Lu’u Lu’u 3

*Ayam* kam na ta buga wayar amma shiru ba’a d’aga ba, d’an tsakin rashin jin dad’i tayi tace” Watak’ila Momma na mak’ota.”

Aje wayar tayi ta kalli mai kula da k’ofar tace” Shin-shiy (nagode).”

Da kallo mamaki ya bita 脿 zuciyarshi yana fad’in” Me yasa take son raina min hankali yarinyar nan, kullum da kalar yaren da take min.”

Zata shiga cikin sauri shi ma zai shiga a hanzarce, kafad’unsu ne suka had’u, amma Ayam dake wata pigigiya ce saida ta nemi fad’uwa a k’asa, cikin takaici da rashin sanin yaren da ita kanta tayi tace” Tirr! Yau jakuna nake ta had’uwa da su.”

Gyara jakarta tayi sai a lokacin ta d’aga kai ta kalli dogon mutumin, mummunan fad’uwa gabanta yayi sakamakon tsoron daya bata, ba wai hallitarsa ke da ban tsoron ba, had’add’iyar fuskar shi da babu annuri a cikinta, fararen idonshi k’anana daya zazzaro ya k’ura mata, girarenshi duka biyun daya bala’in d’agesu sukayi sama daga k’arshensu, ga kuma matsatsen bak’ar rigar dake jikinshi data fito da k’irarshi.

D’an bakinta ta bud’e har hak’oranta suka fito ta shiga zazzare ido, gyara tsayuwarta tayi tare da sunkuyar da kanta, ko Momma da Papanta bata tab’a had’a ido dasu ba haka, duk yanda take son su kalleta itama kuma ta kalli cikin idonsu abun ya gagara, da sun had’a ido suke d’auke na su, haka ma daga k’awayen abokai da sauran mutane, hakan ya dameta har wata rana ta tambayi Deeyam me yasa bata had’a ido na tsayin sakan uku da ita? Sa茂 tace mata “Ji nake kamar ina kallon babban teku, hakan ya sa naji kamar zan fad’a ciki.”

Sake d’aga kanta tayi ta kalleshi, tar-tar suka sake had’a ido da shi yana mata mugun kallon nan kamar zai taka wuyanta ya yankata, mitsitsika idonta tayi ta motsa bakinta ta aro jarumta cike da tsiwa da tijara tace” Malam baka gani ne? Ina kake kallo da zaka kawo min hari haka?”

Yanda yake kallonta babu rusunawa da kuma sak’onnin dake cikin kallon yasa ta juyawa da gudun tsiya ta shige ciki tana k’yalk’yala dariya kuma tana fad’in” Sai ka ce wani dorinar ruwa wacce kullum fuskarta a murtuke.”

Da kallo ya bi bayanta, yanda take gudu tana dariya hannayenta rik’e da jakarta, kayan makarantar ne jikinta, riga mai hannaye iya damtse mai ratsin shud’i, sa茂 farin wando shi ma da ratsin shud’i amma iya gwiwa yake, rigar ma tsayinta ya sauko kan cinyoyi kuma botira gareta a gaba har k’asa, sai hula fara dake kanta wacce a saninshi dai yasan ba doka bace sakawa.

Takaici mai sunan takaici, haushi iya haushi had’e da jin d’aci a mak’oshinshi, ga kuma azababbiyar tsanar yarinyar da yaji har zuciyarshi, ba dan komai ba sai yaren da tayi magana dashi na Italy, shekararsa shida a garin yana karatunsa, dan haka babu abinda za’a fad’a ya gaza ganewa.

Wata zazzafar iska ya huro ya shiga d’aga k’afar sa wanda kana gani zaka san ranshi a b’ace yake zuciyarshi kuma tafasa take, cikin ranshi ban da tsaki da k’wafa babu abinda yake, cikin jin haushi da masifa yake ayyana “Busassar banza, kafin na gama abinda ya kawoni sai na tabbatar ba kya iya banbance tsakanin ruwa da yawu, banza mai idon mayu.”

Kai tsaye ofishin babban jami’in ya shiga ya gabatar masa da kan shi, tarba ya samu kafin ya had’a shi da k’aramin mataimakinshi ya rakashi zuwa masaukin malaman ga masu buk’ata.

 

*Alhamdulillah*

The post Lu’u Lu’u 3 first appeared on 2gNovels.com.ng.

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button