Lu’u Lu’u 13

Sai kuma tayi shiru ta sake tsura musu ido, da d’an hanzari Bukhatir ya k’araso gareta yana fad’ad’a murmushi yace “Kwantar da hankalinki gimbiya.”
Wani kerere ta shig binshi da kallo tana had’e fuska da kula yatsina ta, k’ofar dake fuskantar ta aka bud’e, Zafreen ce ta shigo ita ma ta shirya sai dai babbanci na nesa ne tsakanin shigar Ayam da ta Zafreen d’in, sauk’akk’an riga ce doguwa kalar fara wacce ta saukar mata har k’asa, gashinta a sake yake da kuma bandeji a kan ta saidai alamu sun nuna ita ma an canza mata wani ne.
A wani gadarance Ayam ta d’auke kai daga kallon Zafreen ta kalli Bukhatir dake gefenta ta dafe k’ugu tace “Malam fad’a min me nake yi a nan? Waye kai kuma me yasa ka kawo ni nan? Sannan wannan kayan bana son su a sama min k’ananu.”
Shi dai da fara’a a fuskarshi ya nuna mata maza da matan dake gefensu duk sun mik’e tsaye yace “Muje ki gaisa da mutanenki tukuna.”
Lumshe ido tayi mai nuni da ka fara kaini bango kafin ta tunkaresu da tafiyar sauri, tana zuwa gabansu ta tsaya tana kare musu kallo, daga bayanta Bukhatir ya nuna mata wani dattijo yace “Gimbiya Zafeera, wannan shi ne sarkin gida, ma’ana duk masu aikin gidan nan a k’ark’ashin saka idonsa suke.”
Cikin girmamawa dattijon ya rusuna yana mata wani yare da ba larabci parsi da Bukhatir ke yi ba, amsawa tayi a mutumce a kuma ladabce kamar ba yau suka fara had’uwa ba.
D’an kawar da kan ta da zatayi ta kula duk mutanen har da Zafreen da Bukhatir sun zuba mata ido, nuna mata d’ayar yayi yace “Wannan kuma ita ce shugar mata, daga yanzu kuma zata zama mai kula da ke.”
Ita ma a wani harshen ta gaisheta, ba tare da tayi tunanin komai ba ta amsa mata a mutumce, har yanzu ma kallonta suka ci gaba da yi, Bukhatir kuma da musamman yasa aka samo masa mabanbanta yare dan ya tabbatar da abinda Laika ta fad’a masa na cewa canza yare kawai take sakin baki yayi yana kallonta, haka saida suka gaisa da kowa su kan su ma’aikatan a tsorace suka k’arasa gaisawa da ita, dan bakinta da yanayinta bai nuna koyen yaren tayi ba, kowane amsashi take da k’warewa a harshenta.
Kallonsu yayi yace “Zaku iya tafiya zan nemeku.”
Wani kallo ta watsa masa wanda yana had’a ido da ita yasa shi jin fad’uwar gaba, a wulak’ance tace “Da kasan suna jin yarenka me yasa baka basu izinin yi min ba?”
D’auke idonshi yayi daga cikin na ta ya shiga kame-kame yana fad’in “A… A… Am… Dama, ni ma ban sani ba.”
Sama da k’asa ga kalleshi ta yatsina fuska tace “Mak’aryaci.”
Da mamaki ya waro ido ya kalleta sai kula ya jinjina kai ya maida kallonshi ga Zafreen yace “Kin shirya ne? Dan. Dreba na jiranki zai mayar dake inda kike so.”
Da zumud’i Zafreen tace “E, amma ita fa?”
Had’e fuska yayi yace “Babu ruwanki da ita, ki je kawai.”
Gyara tsayuw tayi ta rumgume hannaye tace “Ba zai yiwu ba, na wa mahaifina alk’awarin zan koma tare da ita.”
Takawa yayi cike da izza ya tsaya gabanta yace “Zafeera ta zo kenan babu komawa, idan zaki je ki je, idan ba zaki je ba sai tare da ita, to ki sani zan sama miki d’aya daga cikin ma’aikata ki aura sai ki zauna a nan da lasisi.”
Cike da fad’a tace “Kai har ka isa ma, ba zan je ba kuma tare da ita zan bar nan.”
Girgiza kai yayi yace “Kar ki ce zaki kawo min wasa a nan, a halin da ake ciki yanzu na fara jin rayuwata ta fara d’aukar saiti daga zuwanta yau, na rantse miki da Allahn da nake bautawa ko ubanki ya zo nan ba zai rabani da ita ba.”
Gyara tsayuwa tayi tace “Lallai kana son tak’aloma kan ka yak’i da dakarun Khazira, ka sani sarkina ba zai barka ba, dan buk’atar da yake wa Zafeera ta take wacce kake mata ta shanye, dan haka ina mai baka shawara da ka gaggauta sakin yarinyar can mu tafi kafin mutuwarka ta riskeka.”
Da sauri ta k’arasa gabansu cike da masifa ita ma tace” Wai ku tsaya malamai, su waye ku? A kan wa kuke magana? Me kuka shirin aikata min ne da kuke jayayya haka kuma a kai na?”
