Lu’u Lu’u 11

*11*

 

Fuskarshi ba yabo ba fallasa yace “Mahma, na zo muyi magana da ke, zan iya shigowa ciki?”

Had’e fara’arta tayi tace “Magana da ni kuma? A kan me?”

D’an d’aga idonshi yayi zuwa saman kanta dake ya fita tsayi ya hangi d’akin, a take kuma ya kalleta yace “Mahma, mai gidan baya ciki ne?”

Murmushi tayi tace “Shi ka ke nema?”

D’aga kai yayi alamar e tare da fad’in “E mahma.”

Kaucewa tayi a hanyar tace “Shigo ciki, ya d’an fita zai siyo mana gasasshen bredi ne, yana shigowa yanzu.”

K’afafunshi ya shiga zurawa cikin d’akin yana bin bayanta, amma idonshi akan gaba d’aya d’akin yake, komai kallo yake yana so ya ga ko zai ga hoto kafin ma ya ga zahirin, saidai babu komai daya shafi mutum, muryar Habbee ce ta katse shi daga wulk’itawar da yake ta ma idon shi tace “Me zan kawo maka?”

Murmushi yayi yacce “Coffee.”

Jinjina kai tayi ta juya ciki, da kallo ya bita kafin ya sake maida idonshi kan komai dake d’akin, yana cikin kallon aka sake danna k’ararrawar k’ofa, da azama ya mik’e da tunanin Utais ne, Habbee kuma har ta fito dan ta bud’e k’ofar, juyawa yayi ya kalleta yace “Karki damu zan bud’e.”

Murmushi tayi tace “Nagode.”

K’arasawa yayi bakin k’ofar ya kama hannun zai murd’a sai kuma ya lek’a ta yar hudar da aka yi don tsaro ne dama, mutumin daya gani ne yasa shi zaro ido, duk da kayan jikinshi ba na masarauta bane amma ya san shi farin sani, da sauri ya shiga waigawa neman inda zai b’oye, a k’arshe wani labule ya d’aga ya shiga saboda jin an banko k’ofar da k’arfin da yasa Habbee daga madafa fad’in “Waye wai?”

Umad na kallo ta labulen nan har suka shigo tsakiyar d’akin, tunaninshi bai wuce son sanin abinda ya kawosu ba, tsakiyar falon suka shiga suna ta waige waige alamar su ma wani abun suke nema, d’aya daga cikinsu ne ya kalli Habbee dake ta tsatsaresu da ido yace “Ina mijinki yake?”

Cikin fad’a fad’a tace “Me zaku masa? Su waye ku? Me kuke nema a nan?”

K’akk’arfan ne ya d’aga hannunshi sosai ya d’auke fuskarta da mari, a gigice ta dafe kunci tana fashewa da k’ara har ta fad’i k’asa, a tsorace ta kalleshi sanda ya d’ora yatsarshi akan labb’anshi yace “Shiiiiii!”

Hannu yasa ya d’aga rigarshi ya ciro bindiga ya d’ora mata a kai yace “Ina yake?”

Daidai shigowar Utais kenan rik’e da takardar dake nad’e da bredi, sakin kayan yayi suka zube ya ruga a guje yana kiran “Kai! Su waye ku? Me ta muk…”

Bai gama fad’a ba d’ayan ya zuba masa k’ulli a ciki, duk’uwa yayi yana dafe cikinshi kamar zai mutu, tarin lafiyayyar gashin kan shi ya kaa da k’arfi ya jawoshi k’iii saida suka kawoshi daf da inda Habbee take zaune suka jefar, dukansu suka nunawa bindiga wanda yafi kaushin a cikinsu yace “Ina take?”

Kallonsu sukayi a tare Utais ne yace “Wacece?”

Wani wawan naushi ya zuba mishi a baki yace “Karo na k’arshe kenan da zaka nemi raina mana hankali, dan haka daga yanzu zuwa sanda zamu bar nan kasan me zaka fad’a mana.”

Habbee fashewa tayi da kuka tace “Na rok’eku ku rabu da shi, ku daina dukansa hakanan.”

A tsawace d’ayansu yace “Shiru.”

Sake nuna Utais yayi da bakin bindiga yace “Tana ina?”

Lumshe ido Utais yayi ya had’e wasu yawu masu d’aci, bud’e idon yayi ya kallesu yace “Saidai ku kashe ni, amma na yi alk’awarin ba zan fad’a ba, ba zan tab’a cin amanar sarauniyata ba.”

Jinjina kai d’ayan yayi ya d’an ja baya kad’an ya d’ana bindigar ya saita akan Habbee yana fad’in “Idan kai a shirye ka ke ka mutu, ban sani ba ko ka shirya rasa matarka ma? Zan k’idaya uku ka ceci matarka.”

Da sauri ya kallesu a rud’e yace “A’a na rok’eku, kar ku tab’a ni ku min ko ma menene, kar ku cutar da ita.”

Cikin kuka Habbee tace “A’a ka barsu, na yarda su kashe ni indai akan alk’awarin da muka d’aukawa sarauniya ne.”

