Lu’u Lu’u 3

Kawar da kansa yayi yace” Kai zan tambaya ai me kake?”

A hankali Haman ya matsa kusan Umad d’in murya a sanyaye yace” Umad ka saurare ni, kaga fa gobe ne tafiyarka, kuma in da zaka je da abinda zaka je yi abune mai matuk’ar mahimmanci, to me yasa ba zakayi duk abinda kasan zai kusanta ka da lamarin nan ba?”

Had’e hannaye yayi ya rumgumesu a k’irji ya sake gimtse fuska a dak’ile yace” Me kake nufi?”

Jinjina kai yayi yace” Yawwa! Ka gane ko? Duk da kai d’in malamin bogi ne, amma ai ba kowa ya sani ba, kenan dole kayi kama da malamin horaswa, daga gobe fa kakin babban major na gandun daji zaka fara sakawa a jikinka, to kana ganin ya kamata a ce ka je a haka?”

Shiru d’akin ya fara d’auka na wasu dak’ik’u, a tausashe ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalli Haman cikin yatsina fuska yace” Na sani Haman, amma ka fahimci wani abu, ni ba zama bane zai kai ni, da na je wurin nan abinda ya kaini kawai zanyi na juyo, ban damu da wata shiga ta ba.”

Cike da gamsuwa Haman yace” Na fahimceka, amma ni ina so ka tuna da nagartar aikinka.”

D’an k’ura mishi ido yayi na wasu dak’ik’u sai kuma ya jinjina kai alamar gamsuwa, hannu ya mik’a mishi sukayi musabaha tare da d’orawa da fad’in” Ka cika alk’awarinka Haman, duk rintsi babu wanda zai san komai akan aikina da kuma shirina, na rok’eka.”

Jinjina kai yayi yana murmushi yace” Baka da matsala da wannan d’an uwa, fatan nasara.”

Hararanshi yayi yace” Ka jira har lokacin shiga na jirgi yayi mana.”

‘Yar dariya yayi yace” To ai kace sammako zakayi, ni kuma ban iya tashin safe ba, kaga kenan saidai muyi waya idan ka sauka.”

Dukanshi yayi 脿 kafad’a yace” Baka isa ba ai yaro, kai zaka kaini har filin jirgi, ragon maza kawa.”

Shafa yalwatacciyar sumarshi yayi yace” Ni ma zan zama jarumi, da fari na saka rai a lokacin da mai martabanmu ya so auro mana zab’abb’iya, to amma da naga an kasa cimma burin sai kawai ni ma na cire rai tare da sauyawar tsarukan k’asar nan.”

Girgiza kai Umad yayi bai ce komai ba ya koma kan kujerar ya zauna, ganin haka ya sa Haman lek’awa ya kira mai askin dan ya rage wa Umad tsirakun daya tara a kai.”

*Larhjadin*

Da sauri suke ta fitowa daga ajin suna tunkarar sale a manger (wajen cin abinci) dan minti sha biyar malamin ya basu.

Ayam kam ba abincin ne ya dameta sai son tayi waya da Momma ta, hakan yasa ta nufi hanyar fita daga b’angaren na su, inda a nan ke da mai wannan alhakin. Sauri take sosai tana k’ara gyara zaman jakarta a bayanta, kusa da k’ofar zata fita wasu ‘yan matan ma suka shigo, kaucewa tayi suka fara wucewa da d’ai-d’aya, amma Zafreen dake k’arshe sai ta shiga kallon Ayam tana yamutsa fuska tana jin gabanta na fad’uwa.

Ayam ma kallonta ta shiga yi da idonta wanda basu da d’igon bak’i ko d’aya, daga kalar farin data mamaye girman idon, sai k’wayar mai d’auke da launin shud’i mai hasken sararin samaniya, ‘yar k’aramar k’wayar kuma wani irin ratsin fari ne mai kama da zaiba, ga shi kuma launin shuud’in har wani tsage-tsage gareshi, daga can cikin k’aramar k’wayar kuma sai ka rantse ruwa ne kake kallo wanda zasu iya tafiya da kai.

Da sauri Zafreen tayi k’asa da idonta tana jan tsaki, a ranta kuma cewa tayi “Mayya kawai.”

