Lu’u Lu’u 15

*15*

 

Murmushi ta sakar masa ta tafa hannayenta tace “Ni ce, ai guduwa na yi, na rok’eku ku tafi da ni, idan na bar nan daga can zan koma garina ni ma, kai tsaye ma gidanmu zan wuce dan mutanen can sun tsorata ni da haukansu.”

Da fara’a sarki Wudar ya amsa mata da “Haba ai ba sai kin rok’emu ba, mu da masarautarmu ai duk mallakinki ne.”

Nuna mata hanya yayi yace “Muje ko?”

Kallon wani bafaden shi yayi cikin rad’a yace “Ka tabbatar bata samu matsalar hawa jirgi ba.”

Jinjina kai yayi ya juya zuwa gurin masu ruwa da tsakin na kampanin, su kuma tuni suka shiga jirgin har da Ayam d’in wacce har zata zauna kusa da Umad sarki Wudar ya nuna mata kusanshi yace “Zauna nan.”

Cike da girmamawa ta zauna kamar yanda ya ce dan ita a uba take kallonshi tunda mahaifin malaminta ne, sun d’auki a k’alla minti sha biyar kafin jirginsu ya d’aga zuwa k’asar Giobarh.

Kamar wacce ke son fakar idon mutane tayi sata haka Ayam ke son fakar idon sarki ta ma Umad magana, bakinta cike yake da kalamai inda zuciyarta ke tumbatse da tambayoyi kala kala, shi kan shi Umad a k’alla zata jefa masa tambayar data bawa guda biyar baya, dan haka ta matsu, ta k’agu ko jirgin nan ya sauka su keb’e ta fara bayani.

Har ga Allah sai ta fara bashi dariya saboda yanda ta tsaresa da ido bakinta kam mm-mm-mm kawai yake, hnnayenta dake kan hannun kujerar sai bubbugasu take tana d’an jijjiga k’afafunta, daya kalleta yake d’auke kan shi dan ya sani ne da magana a bakin nan da take ta turo masa.

Adadin awoyin da suka d’auka gurin tafiya yanzu ma suka b’ata illa sab’anin sakanni kawai, Ayam ta ga ikon Allah ganin idonta sanda aka shiga yi musu tarba ta musamman ana murnar dawowarsu ka d’auka shekara sukayi basa nan.

Ita yanda ta ga ana t sunkuyawa Umad shi ya fi bata mamaki, suna shiga katafaren falon ta kuma bud’a idonta tana lumshe su a hankali, saida suka kai tsakiyarsa suka tsaya, a k’alla hadimai maza da mata sama da goma ne suka ding rusunawa suna gaishesu, babban abun mamakin yand sarki Wudar ke ta nunata yana fad’in Zafeera ce, kai ita wannan suna ma k’ona mata rai yake, wani wai Zafeera a ganinta fa.

Wani dattijuwa ya nuna mata yace “Wannan ce zata zama mai kula dake daga yanzu, duk abinda kike da buk’ata kai tsaye ki fad’a mata zata sanar min.”

Da mamaki Ayam ta d’aga labb’a tace “Amma kum…”

Nuna mata wata kyakyawar matashiya yayi wacce shigarta ta banbanta data sauran da alama itama babba ce a gidan yace “Wannan Joyran kenan, k’anwar matata ce, sakamakon rashin lafiyar dake damun uwar d’akina wacce muka rasa gabanta yasa yanzun alhakin kula da cikin gidan nan yake wuyanta.”

Kallon fuskarta Ayam ta sake yi, a kallon nan d’aya tak ta ji sam matar bata kwanta mata a rai ba, uwa uba kwalliyar dake fuskarta ta wayayyi, kayanta kua duk da na sarauta ne manya amma rigar ta fito da maman ta sosai.

Joyran ma haka ta k’ura mata ido cike da zababbiyar tsana da kishi had’e da takaici da jin kamar ta shak’o wuyanta, tsabar ta rasa jurar halin da take ciki yasa ta gagara b’oyewa har saida tabi Ayam da mugun kallo sannan ta d’auke kan ta ta mayar kan sarki Wudar, wani fitinannen kallo ta masa ta shiga masa signa da ido alamar tana son magana da shi ya kuma biyota.

