Lu’u Lu’u 15

Zunbur ta mik’e tsaye tace” Me? Kamar ya? Ka kuwa san me kake fad’a?”

Girgiza kai tayi tace” Ta ya ya?”

Kallonta yayi cike da tausayin yanayin da zata samu kan ta yace “Ki samu kiyi wanka ki ci wani abu sai ki huta, zuwa dare zamuyi magana.”

Matsawa tayi kusanshi ta girgiza kai tace “Ba zan iya ba yallab’ai, ka daure ka fad’a min ko na samu sassauci, ina so na san dalilin da yasa aka kawoni nan, kuma ina so na ga iyayena.”

Tsare fuskarta yayi da ido yace “Ayam.”

Zuba masa ido tayi ita ma tace “Na’am.”

A sanyaye yace “Kiyi abinda na ce, bana so idon mutane ya dawo kan mu yanzu.”

Dantse leb’enta tayi da hak’ora dan yanda ya mata magana yanzun ba zata iya musawa ba, sunkuyar da kai tayi dan gabanta fad’uwa yake, tunaninta bai wuce son sanin wane irin garari ne ke neman tunkaro rayuwarta haka? Me ye b’oye a cikin rayuwarta haka da ake neman bankad’o mata shi yanzu? Ko kuma dai sab’ani aka samu wata ake nema ba ita ba? Rashin sanin ko d’aya daga cikin amsoshin nan yasa ta jin k’walla taf a cikin idonta.

Lumshe ido Umad yayi ya sake bud’ewa a kan ta, dan ba komai ya zo masa ba sai tunanin ta yanda zai fara fad’a mata wacece ita, da kuma alak’arsu ta yanzun, a hankali ya tako gabanta ya saka yatsa d’aya ya tallabo hab’arta, suna had’a ido hawayen suka gangaro kan kumatunta har saida suka sauka kan yatsarshi.

Cike da rashin jin dad’i yace “Ohh! Haba dai zakanya, kuka kuma? Kiyi hak’uri kinji, na miki alk’awarin fad’a miki komai anjima, yanzu babu lokaci ne, ki daina kukan nan bana so.”

Kamar k’ara zugata ne yake sai kawai ta fashe da kukan da ita kan ta a rayuwarta bata tab’a irinsa ba idan ka cire na farin ciki da tayi sanda gwamnatin Khazira ta d’auki nauyin karatunta a sanda iyayenta suka nemi gazawa, ba tare da sanin me tayi ba, cike da son samun wanda zai rarrasheta, cike da kwad’ayin a lallab’ata ta fad’a k’irjinshi tana ci gaba da kukan.

Gam gam ya rintse idonshi sakamakon irin jijjigar da jikinshi ya d’auka, ya san ba da wata manufa ko niyya tayi ba face hakan su ba komai bane, saidai shi yanzu yana da ak’ida, yana da madogara da kuma k’akk’arfar shari’ar dake saitashi ga daidai da barin daidai, sa’a d’aya ita ce akwai igiyarshi a kan ta, amma dake abun sabo ne gareshi sai ya gagara komai, jinta yake har cikin b’argon jikinshi da jininshi, jin ta yake can k’asan k’asan zuciyarshi kamar tare aka haifesu, sai yake tuhumar ko dai jikinta ne ke da wannan tasirin.

Jin bata samu abinda take nema ba sai kawai ta jaye jikinta daga na shi cike da kunya kanta sadde ta juya mas baya, bakin gadon ta zauna tana share fuskarta ta k’i d’aga kai bare ta kalleshi.

Shi kan shi sai yaji wata kunya ta kama shi daya kasa d’an daddab’a bayanta ko ya ya dan ta ji sanyi, a kunyace ya juya shi ma ya fice a d’akin.

Tana ganin ya fita ta fad’a kan gadon ta sake rushewa da wani kukan tana sake fad’in “Wai me yake shirin faruwa ne da ni?”

Umad na fita kai tsaye b’angaren Joyran ya nufa inda ya ga mahaifinsa yayi, bai samu kowa a b’angaren ba haka ma a falon, tsaye yayi a tsakiyar falon yana dubawa, a ranshi ya tambayi kan shi “Ina kuma suka nufa?”

