Lu’u Lu’u 4

Cikin sand’a suka dinga fita a d’akin har sukayi sa’ar haurawa ta wani corridor ba tare da tsoron su fad’i ba, ai kuwa a sauk’ake sai gasu a b’angaren malam kamar wasu b’arayi, jerawa sukayi suka dinga hawa matakalar har suka iso wajen d’akunan, kallon juna sukayi Deeyam tace “Ina d’akin?”
Nuna musu Ayam tayi tace “Wannan d’akin ne ai babu kowa.”
K’arasawa sukayi suka sake tsayawa cirko cirko, kallon su Ayam tayi tace “Yanzu Sabrine ke ki fara shiga.”
Waro ido tayi tace “Me yasa ni zan shiga.”
Cikin rad’a Ayam tace “To ai kin fi mu kyau da dirin halitta mai kyau.”
Harara ta wurga mata tace “Na k’i to, babu ruwana ni.”
Juyawa Ayam tayi ta kalli Deeyam tace “To ke ki shiga, tunda kina da abubuwan d’aukar hankali.”
Cikin fad’a Deeyam tace “To wai ke da kika jagorancemu me zai hana ki shiga?”
Wata dariya tayi ta kalli kanta tace “Haba dai, dubeni fa, aini bana da fasalin d’aukar hankalin namiji, ba kowane namiji nake birgewa ba saboda nayi rama dayawa.”
Tab’e baki Sabrine tayi tace “To saidai mu koma kam, amma babu inda zanje.”
Deeyam ma had’e hannaye tayi tace “Ni ma haka.”
D’ayar ce ta kallesu tace “To mu koma kunji, bana son wani ya ganmu za’a hukuntamu.”
Cikin rad’a Ayam tace “Yanzu ku d’an aikin nan ne zai gagaremu? Kun manta irin tijarar da muka zuba a baya ne?”
Deeyam ce tace “Bamu manta ba, amma dai yau kam ni dai babu ruwana, inda matsalar take shine rashin sanin waye malamin, ni bansan me yasa kika damu da son sanin wane iri ne shi.”
Gyara tsayuwa Ayam tayi da kyau ta kallesu tace “Ku fad’a min zaku shiga ko a’a?”
“A’a.” Sabrine ta fad’a tana juya baya, jinjina kai tayi tace “Shikenan, ni zan shiga ciki, amma ku jirani a nan.”
Murmushi Deeyam tayi tace “Fatan nasara.”
Harara Ayam ta jefa mata tana gyara hularta tace “Matsalarku ce.”
Kallon k’ofar d’akin tayi tana sauke numfashi, wani yanayi na tsoro da fad’uwar gaba take ji wanda bata tab’a ji ba, hatta da jinin jikinta ji take ya k’ara gudun tafiyarshi.
Cije leb’enta tayi na k’asa sannan ta kai hannu ta k’wank’wasa k’ofar d’akin, amma sai ta ji shiru babu ko alamar motsi, sake kwank’wasawa tayi nan ma shiru, a karo na uku ta sake kwank’wasawa tana jan gajeran tsaki.
Deeyam ce tace “Ayam, tunda kika ji shiru ki zo mu je kawai, watak’ila baya nan.”
Sabrine ce ta karb’e da fad’in “Ko kuma ma bai zo ba.”
Juyowa tayi ta kalli Sabrine da tayi maganar tace “Hakane?”
D’aga mata gira tayi alamar e, jinjina kai tayi tace “Bari mu gani to.”
Cikin sand’a ta kama hannun k’ofar ta murd’a a hankali, jin ta bud’e yasa suka kalli juna, maida kallonta tayi ga k’ofar ta tura a hankali tana shiga cikin d’akin.
Tattausan k’amshin turaren 112 ne ya fara mata maraba, sai kuma siririn hasken daya gauraye d’akin, komai na d’akin a gyare kuma a killace yake sannan a tsaftace, babu alamun da suka nuna akwai mutum a d’akin, hakan yasa ta bayan k’arewa d’akin kallo ta jawo k’ofar da niyyar rufewa.
