KYAWUNA JARAFTA TA Page 31 to 40

Allah da ikonsa ne kawai yakawoshi gida lafiya, ko parking din kirki bai iya yayi ba yafito daga motan dawani irin gudu security su yace “subhanallah” ganin motan na tafiya yashiga yay parking da kyau shikuma Asad yay wucewan shi batare dayama juyoba, ko katon Sharif dake zaune a garden dake kusada flat dinsu baiyiba yawani irin buga kofa yashiga ciki, binshi da kallo Sharif yayi saikuma ahankali yasauke ijiyan zuciya yacigaba da aikin dayake yi akan system, karan zubarda abu dayaji yasa yatashi da sauri ya ijiye system dinshi awajen, bude kofa yayi yashiga falonsu sanan yamaida kofan yarufe yay kitchen dinsu da sauri tsayawa yayi awajen kofa yana kallon yanda Asad ke zubarda komi na kitchen din yana rotsasu akasa kaman wanda yazare, cikeda damuwa Sharif yace “what’s wrong with u Asad”? Wani irin daga kafa Asad yayi yadaki fridge din kitchen din cikin zafin harshe yace “it’s none of your business leave me alone Sharif” shiru Sharif yayi yana kallonshi yanda yake haukanshi shi kadai wanda is not new to him, kowa yasan Asad da zafin zuciya haka Ammi ta haifoshi da halin nan.
???? KYAWUNA JARABTA TA ????
✍️ M SHAKUR
Freepage
EPISODE 1️⃣7️⃣
Yagama barinshi duk basu isheshi ba ganin yafara punching kofa da hannunshi yasa dasauri Sharif yashiga kitchen din wani irin kamashi Sharif yayi yasashi ajikinshi ya rungume tsam yace “calm down Asad ba Ammi tace idan ranka yabaci kadinga salati ba, calm down please” kokarin fizge kanshi yake yana ihu. “I said leave me alone Sharif, stay out of this” kankameshi sosai Sharif yayi with all the power he got yace “Ya isa Asad I am here for u, I am here, we gonna be brothers forever okay, ina kaje? what happen? Giran da kayi dazu ina kaje?” shiru yayi yakasa magana ahankali Sharif yace “you went to see Dad ko”?Murya chan kasa yace “I guess kaima kasan babu wani US din dayaje” shiru Sharif yayi sai chan yace “before muje kano lokacin kana UK I saw how worried Ammi is yasa naje office naduba shi, I saw him though shi baiganni ba baisan naganshi ba” shiru Asad yayi saikuma gently yatashi daga jikin Sharif zama yayi akasa ahankali yajingina da cabinet din kitchen din idanunshi sunyi jajir, zama shima Sharif yayi kusadashi yana kallon kasan wajen, ahankali Asad yace “I don’t know why Dad choose this life he’s 60 but jin kanshi yake kaman dan 20, that Oldman is lost Sharif completely, can u believe niyake gayawa I am just like him eh Sharif” yay dan shiru idanunshi sunyi ja yace “I can never be like that man, bazan taba neman matan banza ba, wlh bazan tababa cus I hate them kyama ma suke bani, I hate that I am his son, wlh da ana chanza uba da na chanza nawa, I hate that man Sharif” kallonshi Sharif yake bakaramin tausayi yabashi ba matsawa yayi kusada shi ya jingina da cabinet shima yace “bazaka taba zama kaman shiba that I am sure of Asad but we gonna do something right now” yay maganan ahankali yace “inaso ka share batun Dad for now dan is affecting u physically and mentally bayan kasan u need to be at ur best gobe zaka fara TV show dinka eh Asad, this whole mess will affect ur productivity as well as ur performance, I cannot be managing everything for u eh, u need to be at ur best mugama this TV program in the next 7days sabida kasamu muyi concentrating a office we need to release new collection eh Asad, banda ma haka kanason Ammi taganka ahaka ne kaga how I am better than u kenan, tunkafin mutafi kano nasan Dad na garin nan amman koda wasa ban nunama Ammi ba sabida I need her happy, kaiko look at u now bayan kasan mu Ammi ke gani taji dadi common be a man for Ammi, let’s keep pretending we don’t know what Dad has been up to koma yana gari” Ahankali yasaki dan murmushi saiya kalli Sharif din yace “kasami wanan illustrator din?” girgizamai kai yayi yace “no he’s on his summer break wai, kaima I don’t get u Asad why don’t u wanna give Nigerians dinmu a chance” “cus they can’t give me what I want” hararanshi Sharif yayi yace “shikenan haka zan zuba idanu inta kallonka wlh idan ka shiga tight corner kaida kanka zaka dinga neman su” tashi yayi ahankali yace “don’t worry I will get one” fita yayi daga kitchen din Sharif yabishi da kallo cikeda so dakuma tausayin dan uwan nashi yasan wani zubin Allah kan jarabci yara da iyayensu and that’s Asad da dukansu ma a family nan biggest test, Dad gashinan ne kawai living one kind of useless life kaman yaro, imagine Babba dashi he is willing yayi karya yabar gidanshi da sunan yatafi UK just dan yatafi wajen matan banzan shi, tsohon mahaifinshi baida lpy he don’t care yaje yaduba shi saidai yayta tura kudin magungunan shi, ayanzu kuma shi kadai ne dandan Dadda namiji, dan dama Dad ne Babba sai mahaifinsu daya rasu, sai Anty Turai mahaifiyar Aneesa, Mahaifinsu daya rasu ne kawai ya haifi yara dayawa a family Shine first born sai Rahima sai Mariya, itakuma Aneesa ita kadaice yar Mamanta Turai, da mijinta yasakota tadaukota suka dawo gidan Dadda dazama kafin tabama Ammi ita aka zo da ita Abuja tafara school gudun kar mijin ya kwace ta dan Anty Turai yar rigima ce fitinanniya saisa ma takasa zaman gidan miji.