Hannu d’aya yasa ya shafi sumarshi ya d’aga kafad’a alamar ohon nan sannan ya juya zai fita, ya fara takawa kenan ya ji sautin Joyran ta kwamtsa k’ara da “Ahhhhh.”

Dakatawa yayi ya juya ya kalli k’ofar da ya ji sautin, da d’an sauri ya fara takawa dan ya ga ko lafiya, sai kuma ganin mahaifinshi yayi ya fito daga d’akin Joyran a bayanshi ta rik’e babbar rigarshi tana share hawaye.

Wani irin mummunan bak’on yanayi ne ya ziyarceshi sanadiyar abinda zuciyarsa ta hasko masa lokaci d’aya, gagara komai yayi sai zuba musu ido suna ta kame-kame, daga bisani kuma sai mahaifinshi ya juya gareta a hassale ya fincike rigarshi ya nunata da yatsa yace “Na gama magana Joy, ko kina so ko ba kya so yanda na fad’a haka za’a yi, dan ba zan yarda ki zubar min mutumci ba, kowa laifina zai gani a ce da saka hannu na a faruwar komai.”

Juyowa yayi dan fita har ya zo daf da Umad zai rab’ashi ya wuce, da kallo Umad ya bishi yace” Sarki na, meyake faruwa ne?”

Wani huci ya dinga saukewa yana hararen Joyran data k’araso garesu, cikin shashek’ar kuka tace” Umad, mahai…”

Da sauri ya katseta da fad’in” Ciki ne da ita, ni kuma ba zan yarda wannan labarin ya fito ba.”

Da matsanancin mamaki ya kalli sarki yace” Ciki?”

Kallon Joyran yayi data shiga k’yabta ido, a razane yace” Ta ya ya? Goggo wa ye ya miki ciki kuma ba…”

Da sauri sarki Wudar yace” Waziri ne, dama soyayya suke amma rashin lafiyar mahaifiyarka ta sa ta k’i aminta da maganar auren.”

Wani iska Umad ya huro daga bakinshi ya dafe goshi, shiru kamar ba zai ce komai ba, ya d’an jima haka suma kuma jiran abinda zai fad’a suke, can ya d’ago ya kalleta yace” Amma gwoggo m yasa zaki yarda da haka kamar wata k’aramar yarinya, yanzu gashi ya kike so muyi?”

Sarki Wudar ne yace” Abinda nake fad’a mata kenan, na ce a zubar ta dage ita ba za’a zubar ba.”

Zaro ido yayi ya kalli mahaifinshi yace” Sarkina zubarwa kuma? Gaskiya ni ma ban goyi da bayan haka ba, kar a zubar mahaifina.”

A d’an hassale yace” To yanzu ya kuke so a yi? Ba fa zan yarda a haifa min shegen nan ba.”

Da wani kallo Joyran ta d’aga kai ta kalleshi, da k’yar ta had’iye abinda ya tokare mata ta sunkuyar da kai, a nutse Umad ya kalli mahaifin na sa yace” Abba na ka je kawai, zamuyi magana da ita, kar ka damu da abinda mutane zasu fad’a, zan ji da komai.”

Kallon Joyran sarki yayi irin kallon garhad’i kafin ya juya a hassale ya fita, ajiyar zuciya Umad ya sauke ya kalli agogon hannunshi, kallonta yayi da sauri yace” Goggo zan je amma zan dawo, ki kwantar da hankalinki kinji.”

Jinjina kai tayi alamar to, da sauri ya juya ya fita dan sallolin dake kan shi yae san saukewa wanda suka riskeshi a hanya.

*12:36* daga d’akin mahaifiyarshi cikin sand’a ya shigo nan ba tare da ya bari kowa ya gan shi ba, a hankali ya bud’a k’ofar ya shiga ya mayar ya rufe, yana juyawa das ya sameta zaune tsakiyar gadon, fad’uwa gabanshi yayi dan yanda ta zubawa k’ofar ido da kuma yanda take zaune ya nuna fa tun da ya fita ya barta haka take, a hankali ya k’araso yana kallon fuskarta da idonta da sukayi jajir suka d’an kumbura, jiki a mace ya zaune gefenta yana ci gaba da kallonta ita ma kuma haka.

Cikin tattausan murya yace “Me yasa da aka kawo miki abinci kika kori mai aikin?”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button