Lu’u Lu’u 14

Shiru yayi kamar ba zai amsa ba sai kuma ya kalli fuskar Bukhatir kamar irin da shi yake magana yace “Kasancewata d’an sarki matsayi ne da Allah yake son gani na a haka, zamana malami kuma aiki na ne da nake so.”

Kallonshi tayi tare da dakatar da bubbuga cokalin cikin masifa tace “Ama kuma shi ne baka tab’a fad’a mana ba, kenan zuba ido ne kayi kana jira mu maka rashin kunya ka hukunta mu?”

Kallonta yayi saidai kafin yace wani abu tayi saurin fad’in “Ni ba wannan ba, wannan k’aton garjejen basamuden daya kawoni nan ya aje, bana son ganinshi kuma bana son zama a nan, ka yi wani abu a kai yallab’ai Umad, sato ni sukayi.”

D’an satar kallon Bukhatir yayi da a daidai lokacin ya tsura masa ido, ido cikin ido suka dinga kallon juna da shi kafin Umad yace mata” Ki zama cikin shiri, zan bar nan tare dake.”

Murmushi tayi ta fara tsakurar abincin, zata kai lomar farko suka had’a ido da Wudar banda murmushi da kallonta ba abinda yake, murmushin yak’e ta masa ta kai lomar bakinta tana taunawa, sautin wasu takalmin suka ji daga bayansu da kuma alamar mai tafiyar ranshi a b’ace yake, dan yanda k’arar ke fita da k’arfi da kuma sauri zai tabbatar maka da haka, Bukhatir da kujerarshi ke fuskantar k’ofar da kuma sauran mutanen Wudar kawai suka kalleta, cike da gatsali da raini ta tsaya tsakanin kujerar Bukhatir da sarki Wudar hannunta d’aya rik’e da rigarshi data sauka k’asa sosai, cikin d’aga murya tace “Wai ni ka fad’a min zaman me na ke a nan? Na je na fita banzayen masu gadin can sun hanani, me kake nufi da ni?”

Fadawan dake bayan sarki Wudar ne suka zaburo sukayi kanta d’ayan na fad’in “Murya k’asa yarinya a gaban sarki kike.”

Juyawa tayi ta wani kalkesu a wulak’ance kuma a gatsine, sake juyawa tayi ta k’arewa mutanen kan teburin kallo, sake juyawa tayi ta kalli fadawan tace “To ai ni nan ban ga wanda ya d’auki kalar kama da bawan gidan mu ba ma bare kuma sarki.”

A tsawace Bukhatir ya buga tebur d’in ya nuna mata k’ofa yace “Bar nan kafin na lalata miki fuska.”

Tsaki ta masa ta harareshi sama da k’asa kafin ta juya da k’arfi zata koma, saidai had’ewar da idonta sukayi dana Umad yasa ta tsaya cak da mamaki ta kalleshi, a hankali ta k’arasa gabanshi tana k’ak’aro murmushi a fuska tace” Yallab’ai, kai ne?”

Da sauri ta k’arasa ta ja kujerar kusa da shi ga zuba tagumi tana kallonshi bakinta har kunne tace” Amma ya akayi ka zo nan? Kai ma kasan wannan mutumin ne?”

Kallonta kawai ya tsaya yi da mamaki bai ce komai ba, murmushi ta kuma saki ta kalli Ayam tace” Yasan dalilin zuwan mu nan ne?”

Sai kuma ta kalleshi tace” Yallab’ai, kayi wani abu kai, mutanen nan sato mu sukayi bamu san su ba, ina tsoron kar su siyar da mu fa.”

Sarki Wudar da baya jin yarensu ne ya kalli Zafreen fuska a murtuke yace” Idan ma kina son d’ana ne to ya fi k’arfinki.”

Kallonshi Ayam tayi ta tab’e baki ta ture plate d’inta ta juya dan barin wurin, sarki Wudar ma ture plate d’inshi yayi yace” Cin abinci ya k’are.”

Kallonshi Umad yayi yace” Hakan na nufin zamu tafi kenan?”

Sauran ma duk mik’ewa sukayi sai Bukhatir da yace” Ina ganin hakane, na ji dad’in ziyararku.”

