Lu’u Lu’u 12

Da wani sabon mamakin yace “Me? Gimbiyoyi kuma?”

Cike da d’ar d’ar yace “E shugabana, gimbiya Zafreen da gimbiya Zafeera sun b’ata a cikin tarzomar nan.”

Da bala’in k’arfi sarki Musail ya cire kambun dake kan shi na tsantsar gwal daya sa aka k’era masa dan alfahari ya jefar a k’asa, a fusace ya juya b’angaren da Dhurani yake ya kalleshi, sai kuma ya tattare rigarshi dake jan k’asa ya tunkari hanyar fita, rufa masa baya sukayi inda waziri Khatar ke fadin “Sarki na, ka nutsu mu bi komai a hankali, na tabbata sarki Wudar ne ya d’aukesu, dan shi ke da burin son d’aukar fansa a kanmu.”

Dakatawa yayi ya juya ya kalli Khatar da yayi maganar, jinjina kai yayi yace “In kuwa hakane sarki Wudar ya jaza ma k’asar sa yak’in duniya na uku, dan babu abinda zai hanani shiga masarautarsa sannan nayi fata-fata da su.”

Dhurani ne yace “A’a sarkina, ba da haka zamu fara ba, kafin mu farmake su buna buk’atar samun tabbaci suna hannunshi, daga bisani koma menene sai ya biyo baya.”

Adah ne yace “Hakane shugabana, dan na tabbata kamar yanda muke tsananin buk’atar gimbiya Zafeera, haka shi ma sarki Wudar, ba kuma zai kamata bane dan ya kasheta.”

Cikin hassala yace “To yanzu ya zamuyi? Me ye mafita? A yanzu na fi buk’atar Zafeera a kan Zafreen d’in.”

Adah ne yace “Wannan mai sauk’i ne shugaba na, zanyi magana da d’aya daga cikin masu lek’en asirinmu dake sintiri a cikin fadarsa.”

Nunashi yayi da yatsa yace “Ka tabbatar nan da zuwa yammacin yau ka samo min masaniyar komai.”

“Angama yallab’ai.” Ya fad’a yana rusuna masa, saida suka ga ficewarsa kafin su ma duk suka bar wurin babu wani mai farin ciki da yanayin da yake ciki, dan su kansu sun fi buk’atar a samu Zafeera a kuma k’ara mata gudu zuwa lahira, dan su canjin da aka ce zata kawo shi ne yafi tsaya musu a rai, a ganinsu zata rabasu da addinansu ne, muk’amarsu da martabarsu, hakan kuma ba zasu bari ya faru ba mundun ran su.

Bai zame ko ina ba sai kurkukun sabah, tsabar a rikice yake bafade d’aya ne ya take masa baya zuwa can, hannunshi rik’e da doguwar rigarshi cikin sauri har suka isa can, mai tsaron d’akin da take ne yayi saurin bud’ewa sarki Musail ya shige.

Tana zaune rakub’e a jikin bangon ta had’a kai da gwiwa, idonta a rufe suke ruf dan ko ta bud’e babu abinda take gani face dishi-dishi da jiri, har saida ya isa gabanta ya durk’usa irin tsugunnon maza ya finciki gashin ta sakamakon gyalenta daya sauka a kan kafad’unta, da k’arfi ya d’ago kan ta har saida ta saki yar k’ara saboda zafin da ta ji, da k’yar ta d’aga idonta ta kalleshi.

Cikin gadara da cika baki ya mata murmushi yace “To ya kike sarauniyata?”

Kamar wacce ke cikin maye tayi luuu da idonta ta saki wani murmushi ita ma tace “Yan…da kake, haka na ke.”

Tura kanta yayi da k’arfi har saida ta bugu ga bango ya fashe da dariya yace “K’arya kike sarauniyata, ni ina lafiya kuma ina cikin farin ciki.”

Cikin layi tace “Kai ma ba gaskiya ka fad’a ba sarkina, hankalinka a tashe yake kamar yanda muryarka ke b’arin tsoro saboda ka fara jiyo k’amshin mutuwarka.”

Da sauri ya mik’e tsaye yana lumshe idonshi dan gaskiya ta fad’a kam hankalinshi a tashe yake, cike da k’arfin hali ya kalleta yana nunata da yatsa yace” Ki zuba ido ki gani Juman, gobe warhaka ke da ‘yarki duk zaku mutu, wannan alk’awari na ne.”