A tsawace yace mata “Shiru, kina da buk’atar kasancewa a raye, ko kin manta kina da mahaifiyar da rayuwarta ta dogara a ta ki ne? Ita kan ta gimbiya ta fi buk’atarki fiye da ni.”

A hassale mutumin ya daka musu tsawa ya saka yatsarshi zai danna kunamar bindigar a kan Habbee yana fad’in” Ku mana shir…”

Bai gama fad’a ba alburushi ya tashi kan shi sai fad’uwarshi kawai suka gani da kua sautin alburushin, k’ara Habbee tayi a take Utais ya jawota jikinshi suka duk’e, d’ayan kam da wani irin sauri ya kalli inda harbin ya fito, saidai tuni Umad ya kawo daf da shi, bai ankara ba kawai ya buga mi shi hannun bindigar a hanci ya b’arke da jini, a take kuma ya rik’e hannunshi mai bindigar ya karya wuyan hannun hakan yasa shi sakin k’ara, su Habbee na kallon ikon Allah sai gani sukayi ya kama wuyansa gaba d’aya ya murd’e ba tare daya barsu sun shaida wanda yayi ajalinsu ba ya turasu kiyama.

A matuk’ar tsorace suka shiga kallonshi sai Utais da yayi k’arfin halin tashi tsaye yana kallonsa, nunashi yayi da yatsa jikinshi har b’ari b’ari yake yace “Kai ne? Me ka ke yi anan?”

Gyara tsayuwarshi yayi tare da soka bindigarshi a mazauninta ya kalli Habbee yace “Mahma, ki gafarce ni kar ki fahimce ni ba daidai ba.”

A tare kuma ya kallesu yace “Kun ga, ya zamar muku dole ku fad’i sirrin da kuke b’oyewa tsawon shekara ashirin, ko ku fad’a ko kar ku fad’a kun sani da dole zata zama shugaba, dan haka ban ga anfanin b’oyewar ba har yanzu.”

Jiki a d’arare Habbee tace “Waye kai? Ya akayi kasan da maganar nan? Ko dai kai ma kana cikin masu nemanta?”

Fuskarshi a d’aure yace “Sanin waye ni ba shi ne a yanzu ba, ina so na san wacece gimbiya Zafeera?”

Girgiza kai Habbee tayi sai Utais da yace “Kai kuma a cikin wace tawagar masarautar ka ke?”

Wani kallo ya musu ya zura hannu ya fito da bindigar yana sake saisaita ta, wani shak’iyin murmushi yayi yace “Kar ku d’auka na taimake ku daga hannunsu ne, gani na yi basa buk’atarta tunda har zasu juri jin jayayya a kan ta, shiyasa na k’ara musu gudu.”

Tsakiyar goshin Utais ua d’ora bindigar dan yasan mace ta fi rauni sannan ya kalli Habbee fuska a tamke ba alamar wasa yace” Zaki fad’a ko sai kin ga gawar mijinki?”

D’aga hannaye tayi tana girgiza kai tace” A’a, a’a na rok’eka kar ka kashe shi zan fad’a, zan fad’a maka.”

” A’a Habbee, kar ki…”

Dungura masa bindigar yayi yace” Zan fasa kanka na sake jin bakinka.”

Jiki na rawa Habbee ta nufi inda Umad ya b’uya d’azun a bayan labule, bud’a labulen tayi ta wareshi gaba d’aya, Umad na kallonta ya ga ta tura wurin ka rantse bango ne, amma sai gani yayi wurin yayi baya alamar dai mashiga ce, juyowa tayi ta kalleshi tace “Zo ta nan.”

Kallon Utais yayi ya sake kallonta, nuna Utais yayi alamar ya fara wucewa, gaba Utais yayi sannan ya bishi baya ba tare daya d’auke bindigar ba, saida suka shiga dakin Habbee ta kunna hasken daya gauraye wurin.

Dauuuu! Hotonta da hasken d’akin suka daki idonshi a tare, zazzago idonshi yayi kamar zasu fad’o k’asa yana sake k’urawa sosai, gab d’aya jikinshi ya ji ya d’auki wata irin tafiyar tsutsa yayam yayam, sauke bindigar yayi daga kan Utais ba tare daya sani ba, baki da hanci da ido duk bud’e yana kallonta.

Ganin kamar baya hayyacinshi yasa Utais kallonshi yace “E ita ce, nasan abinda kake tunani kenan, ni ma ko da na ganka jiya na ji ban yarda da kai ba, sannan ina ji kamar na san fuskarka, sai dai na rasa inda na sanka.”

A hankali Umad ya taka ya k’arasa gaban tabkeken hoton da aka manna a bango na takarda, rigar sanyi ne jikinta kalar bleue mai haske da dogon wando, gashinta mai yawan gaske da yasha gyara kalar maroon ya kwanta a gadon bayanta, d’aya hannunta a mik’e har yana gugar cinyarta d’ayan kuma ta rik’e damtsenta da shi ta kalli hoton.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button