. “welcome Alhaji, welcome Hajiya” gyadamusu kai yayi yanabin matan saloon din da kallo one by one, zama matar dake taredashi tayi kan kujera tawani kamo hannunshi ganin ba ita yake kalloba da sauri yajuyo yakalleta jinta kamamai hannu, kashemaai idanu tayi tace “Baby kagaya musu style din da za’a min” washe baki yayi yace “kai wlh mata kun iya rigima yanzu style ne sai an tambayani, ninasan kan style ne” kallon yar aikin dake gabansu yayi wacce ke jiran bayanin su kafin sufara aiki yadan lashe baki sanan yace “okay bari muga” juyawa yayi yacigaba da kallon yan shagon, Du’a yanuna da akema rolling gashinta a roller za’a sata a dryer yace “how about that fine baby style, Zinariya kinason style din”? yamata tambayan still yana kallon Du’a da akema gyaran gashi wacce ko kallonsu ma batayiba madubi take kallo tana kallon abinda ake mata akai wanda is new to her tabama kofa baya, ganin inda yake kallo yasa Zinariya tace “katafi meeting din dakake dashi Sweet, idan kagama saika biyo kadaukeni” tai maganan tana shafamai hannunshi still datake rikedashi, dan juyowa yayi yakalleta kaman wanda ya manta da abinda ke gabanshi yace “ohh meeting dinan, to,to bari inje, saina dawo” yay maganan yana juyawa bude kofan yayi harzai fita saikuma yadawo dasauri yawuce wajen kujeran Du’a ya tsaya tagaban wajen yana facing nata directly yakare madubin datake kallo yana murmushi yana kallonta kaman yanda takedan kallonshi atsorace yace “nace nawane kudin gyaran kan Zinariya”? Ya tambayi mai gyaran kan Du’a yana kallon Du’a kaman wani tsohon maye wanda baitaba ganin mace ba sai akan Du’a, Mai gyaran gashin Du’a dake kallonshi ne itama cikeda girmamawa tace “all payments are done to Christy Alhaji gatachan the cashier” tanunamai wacce ketare da Zinariyan shi data daure fuska tana kallonshi, yana kallon Du’a still yace “in that case ba matsala, by the way young lady ur hair is beautiful” yama Du’a magana yana wani kalan kallonta, sai alokacin Du’a tadago kanta ta kallai da kyau wanan sa”an Abban tabe hakan yasa tamai shiru, wani irin hadiye yawu yayi yana lashe baki murya chan kasa yace “bala’i Allah yayi mace anan” rasa yanda zaiyi yasa yawuce yawayance yana kallon Zinariya yace “natafi Baby” yawuce yafita ya shiga hadaddiyar jeep din da aka kawosu ciki daidai lokacin Razika na shigowa rikeda ice cream guda biyu tazo inda Du’a take tamika mata tace “gashi” hannu tasa takarba tana murmushi tace “thank u” gajeren tsaki Zinariya tasaki tadauke idanunta dagakan Du’a kishi nawani irin turnuketa kaman taje tashake yarinyar takeji tadai daure dantafi karfin karaman yarinya haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button