Malalacin murmushi tayi ba tace komai ba har saida ya fita a wurin, a zahirinta kam bata nuna damuwa ko tsoron abinda ya fad’a ba, amma k’asan zuciyarta cike take da tsoro da alhini da zulumin abinda zai iya aikatawa.

*Larhjadin*

Ko da Umad ya isa ya samu Haman a masaukinshi fad’a masa abinda ya faru a makaranta yayi, saidai haka kawai ha k’i yarda ya fad’a masa batun auren nan, dan dama yayi ne saboda yasa hankalinsu Habbee ya kwanta su ji nutsuwar zuci su tabbatar tana hannu na gari, duk da dai yasan ba lallai sun yarda da shi ba musamman da suka san waye, amma dai yanzu a tunaninsu tana tare da shi kuma ba zai bari a cutar da ita ba kamar yanda ya fad’a musu, dan haka a sanin da yake da shi yasan aurenshi da Ayam zai cika k’aida ne idan da amincewar iyayenta mahaifa tunda suna raye, shaidu da kuma sadaki.

Cikin tashin hankali Haman yace “Me? Yanzu kana nufin ta sake b’ata kenan?”

Jinjina kai yayi ya kalleshi yace “Hakan alamu suke nunawa, amma a yanzu zamu iya cewa mun san inda take.”

Cike da k’aguwa yace “A ina kenan?”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace “Zan koma gida yanzun nan, ta hakane zan san inda take.”

Da mamaki Haman yace “Kana nufin zaka koma masarauta kenan?”

Jinjina masa kai yayi alamar e, cikin d’ar d’ar yace “Bana tunanin sarkinmu ya sameta, me zai hana ka fara saka ido akan Bukhatir?”

Da wani mamaki Umad ya kalleshi ya d’aga labb’enshi da k’yar yace “Bamu tab’a maganar Bukhatir da kai ba, ya akayi ka san shi?”

Zaro ido yayi alamar firgici, a take kuma ya had’e komai ya saki murmushi yace “Haba dai, ka manta ka min maganar sa? Daga gareka na ji batunsa ai.”

Cike da son waskewa ya d’an zagaya ya matsa daf da shi ya dafa kafad’arshi ganin kamar bai yarda da abinda ya fad’a ba yace “Ka gane ko, ina ga zai fi ka fara ta can d’in, zuwa gobe sai mu koma tare.”

Wani arnan kallo Umad ya masa sai kawai ya jinjina kai alamar to sannan yace “Shikenan.”

Sallama sukayi inda Umad na d’aukar hanya masaukin daya fara sauka ya k’arasa ya had’a kayanshi, dan yayi niyya yau ba sai gobe ba zai d’ora da neman Ayam, dan sai yake gani kamar Haman ya manta shi ne wajen rashin yarda da kafuwa, duk aminci da yardar dake tsakaninku ba zai saka shi d’auke ido a kan ka ba, bare al’amari na wacce yake da tabbacin za’a iya sadaukar da bilyoyin kud’i don samunta. Yana gama shiryawa saida ya fito ya d’auki hanyar zuwa filin jirgi sannan ya kira canal Jacob dan sanar da shi aikinshi ya k’are, dama hanya aka masa a gwamnatacce dan cika aikinshi, to tunda ya tabbatar da wacce yake nema ai shikenan.

*Bayan awa shida (Giobarh*: yana sauka a k’aton jirgin emirates d’in motoci guda hud’u ne suka zo dan d’aukarsa, sanda suka shiga rusuna masa d’aya daga ciki ya karb’i jakarsa mamaki ya shiga yi na samun tabbacin abinda yake zargi, dan ko mahaifinshi sarki bai fad’a ma zai zo ba, amma ga tarba ta musamman daga masarautarshi.

Limozine d’in da aka bud’e mishi ya shiga ya zauna suka mayar da k’ofar aka rufe suka d’auki hanya, gudu ake sosai dan tafiya ce mai nisan gaske daga filin jirgin zuwa fadar ta su, a d’an lokacin nan kuma tangale hab’arshi yayi yana kallon titi a zahiri a bad’ini kuma tunanin komai daya faru kuma yake faruwa yake, da wannan suka share awa d’aya a hanya kafin motocin su tsaya a k’ofar gidan suna oda.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button