Uncategorized

SAMEEHA J


*_????SÂMÊÊHÂ????_*

              (J)

 A cikin ƙasashen duniya daga ciki akwai chaina,dubai,da saran ƙasashe masu harkar cinikaya da 9ja,yana da ƙanne biyu mata da iyayensu suka rasu suka bari,shiya zama uwa da ubansu har suka sami mazajen aure a lokacin ya duƙufa da sana’arsa iya cikin Najeria,Hajiya fatima ita ke bin Alhaji bukar sai ƙanwarsu bilkisu wadda a yanzu take a abuja huse tana auran wani hamshaƙin ɗan kasuwa dake harkar atamfofi,duk wata babbar atamfa Alhaji kasim shiyake safararsu daga dubai zuwa Najeria,si dai Allah bai azurtashi da yaro ko ɗaya ba a tsakanin sa da hajiya bilkisu har yanzu,hajiya

fatima kuwa a nan kano kusa da Alhaji bukar take a wata unguwa da ake kira da gandun albasa,yaran ta huɗu,uku maza mace ɗaya,gidan kishiyoyi hajiya fatima ta faɗa amma duk da haka lafiya ƙalau take zaune da kowa,mace ce me haƙuri bata da faɗa ko kaɗan,idan kayi mata abu me daɗi da akasin haka murmushi ne kaɗai zai haɗaku,ya rabaku,hakan yasa ta baiwa ƴar uwarta hajiya bilkisu Hamida tun tana ƙarama,zumunci da ƙauna haɗe da shaƙuwa me ƙarfe yashiga tsakaninsu duk abinda hajiya bilkisu ta mallaka tofa hajiya fatima ma ta mallake shi,abin kowa na ɗan uwansa ne har yaran.

    A lokacin da Alhaji bukar yayi auran fari da matar sa Amina,suna mugun son junansu koya yayi magana ɗaya to ta biyun fatima da bilkisu zai furta hakan yasa Amina ta riƙesu kamar ƴan uwanta uwa ɗaya uba ɗaya zumunci me ƙarfi ya shiga tsakanin su su kashe su bunne Alhaji bukar bai ma san ana yiba har cewa yake Amina ta ƙwace masa ƴan uwa ta wareshi shi kaɗai dan sunga bashida ɗan uwa namiji ana haka Allah cikin ikon sa ya baiwa Amina ciki ta sha wahalar laulayi kafin yayi ƙwari yau idan fatima ta zauna a wajan ta,gobe bilkisu ce zata zauna haka suka dinga yi dan taimakawa matar yayannasu har cikin yayi ƙwari ta fara ayukan ta na yau da kulum kamar ko yaushe har cikin ya kai watan haihuwar sa.

         “””,karku so kuga yadda Alhaji bukar da ƴan uwansa suka kwallafa rai akan ƴa ko ɗan da Amina zata haifa kaya tun tana murna har sai data fara fishi akan wanda Alhaji bukar yake siyowa musamman da aka ce ɗa namiji zata haifa,Alhaji bukar ya dinga murna yana dariya shima ya kusa samun aboki kuma ɗan uwa,ɗa a wajansa, acewar sa duk saiya rama haɗe masa kan da akayi aka wareshi shi kaɗai,dariya Amina da ƙannansa suka saka,suka ce sunji sun ga ni shima layin su zai shigo idan Allah ya kawo shi duniyar,ba ayi kwana biyu da wannan muhawarar ba Amina ta tashi cikin dare da ciwon na ƙuda kafin a kai ga asibiti jini ya ɓale hankalin kowa ya tashi akayi sauri akayi asibiti da ita,da gudu likitan daya ke kula da ita ya amshe ta yace Alhaji bukar yasa hannu da sauri ayi mata aiki sakamakon jinin data zubda bazata iya haihuwa da kanta ba saboda jikinta duk ya saki,nan da nan Alhaji bukar ya rattaba hannu aka shiga da Amina ɗakin tiyata.





“”Allahu akhubar,duk me rai mamaci ne,Amina rai yayi halinsa Allah ya karɓi abarsa bayan likita yayi nasarar ciro ƙaton jaririn ta me kama da ita sak,ko ganin yaron batayi ba ta cika,kar kuso kuga yanda Alhaji bukar ya fita hayyacin sa lokaci ɗaya ya sauya banda sumbatu babu abinda yakeyi,bilkisu na ƙanƙame da gawar tana,”Ƴar uwata ki tashi kiga abinda Allah ya baki,kar kiyi mun haka Amina dan Allah ki tashi,ga jaririn naki,innalillahi wa inna ilaihirraju’un Amina ki farka karki mutu Amina dan Allah ki tashi kiga kyautar da Allah yabaki………fatima na kuka bilkisu nayi Alhaji bukar nayi,su kansu likitocin kwalla suke zubarwa abin akwai tausayi musamman da jaririn ya fara kuka yana ƙoƙarin saka hannunsa ɗaya abaki,Alhaji bukar ya amshe shi yana kuka ya ɗorashi kan Amina dake kwance kamar ka taɓata ta tashi,daga nan aka garzayo gida aka suturta Amina da ƴan uwanta aka miƙata gidan ta na gaskiya a ranar daga Alhaji bukar har ƴan uwansa basu rintsa ba,ko bacci ɓarowa bai saka su koda dai da gyangyaɗi ne ba banda kuka babu abinda suke yi barin ma da jaririn ya soma kuka.

