Lu’u lu’u 1

Da sauri sarki Wudar ya tashi tsaye yace” A wacce k’asa za’a haifeta? Wacece mahaifiyar *’ yar baiwata*?”

Rarraba ido ya fara yi tare da fad’in” E to, sarkina saidai akwai wasu yan matsaloli da muka gano a game da hakan.”

A tsawace rai b’ace yace” Ban damu ba, ban damu da kowace irin matsala ba, abinda na sani kawai shi ne zan kashe duk wanda yayi k’ok’arin shiga tsakanina da cikar burina, dan haka ina jinka?”

Jiki a sanyaye yace” Shugabana, yarinyar za’a haifeta a masarautar sarki *Musail*, sarauniya *Zeyfi* ita ce mahaifiyar yar baiwarka.”

Wata arniyar dariya sarki Wudar ya bushe da ita tare da fad’in” Lallai boka Kusar baka da hankali, shin ka manta tsakani na da sarki Musail ne? Gaba ce marar iyaka, kuma a yanzu na samu damar da zan d’auki fansa a kan shi, duk da na sani hakan ba k’aramin jan aiki bane, amma akan cikar burina babu abinda zan yarda ya gagareni, zan auri ‘yarsa a gaban idonsa idan bai kawo min tangard’a ba, idan kuma yayi taurin kai to zanyi shirin yak’i da shi, zan kashe shi da hannuna sannan na mayar da matarshi baiwata ma’ana surukata,’ yarsa kuma zata zama matata a zahirance, a bad’ini kuma ita d’in *nasara* ce ga k’asata. ”

Tsawon lokaci sarki Wudar da boka Kusar suka d’auka suna tattauna kafin daga bisani su rabu zuciyar sarki Wudar na sake narkewa da mutuwar son zab’abb’iyarshi.

*31/12/2000*

*12:01* Yayin da milyoyin duniyoyi suke murnar tsallake shekarar fargaban za’a tashi duniya, a kowace k’asa an kacame da murnar shiga sabuwar shekara, a daidai lokacin Zafeera ta kutso duniyar ba tare da sanin wacece ita ba bare tasan manyan k’alubalen dake jiranta, a zahirance kam soyayya tsagwaronta ake nuna mata, saidai hatta mahaifiyarta da mahaifinta suna da na su nufin dake k’unshe 脿 cikin zuk’atansu 脿 game da ita, haka ma yayarta wacce aka haifa kafin ita mai sunan *Zafreen*, kama daga fadawan dake cikin gidan zuwa masarautun dake kewayensu babu wanda baisan da labarinta ba, saidai kad’an ne ke da kyakyawan k’udiri 脿 kan ta.

*Babban* tashin hankalin da aka fuskanta a lokacin bai wuce b’atan yarinyar da aka haifa ba awa d’aya data wuce ba, an nemi Zafeera an rasata k’asa ko sama, hankalin kowa a masarautar ya tashi musamman ma na sarki Musail wanda babu wanda yasan asalin sahihiyar nuna damuwarshi akan yarinyar sai jakadiyarshi da kuma malamin fada Dhurani.

A wannan rana a masarautar Khazira kowa baccin tsaye yayi, dan kuwa gida gida sarki yasa ana duba masa yarinyar shi tare da hadimansa guda biyu da aka nema a lokacin aka rasa, wannan yasa ya ta’allak’a b’atan yarsa da su, kuma yayi alk’awarin kashesu idan ya samesu.

*Alhamdulillah*

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button