Da kai ya fara amsa mata ta hanyar gyad’ashi kad’an yanda babu wanda ya gane, sai kuma ya lumshe ido alamar tabbatarwa, tana samun amsarta ta juya a fusace ta bar falon zuwa b’angaren daya zama na ta yanzun.

Sarki Wudar ne ya kalli dattijuwar nan yace “Ki rakata d’akin kusa da na sarauniyata, ki mata duk abinda ta buk’ata.”

Sunkuyawa tayi tace “To shugabana.”

Matsawa tayi kusa da Ayam ta nuna lata hanyar da zasu bi tace “Muje ranki shi dad’e.”

Satar kallon Umad tayi da gaba d’aya yayi kamar baya wurin yake ta danna wayarshi, kallon sarki tayi a shagwab’e ta nuna Umad da yatsa tace “Yallab’ai, ka had’a ni da wannan mana ya rakani, na ga ya na jin yaren da na iya.”

Dakatawa yayi daga danna wayar amma bai kalleta ba, sarki Wudar kam jiki na b’ari na ta fad’i buk’atar ta ya nuna Umad yace “Yarima na, ka je sai ka rakata ka ji ko, idan da wani abu da take buk’ata sai ka fad’awa jakadiyarta.”

Kallon fuskar mahaifinshi yayi irin kallon me kake nufi kuma? Ni ma fa masu hidima ne da ni, ha kuma zan zauna yi ma wata rakiya.

Maida kallonshi yayi gareta, har yanzu dai abu d’aya yake gani tareda ita wato zance, sake kallon sarkin yayi ya jinjina kai alamar to, a wani gadarance cikin takon sanyi ya shiga takawa kamar wanda k’wai ya fashewa a ciki, haka suka shiga taka matakalar har suka haye sama yana gaba tana baya, d’aki na farko suka wuce haka ma na biyu inda mahaifiyarshi take, na uku ya bud’e ya kauce a hanya alamar ta shige.

Hannu biyu ta sa ta tura k’ugunshi zuwa cikin d’akin, kamar zai fad’i haka yayi yana kallonta da mamaki, shiga tayi ta ja k’ofar ta rufe da sauri ta k’arasa gabanshi, takalmin k’afarta ta cire da hannunta masu tsini sannan ta dafe k’ugu suna ci gaba da kallon juna tace “Uhum! Tel me, me yake faruwa?”

Wani shashantar da zancen yayi ya mayar da wayarshi aljihu, juyawa yayi ya k’arasa gaban gadon dake lafiye da shinfid’a ya zauna, kallonta yayi yace “Ban gane ba?”

Da sauri ta matsa gabanshi ta zauna k’asa ta tank’washe k’afafu ta rik’e k’afarshi d’aya tana ta mitsikawa tace “Ka ga na fa gane ka, tambayoyi na a kan ka masu yawa ne, yanzu ka fara amsa min wannan?”

Jinjina kai yayi yana siririn murmushi yace “Zana duka tambayoyin, zan amsa miki su d’aya bayan d’aya.”

Sakin k’afarshi tayi ta dinga nuni da yatsunta tana lissafi tace “Na d’aya… Ba kayi mamakin ganina a gidan nan ba, shiyasa ban ji ka tambaye ni me kike yi a nan ba ko me ya kawoki nan? Na biyu kai ma me ya kai ku can a wannan lokacin? Shi mutumin nan waye shi? Me yake nema a gareni daya saceni? Sannan me yasa ka ce kar na nuna musu na san ka.”

Gyara zamanshi yayi ya sauke numfashi yana kallon fuskarta yace” Me yasa kika tambaye ni duka wannan? Me yasa shi baki tambaye sa ?”

Yatsina fuska tayi tace” To ai na tambaye shi amma shi da yarinyar nan suka dinga fad’a min wasu maganganu na daban.”

Kafeta yayi da ido yace” Me suka fad’a miki?”

Cikin turo baki tace” Wai ni yar uwarta wannan ita mai shegen girman kan ce, wai k’anwarta.”

Mik’ewa yayi tsaye ya d’an shiga takawa d’aya biyu sannan ya juyo ya kalleta ita ma ta juya ta kalleshi yace” Gaskiya suka fad’a miki, yayarki ce.”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button