Lu’u lu’u 1

D’aga mata hannu yayi a hankali cike da izza ya mik’e tsaye ya fuskanceta yace “Sarauniya Juman, kakan kakana ya kasance zab’abb’e ne ga abun bauta *Ghira*, shi d’in ya kasance d’an baiwar da ba’a tab’a samun kamar sa ba bayan shud’add’un wasu shekaru, mu malam gurin bauta mun yi amanna cewa k’arni bayan k’arni lokaci bayan lokaci abun bauta Ghira yana bijiro da wani zab’abb’e a cikin bayinsa, kakana ya fad’a min sanda kakansa ke gargarar mutuwa ya ambaci wata zab’abb’iya da zata zo mana bayan wani k’arnin, kin ga nan?”

Ya fad’a yana mik’a mata k’aton littafin nan sannan ya ci gaba da fad’in “Ya suffanta mana alamun bayyanarta, zata kasance ‘yar baiwa da kowane motsinta zai ba wa mai hankali mamaki, idonta masu matuk’ar ban tsoro da birgewa ne ga ma’abota kallonsu, sannan ki sani wannan ‘ya da zaki haifa zata zama mafari ga sabon canjin k’asar Texanda baki d’ayanta. Dan haka ‘yar ki ta samu sunanta tun kafin ki haife ta, *Zafeera*, ko kuma ki kirata da *LU’U LU’U*.”

D’auke idonta tayi daga kan littafin ta kalleshi a matuk’ar tsorace tace “Amma babban malamin, me ye manufar ganinta cikin kaya kamar na sarauta?”

Juya mata baya yayi dan baya son fad’a mata gaskiya sannan yace “Alamu ne na ita ce abun bauta Ghira ya zab’a a cikin zab’abb’un sa, sannan zata zama mai daraja a cikin al’umma.”

Numfashi ta sauke ta ci gaba da kallonshi tace “To kuma me yasa take mik’o min hannu tana fad’a min zata taimake ni?”

Da sauri ya juyo a hassale yace “Sarauniyata ya isa haka, kada ki tsananta tambaya a cikin lamarin ubangiji, ki je gida sannan ki yi shagali tare da farin ciki na zab’arku a cikin masu daraja.”

Lumshe ido tayi a sanyaye ta mik’e tare da aje masa littafin akan kujerar ta juya tana mai d’an rik’e k’asan rigarta saboda jan k’asa da take yi, a sanyaye har saida ta kai bakin k’ofar ta saki ‘yar rariyar dake rufe mata fuska a matsayinta na matar sarki, Habbee da dogaran suna ganinta suka sunkuya suna mata barka da fitowa, a sanyaye ta k’arasa bakin dawakai guda biyun da aka k’awatasu da abun zama aka musu rumfa, shiga tayi ta zauna sai Habbee data zauna daga baya akan wani siddi dake bayan dawakan sannan suka bar wurin.

*MASARAUTAR GIOBARH*

Da sauri ya ja ya tsaya a in da yake sakamakon ganin sarkin da yayi tare da iyalinshi, sunkuyar da kai yayi sosai tare da had’e hannaye alamar girmamawa yace “A gafarce ni ranka shi dad’e.”

A mugun dak’ile cikin yatsina fuska ba tare da ya kalli dogarin ba ya ci gaba da ciyar da uwar gidan ta shi wacce ke kwance bata motsi. Matashiyar matar da ke gefenshi a tsaye rik’e da faranti ce ta kalli dogarin cikin harshen galloi tace” Lafiya? ”

Sunkuyar da kai yayi alamar risinawa sannan yace” Ranki shi dad’e, dama boka *Kasur* ne ya zo kuma ya tabbatar mana lallai sarkina ya ke son gani yanzu.”

A sanyaye matar ta kalli sarki *Wudar* saidai ba tace komai ba, d’an satar kallonta yayi kafin ya sauke numfashi ya sake maida hankalinshi kan uwar gidan shi ya sake mik’a mata lomar abinci, cikin rawar kai kamar wacce lantarki ya kama ta bud’a bakinta ta karb’a har rabi na zubewa, tissue ya d’auka ya goge mata baki sannan ya mik’awa matar nan farantin abinci.

Mik’ewa yayi tsaye ya juya ya kalli dogarin yace “Yana ina?”

A ladabce yace “Yana masaukin bak’i shugaaba na.”

Numfashi ya kuma saukewa sannan ya juya ya kalli matar nan yace “Ki kula da ‘yar uwarki *Joyran*, ina dawowa.”

Da wani kallo mai wuyar fassara ta raka bayanshi tare da sakin murmushi, saida ta ga fitarsu 脿 d’akin ta kalli matar da ke kwance.