Banda haka Ammi is just the best woman aduniyan nan, sosai take tarbiyan yaran batare data nuna gazawanta ko gajiyanta ba, hasalima bala’in son yaran take suma haka suke sonta dan wajen Ammi yafi musu ko’ina.
Mikewa Sharif yayi ahankali yanabin kitchen din da kallo, kwashe abubuwan dabasu wani baci sosai ba yayi sanan yawuce yafita, sama yayi ahankali yabude kofar dakin Asad din, akan gadonshi ya ganshi yana bacci, ajiyan zuciya yasauke sanan yaja kofan yarufe yasauko kasa, masu gyaran gidansu yakira yasasu gyara kitchen din sanan yakoma falon sama yazauna tunawa ma yayi da system dinshi awaje dasauri yatashi yawuce waje.
Dayake tanada yammata hakan yasa Ammi bata dauki yan aiki ba, su take sawa girki, duk tana kitchen taredasu suna aiki takalli Aneesa dake wanke rice tace “namuku kawa fa” dasauri duka yaran suka tsaya suna kallonta, Aneesa ce tace “Ammi a ina”? murmushi Ammi tayi tana maida marfin tukunyan data bude tana rufewa tace “jikan Hajiya ce, sunanta Du’a, she will be ur mate Aneesa keda Mariya” tanuna Mariya da itama ta tsayar da peeling Irish din datake tana kallon Ammi, tafi Aneesa tayi da Mariya tace “yi sauri Mari mugama girki muje gidan Hajiya” murmushi Ammi tayi takalli Rahima data cigaba da aikinta tace “Anty Rahima kinyi shiru” wani irin murmushi tayi tace “Ammi bakina Ya Asad maganan wayoyin muba” dasauri sauran sukace eh Ammi, hararansu tayi tace “wai mesa kuke tsoron yayan ku haka, aiko babu wanda zai kara aikena wajenshi cikinku kuje kusameshi dakanku kokuma kuma Sharif magana yasaimuku” dasauri Mariya ashagwabe tace “Ammi wlh Ya Sharif mugune yace wai babu wanda zaici kudinshi cikinmu wai tara kudin aure yake, duk wanan wahalan inda Dad na nan muna gayamai zai sai mana wlh” shiru Ammi tayi tace “kugama girki kuje ku sami Asad to baruwana kudena sani a lamarin ku” nariga nahada muku komi ku karasa kuyi setting dinning up tai maganan tana fita daga dakin.
Wuraren 5 suka gama girkin tass sukai setting dinning dakinsu sukayi kowa yay wanka, Aneesa data gama shiryawa cikin wata yar rigan zaman gida half gown mai spaghetti hand ya tsaya mata a knee ta kallesu tace “kumuje wajen Ya Asad” kwalalo ido daga Mari har Rahima sukayi atare sukace “kidawo lpy nidai bazani ba” hararan su tayi tace “wlh naje nawa kadai zan fadamai” tawuce fuuu tafice tana tafiya ahankali gabanta nafaduwa, tsayawa tayi takalli kanta a madubin dake bangon falonsu tayi kyau sosai ga kitson kanta yamata kyau abunku da faran yarinya dan gidan Asad ne kawai black cikin yaran, bude kofa tayi tai flat dinsu Asad, tsayawa tayi abakin kofan tai knocking, jin ba’a amsaba yasa ta danna door bell har sau biyu, sake knocking tayi cikin wata irin isasshiyar murya akace. “waye”? faduwa gabanta yayi muryanta har rawa yake tace “Ya Asad is me, Aneesa” shiru aka sakeyi takai kusan 3min atsaye awurin sanan akace “come in” dasauri tabude kofan ta shiga yana zaune a falo dagashi sai towel daya daura a waist dinshi ya zaunar akan kujera ya mikarda kafa yadaura kan enter table yadaura MacBook akan cinyanshi yana aiki ruwan coily gashinshi nabin fuskanshi.