Ayam kam da sauri take dama rab’ata tayi zata wuce, dan gaba d’aya kallon Zafreen d’in yasa ta jin jikinta yayi wani iri har tsigar jikinta na tashi. Wajen ta wuce kuma kawai kafad’arsu ta gogi juna, zata fita a wurin Zafreen ta cabko hannunta ta dawo da ita baya, cike da wulak’anci da jin izza 脿 yarenta na slovaque tace “Wacece ke da har zaki rab’ani ki wuce?”

Gyara tsayuwa Ayam tayi a hankali tasa hannunta ta b’amb’are na Zafreen dake jikinta, a tausashe kuma a ladabce itama 脿 harshen slovaque tace “Ni ba kowa bace, amma d’aliba ce nima a makarantar nan, kamar dai ke.”

Ta k’arashe tana nuna Zafreen, cikin jin haushi Zafreen ta nuna kanta tace “Kinsan wacece ni kuwa?”

Wani dogon tsaki Ayam taja tare da fad’in “Shirme kawai, amsar tambayar nan fa na baki yanzun nan, akan me zan tsaya b’ata lokaci na a kan ki?”

Yatsina fuska tayi cike da wata irin gadara da izza ta sake niyyar fita a k’ofar, tare gabanta Zafreen tayi tana fad’in “Ke kin isa ki fad’a min magana sannan ki wuce, k’arya kike.”

Kallon k’awayenta tayi dake gefe suna kallonsu tace “Ku fad’a mata wacece ni, ku fad’a mata ni ke da gaba d’aya k’asar nan da kewayenta, idan har na so yanzun nan zata bar makarantar nan.”

D’aga gira Ayam tayi ta turo d’an bakinta k’arami ta juya ta kalli k’awayen ita ma, wata doguwa a cikinsu ce tayi saurin fad’in” Ke kinsan wacece Zafreen kuwa? To ita ce gimbiyar Khazira, ‘ya d’aya a gurin sarkinmu Musail.”

Babu alamar damuwa ko wata shakka Ayam ta tab’e baki tace” Da gaske? To ni kuma sunana Ayam,’ ya ga… ”

Mai kula da shiga da ficen d’aliban ne ya katsesu ta hanyar fad’in” Kai ku fita a nan, kunsan minti goma na baku ku shiga ku ga k’awar ta ku.”

Da sauri k’awayen suka ce” Gimbiya zo muje, ki rabu da ita zamu had’u wani lokacin.”

Ido cikin ido suka kalli juna amma a take Zafreen tayi k’asa da na ta tana kallon fararen takalmi k’afa ciki masu kamar soso kuma kamar roba dake k’afar Ayam d’in, cike da shak’iyanci Ayam tace” Ki kula malama, wannan fa makarantar gwamnati ce, kuma shekara ta dubu biyu da ashirin muke, babu k’arancin ‘yancin a zamanin nan, bugu da k’ari ni d’in haifaffar Larhjadin ce, esxuze moi.”

Baki bud’e suka bita da kallo har ta tsaya kusan mutumin dake zaune cikin case d’in shi, magana ta mishi hakan yasa shi mik’o mata wayar tafi-da gidanka ta shiga danna lambar gidan na su, dan ba kowane lokaci ake basu damar anfani da wayoyinsu ba.

Rai b’ace kamar zata mutu ta juya suka fita tana fad’in “Na fasa ganin shi d’in ma.”

Da sauri suka rufa mata baya d’ayar na fad’in “Gimbiyarmu, kar ranki ya b’ace kinji, k’aramar alhaki ce wannan, zaki iya sa wa 脿 koreta ai.”

Cak ta tsaya sai kuma ta kalli wacce tayi maganar, ita kuma sunkuyar da kan ta tayi k’asa da tunanin ta fad’i ba daidai ba.

Murmushi ta saki tace “Kin kawo shawara mai kyau *Laika”*, ban wayata?” Ta fad’a tana tara mata hannu, mik’a mata tayi ta karb’a ta shiga danna wasu lambobi sannan tayi gaba suka nufi na su b’angaren tana amsa waya.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button