“madara aka shiga bawa baby,ganin tana sa cikinsa na kumbura aka zauna shawarar yanda za’ayi,da fari dangin Amina sun so karɓar jaririn Alhaji bukar yace sam shi babu wanda zai rabashi da ɗansa ba zai bawa kowa ba,shi zai raini abinsa bilkisu ta ce ita abata shi ko me akesha nono yazo zatasha ta shayar da yaron fatima tace,Aa tunda ita bata jima da yayen Muhammad ba,abata shi zata shayar dashi insha Allah ba za’asamu wata matsala ba ko daga ɓangaran mijina ne,ita ko bilkisu duba da yanda bata taɓa haihuwa ba,ga kuma mijinta ba lallai ya amince da hakan ba haka kuwa akayi,fatima ta soma shan duk wani abu da zai dawo mata da ruwan nono,nan da nan abu yazo ta karɓi,Muhammad wanda ake kiransa da Sameer ta fara shayar da shi cikin ikon Allah yaro ya amshi nono bai wata biyu ba ya koma ƙato dashi nono ya amshe shi ga ƙarfi da yawaitar lafiya,ko ɗan zazzaɓin nan da yara kanyi shi babu abinda yayi har ya soma wayo Alhaji bukar na zuwa ganinsa duk sati wani zubin ma satin baya kaiwa har ya fara ƙetare Nageria yana barin ƙasar.




   ………..Kwanci tashi ga mai yawan rai har Amina ta cika shekara biyar da rasuwa lokacin Sameer ya girma masha Allah dashi musamman daya samu kulawa daga wajan ƙanwar mahaifinsa yayi kyau dashi kamar a hannun mahaifiyarsa,a tafiya tafiyan ne Allah ya haɗa Alhaji bukar da momy lokacin tana goyon wata yarinya da bata fi wata takwas ba ta sanadin wani dayake bashi labarin mijin tane ya yarasu ya barta da ciki gashi an rasa inda ƴan uwansa suke ga ita kanta nata ƴan uwan ba ƙarfi garesu ba duk sun guje ta kullum sai taje tayi wanki da wanke wanke a gidajen masu kuɗi take samun na lasawa idan ko ƴar ba lafiya sai abin ya baka tausayi,Alhaji bukar yaji tausayin ta sosai ya amince zai aureta ya taimaketa har yarinyar ta ta,shima yana da marayan yaro yana hannun ƴar uwarsa ba aɗauki dogon lokaci ba aka gama shirin haɗa komai aka ɗaura aure momy ta tare da ƴarta a gidan da Alhaji bukar ya gina sabo Aljannar duniya.


      Shigar momy gidan Alhaji bukar gaba ɗaya hankalin ta ya tashi ta ɗirsawa zuciyarta sai ta mallakeshi da dukiyarsa gaba ɗaya data lura yana ɗora sunan ɗansa akan komai nasa ta fara kishi da baƙin ciki nan da nan ta bazama neman haihuwa,haihuwa taƙi zuwa,ba ƙaramin kashe kuɗi momy tayi dan ta haihu da Alhaji bukar ba maganin hausa dana asibitin ba wanda bata shaba,data sha zakaga kamar bata shaba har ta yaye ƴarta Zainabu abu wadda ake kira da Zee Zee.


“”Kishi Momy tashiga yi dasu Hajiya fatima da bilkisu ba dama taji ɗan uwansu ya kira suna gaisawa ko anbawa Sameer yana ta gwalangwalansa dake sa Alhaji bukar ɗin dariya harda ƙyaƙyacewa ran momy ya cika ɓam ta kasa zaune ta kasa tsaye dolle sai da tashiga tsakanin Alhaji bukar da ƴan uwansa lokaci ɗaya yaje har gida ya ƙwato ɗansa da sharaɗin kar su kuskura su ƙara zuwa inda yake su saka aransu basuda wani ɗan uwa a duniya shi ya daɗe da ciresu a ransa har abada.


Wannnan magana ita take saka hajiya fatima kuka wiwi da rashin abin ƙaunarta Sameer bacci ne kaɗai ke rabasu ko baccin ma sai tajira yafarayi, yayi nisa tukuna take tashi taje ta kwanta ganin sameer take kamar mahaifiyarsa gashi mahaifinsa ya ƙwaceshi ya kuma saka takun kumin hana zuwa ganinsa har asibiti sai da hajiya fatima ta kwanta akan rabata da Sameer yaran ta suka dinga kuka zata mutu,daga baya ta fawalawa Allah komai,,hajiya bilkisu ba haƙuri ta daki ƙafa taje gidan yayan nasu,da kuka ta dawo da alƙawarin ita da gidan har abada saboda kafin ya sauko ma yazo ya sameta yafi awa guda a sama bai sakko ba,daya sako ɗin ma yaganta sheƙeƙe ya dubeta yayi mata korar kare daga ƙarshe matarsa ta zageta tas,ta hana Sameer zuwa gunta har tafita daga gidan tana jiyo ihu da kukansa yana kiran AUNTY NA,AUNTY NA NI ZAN BITA….

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button