Lu’u Lu’u 16

Da azama ya sunkuya yana girgiza ta da kiran sunanta, d’ora yatsanshi yayi daidai hudar hancinta ya saurari sautin fitar numfashinta, tabbatarwa da yayi tana numfashi yasa shi saurin d’aukarta cak ya shinfid’e kan gadon, zaune yayi daf da ita yana kallon fuskarta cike da tausayinta, hannunta ya kama ya dinga shafa tafin hannunta yana murzawa da sauri sauri, a hankali kam sai ta fara d’an motsa idonta amma kuma bata bud’esu ba.
Sunkuyar da kan shi yayi kamar zai sumbaceta ya kira sunanta “Ayam.”
Jujjuya kan ta ta fara yi tana yatsina fuska tace “Na’am, Mahh… Mah.”
Sakin tafin hannunta yayi ya shiga murza tafin k’afarta, sannu sannu ta fara bud’e ido har ta bud’esu tas a kan rufin d’akin, da sauri kuma sai ta kalleshi suna had’a ido ta yunk’ura zata tashi, luuuuuu da ta ji tayi d’akin ya juya mata yasa ta komawa ta kwanta, kamar zata fashe da kuka tace “Yallab’ai kira min iyaye na, ina so ‘a gansu yanzu, na rok’eka ka taimaka.”
Mik’ewa yayi tsaye yana had’e fuska yace “Ki kwanta ki huta yanzu, zan sa a kawo miki abinci ki ci, da safe zamuyi koma menene.”
Fashewa tayi da kuka marar sauti ta dafe goshinta tace “Me yasa ba zaka fahimce ni ba yallab’ai, abinda kuka zo mi da shi safiya zuwa daren nan ya girmi tunani na, ko a tatsuniya ban tab’a kawo hakan zai faru ba, ta ya lokaci d’aya zaku nuna min wad’anda suka reneni ba su ne iyayen da suka haifeni ba? Ta ya kuke so na yarda da ku haka?”
Sauke numfashi yayi yace” Na fad’a miki iya abinda zan iya yanzu, zuwa safe zamu ci gaba da tattaunawa.”
Yana fad’a ya fice a d’akin inda ta bishi da kallo, kasa kukan tayi mai sauti sai marar sauti hannunta kuma dafe da kan ta saboda yanda yake juya mata.
Ba’a d’auki lokaci mai tsayi ba wata matashiyar jakadiya ta shigo d’auke da faranti a hannunta shak’e da kayan abinci, ajewa tayi cikin ladabi tace “Ranki shi dad’e ga abinci inji yarima na, da wani abu da kike da buk’ata?”
Mik’a mata hannu tayi tace “Kamani na tashi.”
Da sauri ta kamata tayi zaune, a raunane tace “Bani ruwa.”
Sunkuyawa tayi a ladabce tace “Amma ranki shi dad’e yallab’ai Umad ya ce ki fara da ruwan d’umin nan, hakan zai ba wa hanjinki damar warwarewa.”
Jinjina kai kawai tayi almar to, tana kallo ta had’a mata tea da zuma kad’an a ciki ta mik’o mata ta karb’a, a hankali ta dinga kurb’awa tana sha, saida ta shanye tas ta mik’a mata kofin ta ajiye.
Bangon d’akin ta kalla inda agogo ya nuna mata k’arfe 01:15, sake mik’a mata hannu tayi tace “Taimaka min na sauka, ina so zan shiga ban d’aki.”
Da taimakonta ta shiga ban d’aki, da fari fitsarin dake mararta ta so tsiyayewa, sai kuma ta cire kayanta ta shiga baho ta dinga tsala wankanta tana k’arewa ban d’akin kallo, had’uwarta da tsabtarta duka sun birgeta, ga rigar wanka kala uku a jere haka ma towel, mayukan wanke baki da shampoo had’a da turaren baki da na ruwa, sam sai ta manta ma da dare ne ta dinga anfani da komai kamar wata gasar zata tafi, sai da ta ji agogo tayi alamar k’arfe biyu ta buga yasa ta fitowa sanye da rigar wankan data sauko sosai a hannayenta rigar kuma har ta kusa sauka a k’afafunta.
Tana fitowa ta samu matashiyar nan durk’ushe da alama ita take jira, da mamaki tace “Wai dama kina nan baki tafi ba?”
