LU’U LU’U 2

*Washe gari* Zafreen ta gama duk shirinta ta nufi wajen malami Dhurani, bayanan daya bata dai kamar yanda ya fad’awa mahaifiyarta ne a sanda cikinta ya bayyana, dan haka ta dawo rai b’ace na jin cewa akan wane dalili ne k’anwarta ta zama zab’abb’iyar ba ita ba?

Tana d’akin mai cike da tarin tsari da kyau tana had’a kayanta dan tafiya, k’wank’wasa k’ofar d’akin aka yi saidai kafin ta bayar da izini aka shigo, juyawa tayi dan ganin wanene haka? Kyakyawar mahaifiyarta ce ta shigo ita d’aya babu rakiyar bayinta ko sabuwar jakadiyarta, tsurawa juna ido sukayi saida ta tsaya daf da ita, kwalliya da adon dake jikin sarauniyar Khazira wato *Juman* zaka rantse ba ta haifi Zafreen ba, dan irin masu kula da kansu ne fiye da kima.

Cike da nuna damuwa da alhini 脿 fuskar ta cikin tausashiyar murya tace “Gimbiya Zafreen, me kike shirin aikatawa haka? Me yasa zaki biyewa mahaifinki wanda kullum a maye yake? Ina zaki je neman ‘yar uwarki…?”

Cikin daka tsawa Zafreen tace “Ba yar uwata ba ce, ita d’in’ yarku ce da kuke matuk’ar so, wacce ba kwa kula kowa da komai saboda b’atanta, wato dan ita tana zab’abb’iya ko? To zan nemo muku farin cikinku.”

Sake marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace “Zafreen ba haka bane, ke ma fa ‘yarmu ce kuma muna sonki.”

A hassale tace “K’arya ne, da kuna so na dana gani a zahiri.”

Juyawa tayi ta rufe zip d’in jakarta, kallon hadimarta tayi dake tsaye bakin k’ofa ta mata alama da ido, d’aukar jakar tayi ta fita da sauri, ita ma zata wuce sarauniya Juman ta rik’o hannunta tace “Zafreen ki saurareni, ba zan bari ki tafi, yanzu ina zaki je? Ta ina zaki fara? Ba zaki tab’a samun ta ba.”

A wulak’ance ta shiga yatsina baki tana fad’in “Makarantar horar da sababbin d’alibai zan nufa, zan karb’i horon zama ‘yar sanda sannan na nemi taimakon abokaina, zamu sameta kinji ko.”

Fizge hannunta tayi da k’arfi wanda yasa mayafin dake kan sarauniya Juman fad’uwa daga kafad’arta, kallon juna sukayi ido cikin ido sannan ta juya zata fita, cak kuma ta tsaya tare da juyowa a hankali, da mamaki ta dinga kallon wuyan sarauniyar kamar zata had’e ta.

Da sauri ta kai hannunta ta d’aga doguwar sark’ar gwal d’in dake wuyan sarauniyar, ‘yar k’aramar sark’ar dake wuyanta mai bak’in zare da wani k’aramin zagaye kamar ziro, cike da al’ajabi Zafreen tace “Maa, wannan sark’ar ai jabu ce, ina ta asalin?”

Wani masifaffen murd’awa cikin sarauniya yayi inda ta zaro idonta kamar zasu fad’o, a take ta tambayi kan ta “Ya akayi ta gane?”

Dan ko sarki Musail bai tab’a lura da hakan ba, duk dai ma yanzu ya zama bugagge kullum a shaye yake. B’oyayyen numfashi ta sauke tana tunanin abinda zata fad’a mata, dan bata so asirinta ya tonu a yanzun, kafin ta ce wani abu Zafreen ta sake fad’in” Maa dake nake magana fa, ina sark’arki mai daraja take?”

Cikin inda inda tace” Am.. Zafreen, waccen sark’ar ta b’ata shekarar da mukayi tafi da mahaifinki wanda aka mana fashi a hanya, kinsan kuma sark’a ce mai darajar gaske, b’atanta 脿 wuyana zai tashi hankalin ‘yan k’asar nan, shiyasa da taimakon malami Dhurani aka had’a min wannan d’in.”

Marairaicewa tayi kamar zatayi hawaye tace” Na rok’eki ‘yata karki bari sarki ko wani ya ji labarin nan, karki fad’awa kowa kinji.”

Sam fuskar Zafreen bai nuna alamun gamsuwa da maganar mahaifiyar ta ta ba, sai kawai ta girgiza kai ta juya ta fice 脿 d’akin, da kallo ta bita saida ta ga b’acewarta kad’ai ta sauke ajiyar zuciya.

 

*Alhamdulillah*

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button