Babban farantin ta ajiye a kan wani dogon desk kafin ta zauna kan gadon gefen matar, fuskar alhini ta nuna sosai idonta tap da k’walla ta rik’o hannunta da ko motsashi ba tayi, cikin muryar jimami tana kallon k’wayar idonta tace “Sarauniyata, kuma ‘yar uwata *Kossam*, hak’ik’a ina matuk’ar jin rad’ad’in wannan ciwon naki, ina ma a ce ina da maganin cutarki? Tabbas da na sadaukar da duk abinda na mallaka dan samun lafiyarki,’ yar uwata ki ci gaba da hak’uri kin ji, wannan ciwon jarabawa ce a gareki, ki tuna wani abu d’aya yayata, da a ce yau wanda ya zama sanadiyar shigarki halin nan yana duniya, na tabbata da zai fi kowa shiga damuwa na halin da kike ciki.”

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da k’ara jimk’e hannunta tace” Kossam, hakan da nake ba dan bana k’aunarki bane, saboda ceton rayuwata nake haka, amma ina baki tabbacin komai ya kusa zuwa k’arshe.”

Muskutawa tayi kafin ta mik’e tsaye tana goge ‘yar k’wallar da suka tarar mata, kallon Kossam tayi tana fad’ad’a murmushi tare da fad’in” Yar uwata, ni zan koma b’angare na, sai na dawo baki abincin ranarki.”

Tana fad’a ta juya da saurinta ta bar d’akin inda doguwar rigarta ke jan k’asa sosai. Hadimar da ta gani 脿 k’ofar d’akin ya saka ta k’are mata kallo, cikin wurga mata harara tace” Kossam ta ci abinci yanzu, idan za ta ci anjima 脿 kirani na bata.”

Da girmamawa ta amsa mata da” Angma ranki shi dad’e.”

Cikin sauri ta k’arasa fita tayi b’angarenta, hadimar kuma da kallo ta bita sannan ta murgud’a baki ta bud’a d’akin ta shiga tana fad’in” Sarauta, kamar mu d’in musakai ne da ba zamu iya bata abincin ba dole sai ita.”

*Masaukin bak’i*

Bayan sarki Wudar ya zauna akan babban kujera ne ya tambayi bokan na shi me ke tafe da shi? Da sauri ya mik’e tsaye cike da zumud’in son sanar da shi abinda ke tafe da shi ya fara da fad’in” Shugaba na, labari nake tafe da shi wanda zai sa ka farin ciki, labari ne da nake da tabbacin zaka min kyautar da baka tab’a kwatanta yi ma wani ita ba.”

Cike da k’asaita da izza irin ta mulki sarki Wudar ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya yana k’arewa boka Kusar kallo, kamar mai ciwon baki ya d’aga labb’an shi yace” Ina jinka.”

Wangale baki yayi yana dariya yace” Sarki na, ka tuna zab’abb’iyar da mu ka maka bayani zata zo a zamanin mulkinka?”

A zabure sarki wudar ya sauke k’afa d’aya yana zaro ido yace” Taya kake tsammanin daidai da sakan d’aya zan iya mantawa da lamarin yarinyar da ku kuka bani tabbacin ita ce ci gabana ? Kai fa ka fad’a min inhar na sameta to ni zan dama mulkin da ya fi na *Alexandre* ma, kana ganin akwai wani mutum da baya son ci gaban rayuwarsa ne ? Ko kuma zan zauna na zama shashashan sarkin da ba zai so dawwama a mulki ba ?”

Sunkuyar da kai yayi yace” Ran sarkina ya dad’e, ba haka nake nufi ba, ina son maka tuni ne saboda abinda na zo da shi.”

Gyara zamanshi yayi yana hura hanci tare da fad’in” Je ga gundarin magana.”

Rusunawa yayi alamar girmamawa da kuma amsa buk’atar sarkin, d’aga kanshi yayi ya kalli fuskar sarki Wudar saidai bai had’a ido da shi ba saboda kwarjini, cikin nutsuwa ya fara fad’in” Sarkina, yarinyar da muka tabbata zata zo 脿 tarihi, kuma muka samu yak’ini ita ce silar duk wani ci gaba na ka da na ‘yan k’asar nan, yarinyar da kyawunta zai wadaci masarautarka da kewayenta, yarinyar da haskenta zai mamaye gaba d’aya k’asar Texanda, yarinyar da shek’inta tamkar na *Lu’u lu’u*, tana kusantoka, dan bincikenmu ya nuna mana da taimakawar abun bauta cewa ba shakka cikinta ya bayyana, za’a haifeta yayin da zamuyi murnar cika shekara ta dubu biyu, sannan mu fara lissafin lokacin da tarihin garinmu ya fara canzawa izuwa shekara ta dubu biyu da d’aya.”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button