Da ladabi tace “Ban tafi ba ranki shi dad’e, ina jiran umarninki ne ko kuma idan da wani abu da kike da buk’ata.”
Numfashi ta sauke ta k’araso gaban gadon ta zauna tace “To yanzu zuba min abinci na ci sai ki tafi ki kwanta ke ma, dare yayi fa sosai.”
“To ranki shi dad’e.” Ta fad’a tana mik’ewa, saida ta gama had’a mata lafiyayyen abincin ta ajiye mata gabanta har da ruwa da lemu, kallonta tayi tace “Ki je kawai, da safe kya zo ki d’auke kwanukan.”
Jinjina kai tayi ta fita tana mata saida safe, a ladabce kuma a hankalce ta shiga tsakurar abincin tana yi tana nazarin duk abinda ya faru daga safe zuwa daren nan, sai ta ji kamar tayi dariya saboda a almara take ganin abun, sai kuma ta kyab’e fuska ta matso k’walla saboda jin kamar zuciyarta na son yarda da abinda suke fad’a mata.
Tana kammala cin abincin ta koma ban d’aki ta wanke bakinta ta dawo, ruwa tasha kad’an sannan tayi zaune, ta jima zaune kafin ta gyara ta kwanta ta ja zanin rufa lallausa ta rufe jikinta ko rigar wankan bata cire ba.
*Egypt*
Kamar da wasa mai kula da ita ta tabbatar da bata d’akin, fargaba da firgici sai ya hanata fad’a masa ta shiga neman hanyar da zata sanar masa.
Yana tsaye tare da Zafreen ta dafe k’ugu ta matsa ya mayar da ita gidansu ko ta jaza masa bala’i, cike da jin haushinta yace “Kiyi duk abinda zakiyi, ba zan mayar da ke d’in ba sai gari ya waye.”
Juyawa yayi ya shige ciki kai tsaye d’akin da Ayam ta ke ya nufa, bai samu kowa a d’akin ba amma dake har da mai kula da ita su biyun sai kawai ya fito da tunanin ko sun shiga zagayawa da iga ne a gidan, yana fitowa suka had’a da d’aya daga ciki ta dawo, da mamaki ya k’are lata kallo yace “Ina gimbiya take?”
Da ladabi tace “Tana ciki yallab’ai, ita ce ta aikeni na samo mata wannan.”
Ta fad’a tana nuna furanni masu kyau, da mamaki yace “Amma kuma bata ciki, me ta ce miki zatayi da su?”
Girgiza kai tayi tace “Gaskiya ban sani ba ni ma yallab’ai.”
Tureta yayi gefe ya fita a b’angaren ya shiga zagayawa duka gkdan amma shiru, b’angaren ya sake dawowa sai kuma ya ci karo da d’aya mai tsaronta sai gumi take ido sun mata jajir, cikin daka tsawa yace “Ina gimbiya ta?”
Cikin i’ina da tsoro ta shiga masa nuni da hannu tace “Yallab’ai ni ma, wallahi ban san inda ta shiga ba.”
Da matsanancin mamaki yace “Baki san inda ta shiga ba? Kika ce bako san inda ta shiga ba?”
Gaba d’aya ya tashi hankalin gidan ta hanyar sa wa a bincike ko ina, ta b’angare d’aya kuma waya yake amsawa daga waje yana bada masaniya daga masu taimakonshi, dattijon nan dake tare da shi yana gefe tsaye ya kalleshi yace” Yallab’ai. ”
A hassale yace” Me ye?”
A ladabce yace” Ina ga fa kamar sarki Wudar raina mana wayo sukayi.”
Zazzaro masa ido yayi yace” Kamar ya?”
A sanyaye yace” Ina tunanin su suka d’auke ta.”
Jim yayi yana sake rarako idonshi waje ya jinjina kai yace” Kuma fa haka zai yiwu.”
Jinjina kai yayi yana murmushi yace” Lallai sarki Wudar ya nemi tashin hankali da ni, kuma zai ga abinda ya fi k’arfinshi.”
Kallon dattijon nan yayi yace” Zuwa wayewar gari zai samu sak’o daga sarkin Khazira. ”
*Yan uwa kuyi hak’uri da wannan dan Allah*
*Alhamdulillah*
[ad_2]