Cak! Ta dakata sakamakon tsikayar wani k’aramin hoto a gefen gadon ajiye, sakin hannun k’ofar tayi ta k’arasa da sauri ta d’auki hoton, k’urawa dattijuwar matar ido tayi mai cikar kamala da haiba, tana cikin shiga ta alfarma kamar wata sarauniya. Samun kanta tayi da sakin murmushi sanadiyar k’aunar matar data ji, a hankali a asalin harshenta na slovaque tace “Watak’ila ya manta da hoton ne?”
Sai kuma ta tambayi kan ta “To amma wa ya zauna a d’akin?”
Rashin sanin amsar yasa kawai ta d’aga kafad’a alamar ko oho, juyawa tayi ta fara tafiya hannunta rik’e da hoton.
Tana daf da hita aka bud’e k’ofar k’aramar ban d’akin dake cikin d’akin, da sauri kuma a mugun tsorace ta kalli inda ta ji k’arar, a wani bala’in tsoracen wanda bata san sanda ya ziyarceta ba ta saki hoton wanda ke lullub’e da kwalba ya fad’i k’asa.
K’arar glass d’in da kuma ihunta a tare suka gudana, sai kuma tayi saurin yin gum da bakinta kamar wacce aka tusawa k’wallon goriba a bakin.
Idonta masu abun al’ajabi ta zuba masa tana kallo ba tare da rusunawa ko jin d’ar a yanda ta ganshi ba, a hankali take yi tana k’yabta idonta tana kuma sauke numfashi kamar wacce aka b’atawa rai, a zahirinta kamar jira take yace kul tace cas, amma a bad’ini kuma gabanta ci gaba yake da fad’uwa, ganinshi d’aure da towel d’in nan kalar shud’i ba k’aramin gigita mata lissafi yayi ba, dogo ne sosai mai k’ira da zubin jarumai, duk da ba wata murd’add’iyar sura ce da shi mai jan hankali ba, amma dai yana da fasali mai kyau wanda zai iya juyar da k’irarshi a duk ta yanda ya so.
Duk da bak’i ne amma kuma bak’inshi mai kyau ne da k’yalli kamar na macen dake samun gyara a kai a kai.
A hankali cikin b’acin rai da mamakin abinda ya kawota d’akinshi ya tsura mata ido, yana d’ora ido 脿 kan ta saida launin idonshi suka canza tsabar haushi da takaici, sai yake bala’in jin kamar ya k’urma ihu dan ya samu sassaucin abinda ya tokare masa zuciya.
Ba ma wannan ba, wai a kan wane dalili ne shi kam yake had’uwa da wannan mai zubin aljanun ruwan, ga ta dai 脿 cikin kayan bacci wando iya gwiwa da riga mai k’ananan hannu, gaba d’ayanta fa ba zata gagareshi ya dunk’uleta a hannu d’aya ya jefata a hudar hancinshi sannan ya fyatota.
Kallon hoton dake k’asa yayi, da sauri ya tako ya tsaya gabanta tare da durk’usawa yana kallon hoton, a mugun fusace ganin yanda hton ya fashe ya sa ya d’ago ya k’ura mata ido.
Ayam da tunda ya fara takowar nan da sauri gabanta ya shiga dakan uku, kasa motsawa tayi sai bakinta data warwareshi daga kumburewar da ta mishi, hannayenta ta d’ora kan mararta ta dafe tana fatan kar fitsari ya taho mata.
Umad kam cikin fitar hayyaci ya d’aga hannunshi ya wanketa da mari, a k’ufule ba tare daya bata damar gama fahimtar rad’ad’in ba ya nuna mata k’ofa da yatsa cikin hard’add’iya kuma nagartacciyar muryarshi da harshenshi da ya fi k’warewa a yaren Gallois yace “Fita a nan, kuma karki bari mu sake had’uwa, *b’arauniya* kawai.”
Da sauri ta d’aga idonta dake kallon k’asa ta kalleshi jin sunan daya bata. Shi ma sai lokacin ya fahimci wani abu a tare da ita, ya mareta marin da yake da tabbacin ya ratsata sosai, to amma” Me yasa bata yi ihu ba? Kuma bata fad’i ba duk da rashin nauyinta.” Abinda ya tambayi kanshi kenan, sam kamar ma ba ita ya mara ba a fuska.