Sarki Wudar ne ya kalli Bukhatir yace” Mu yi magana ko?”

Jinjina kai yayi ya nuna masa wata hanyar yace” Muje ta nan.”

Su biyu suka nufi hanyar duk sauran na kallonsu, saida suka shige ciki su kuma suka nufi hanyar fita, Zafreen da haushi ya gama kamata ganin bai kulata yasa ta mik’ewa tsaye tace” Yallab’ai.”

Kallonta yayi a wulak’ance cikin jin haushin abinda ta fad’a gaba d’aya a kan su har da mahaifinshi, yanda ya zuba mata ido yasa ta fad’in” Wai me yasa kake shareni haka? Na rok’eka kayi wani abu da zan bar nan.”

Cikin abokan tafiyarsu ne ya nunawa Umad hanya yace” Yarima mu je.”

Zaro ido tayi ta kalli Umad da kyau tace” Yallab’ai, dama kai d’an sarki ne?”

Girgiza kan shi yayi ya rab’ata ya wuce suka fita, amma abun mamaki sai ta bishi a baya tana fad’in” Yallab’ai kar ka barmu a nan, ban yarda da mutumin nan ba, kar ya cutar da mu.” Bakin motocinsu suka tsaya Umad hannunshi rik’e da waya yana dannawa.

Yanda ta tsaya masa k’ik’am yasa ya d’ago kai ya kalketa, gyara tsayuwarshi yayi ya soka wayar aljihu, nuna mata hanyar da suka fito yayi yace “Muje muyi magana.”

“Tom.” Ta fad’a da fara’a a fuskarta, har zasu shiga falon da suka fito sai kuma ya kalleta yace “Ina ne suka ajiye ku?”

Turo baki tayi tace “Ni ga b’angaren da yasa aka aje ni can.” Ta nuna b’angaren dake fuskantar wannan d’in, sai kuma ta nuna b’angaren dake manne da wannan wanda yafi kowane girma tace “Amma ita anan suka ajeta.”

Gyara tsayuwarshi yayi ya shiga kallon ko ina na gidan, mai gadi a bakin k’ofa, wani dattijo dake bawa flowers ruwa saboda yamma tayi sosai, sai masu tsaron k’ofar b’angaren da Ayam d’in take su biyu, sai kuwa mutanen da suka zo tare da su, kallon Zafreen yayi yace “Ki je ki canza shigarki, zan d’aukeki a nan.”

Da sauri ta jinjina kai cikin farin ciki ta nufi hanyar b’angaren da take, tun kafin ta shige ya k’araso kusan abokan tafiyarsu ya mik’awa d’aya a cikin dreban hannu yace “Makullin mota.”

Mik’a masa yayi ya karb’a sannan ya kalli dreban yace “Shiga ciki.”

Kamar yanda ya ce haka yayi ya shiga bayan motar ya zauna, shi ma shiga yayi bayan ya zauna ya kalli dreban, fuska a had’z alamar bayar da umarni yace “Ban rigarka.”

Da mamaki ya kalleshi har saida yayi sub’utar baki yace “Rigata kuma yallab’ai?”

“E, ko ba zaka bayar ba?” Da sauri ya girgiza kai ya shiga b’alle rigar dake nuna aikinsa ya mik’a masa, karb’a yayi ya sakata a cikin rigarshi ya daidaita mata zama, fita yayi a motar sai kuma ya zura hannu ya ciro hular dreban dake kan shi.

Da sauri ya koma falon da suka fito, saida ya waiwaya inda ya ga mahaifinshi sun nufa, ganin babu kowa yasa shi yin sassarfa ya bud’e k’ofar da aka shigo da ita d’azu, ya d’auka ko wani d’aki ne amma sai ya ga corridor ne, babu kowa a k’ofar shiga dan haka ya shige ciki, ya d’auka yanda babu kowa a k’ofar haka ma a ciki, amma sai ya samu d’aya daga cikin matan nan zaune tana kallo, a zahiri kallon ba wai wani dad’i yake mata ba, dan da alamar gyangyad’i ma take, amma kuma aikin da aka sata na kula da Ayam yasa dole ta kasance a ankare.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button