Da lalama Bukhatir ya juyo gareta yana fad’in” Kin ga kwan…”
Da k’arfi Zafreen tace” Ba wani hankali da zata kwantar, kinga ke *k’anwata ce*, uwar mu d’aya kuma ubanmu d’aya, iyayenmu nemanki suke kamar zasu yi hauka.”
A hassale Bukhatir y kalleta yace” Amma ai ke neman kasheta kike, ni kuma kareta nake son yi daga sharrinku.”
Hannaye ta d’aga musu tace” Ya isa, ya ksa haka.”
Kallon Bukhatir tayi ido cikin ido ta tsareshi da su tace” Fad’a min, wacece ni? Ni d’in nan wacece?”
Janye idonshi yayi daga cikin na ta yana sunkuyar da kai yace” Zafeera, gaskiya ta fad’a, ke yar uwarta ce.”
D’aga mi shi hannu ta sake yi alamar yayi shiru, dafe kan ta tayi ta nuna kanta tana kallonshi tace” Ka ga da ni da wannan bamu da wata alak’a ta jini, makarantarmu ce kawai d’aya, ina ga fa kuskure kuka yi kuka d’auko ni a zuwan wacce kuke nema.”
A hankali Zafreen ta tako gabanta ta rik’o sark’ar dake wuyanta ta nuna mata tace” Kinga wannan sark’ar, a duk duniya zaki sameta ga wacce ta kasance mata ce a gurin sarkin Khazira, hakan kamar al’adace da aka gada iyaye da kakanni, wannan dake wuyanki mahaifiyarmu ce ta baki ita.”
Yanda take kallonsu galala yasa Zafreen fad’in” Ki yarda dani Zafeera, idan kin amince ki biyoni mu je tare, zaki gani da idonki kuma zaki ji daga bakin mahaifiyarmu.”
Girgiza kai tayi da taji yana mata wani nauyi yana kuma d’aukar zafi sannu sannu tace” Ku taimaka ku had’ani da iyaye na, na rok’eku.”
Cikin rarrashi Bukhatir yace” Shikenan na ji, yanzu ki kwantar da hankalinki kinji, zan kawo miki su kafin nan ki saki ranki, nan gidanki ne kiyi abinda kike so, kin ji?”
Jinjina kai tayi alamar to, Zafreen ta kalla kamar wata bak’uwar hallita a gurinta, wai yar uwarta? To ko dai bugun da aka musu a kai Zafreen ta samu matsalar k’walwa, ko kuma dai garin mahaukata aka kawota.
Da sauri ta kalli Bukhatir da ta ji waya na kururuwa a aljihunsa, yana ciro wayar ya duba mai kira ya kallesu ya musu nuni da yana zuwa, d’ora wayar yayi a kunne ya d’anyi nesa da su.
Kallon juna suka dinga yi har saida ya dawo kusansu ya kalli Zafreen yace “Tafiyarki ta fasu yau, sai zuwa gobe da safe.”
Da sauri tace “Saboda me? Ni bana so na kwana a nan, gidanmu zan je ni ma,tare da k’anwata.” Ta k’arashe tana kallon Ayam da ita ma ta kalleta da mamaki.
Ba alamar wasa yace mata “Saboda zamu karb’i manyan bak’i ne, daga yanzu zuwa lokacin da zasu iso an rufe shiga da fita.”
Da mamaki ta yatsina fuska tace “Su waye wannan?”
Saida ya nufi hanyar fita yace “Sarkin Giobarh.”
Da kallo suka bishi saida ya fita Ayam ta kalleta tace “K’anwarki?”
Dariyar baki da hankali ta mata ta juya ita ma ta bar d’akin duk da kuwa ta ji Zafreen na fad’in “E k’anwata ce ke, kuma nan gaba kad’an zaki san da haka, ki jira ki gani har nan mahaifina zai zo ya d’aukeki.”
Ganin ta fice bata kulata ba yasa ta jan tsaki ta bita da harara tace “Shegiyar banza, gidan uban wa ta iya yarukan nan?”
Sake wurga mata harara tayi ta k’ofar data fita tace “Sai na kasheki zan huta, indai har na kwana a nan to a nan zan kasheki saodai su d’auki gawarki.”
Buga k’afarta tayi alamar jin haushi ta juya ita ma zuwa inda ta fito tace “Banza.”
*04:30*
Tuni gidan ya kaure da hayaniya sakamakon dirowar bak’i daga masarautar Giobarh, sarki da kan shi tare da d’anshi mai jiran gado, mota takwas ta sauke inda fadawa da hadimai da ma’aikata suka shiga take musu gaba da baya da kuma gefe gefensu, inda suka had’e da mutanen Bukhatir wanda yayi iya k’ok’arin sa duk da bai karb’i sarautar ba, amma dake Ayam na hannunshi ya fara jiyo k’amshinta sai kawai ya tara jama’a shi ma aka musu maraba har zuwa babban falon.