NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 48

_NO. 48_*


……….Ummukulsoom ta daɗe tana barci kafin ALLAH ya bata ikon tashi, ta sauke ajiyar zuciya ganin babu Amaan a ɗakin. Gadon ta fara gyarawa bayan ta sakko, kafin ta gyara ko ina na ɗakin ta fesa turaren ɗaki, batai
gigin koda leƙa faloba, duk da zuciyarta na bata bayama sashen, dan batajin motsin komi.
    Bayi ta faɗa tayo wanka, hankalinta kwance ta ɗauro towel ɗinsa, bashi da wani tsawo, dan haka iyakar cinyarta ya tsaya.
    Ƙara sowa tai cikin ɗakin da ɗan hanzari saboda wayarta dake ring, ta share ruwan fuskarta tana murmushi da ɗaukar wayar, gudun karta saka a kunne ta jiƙe da ruwan dake bin fuskarta sai ta saka hans free. Cike da tsokana take faɗin, “Kaga ta gidan Muhseen amaryar ƙamshi”.
      Cikin sanyin murya daga can Bily tace, “Bestie ykk? I miss you so much wlhy”.
     “Nima haka Bily na, an mana wayo ko sallama bamuyiba jiya, amma yanaji muryarki haka ko baki da lafiyane?”.
        “Ummu bazaki ganeba, wlhy Muhseen mugune”.
    “Na shiga uku ni kulsoom, mugu kuma bily? Ya zaki danganta mijinki da wannan sunan miyay miki haka?”.
     Kuka Bily ta kuma sanya mata, da ƙyar ta lallasheta tai shiru. Bily tace “Ummu kofa tafiya bana iyayi wlhy saboda tsabar rashin tausayin da ya gwadamin”.
      Sai yanzune Ummu ta ranfo inda Bily ta dosa, ta sauke ajiyar zuciya, dan duk zatonta da wani mugun abu yayma Bilyn, yanda Bily ta kare maganar tana kuka saiya saka Ummukulsoom kwashewa da dariya, harga ALLAH bily ta bata matuƙar dariya da tausayi……
     “Yanzu nan bestie dariya ma zakimin ba zakiji tausayina ba? Wlhy serious nake miki maganar nan, yanzu hakama muna asibiti fa”.
    Tsayawa Ummu tai da dariyar babu shiri, “Wai dan ALLAH Bestie da gaske kike?”.
       “Hummm da kin ɗauka wasa nake ko? Shiyyasa naketa cewa ki faɗamin yaya abun yake? Tunda ke kinsan sirrin, amma kika kifeni Ummu, gaki nan hankalinki kwance k tunda kin wuce wannan siradin tun shekaru shida da suka shige…..”
      Murmushi kawai Ummu tayi tsoro na sake tsargata, Bily batasan itace ma wadda batasan komanba, ita a wancan zaman auren banda kiss da Amaan yay mata gaban Bukky batasan komai ba daya shafi rayuwar aure…..
    “Kinyi shiru bestie ”.
Ajiyar zuciya Ummu ta sauke idonta yay kwale-ƙwale da tsoro, “Toni bestie mi zance, kiyi haƙuri kawai kowa da haka ya fara, amma shima dai Muhsin yayi wauta wlhy, koda yake bamaga laifinsa ba tunda farin shigane, yanzu ya jikin?”.
     “Da sauƙi, gashi nan zamu koma gida, dama babu wanda yasan mun fito sai ke yanzu dana sanarmawa”.
       “Sorry bestie kinji, zan aiko a amsarmin sauran kazar amarcin”. Ummu ta kare maganar da tsokana.
    Ƙitt Bily ta kashe wayar tana mata ƙunkuni.
   Hakan sai ya saka Ummukulsoom ci gaba da dariyarta, ta yaye towel ɗin hankali kwance  zata shafa mai.
    Ganin kamar inuwar mutum ta cikin mirror ɗinne ya firgitata, tai saurin maida towel ɗin ta ɗaure tare da juyowa cikin zafin nama. Ba ƙaramar faɗuwa gabanta yayi ba ganin Amaan a tsaye jikin ƙofa ya harɗe hannayensa duka a ƙirji, hakama kafafunsa harɗe suke, ya jingina rabin jikinsa a bango. Harga ALLAH batasan adadin lokacin daya ɗauka a wajen tsayeba, babar damuwarta ma ace yaji wayar da sukayi da bily da kuma yaye towel ɗin da tayi yanzun, dan ta tabbata dolene ace ya ganta.
          Ƙasa tai da kanta tana haɗe fuska da matse ƙafafu alamar jin kunyar ganinta da yay da mazuran naɗe tabarmar kunya. Ya lumshe idanunsa daya janye daga kanta ya kuma buɗewa a kantan…
     “Amma haka bashi da ƙyau gaskiya, yakamata kafin ashigoma mutum a dinga neman izininsa mana” ta ƙare maganar cike da tsantsar takaicinsa da haushi.
     Murmushin gefen baki yayi yana warware hannunsa dake a ƙirji, hakama kafafunsa ya tsaya kyam a kansu tare da tura hannayen duka aljihun wandon jeans ɗinsa, Yanda yake kallonta ƙasa-ƙasa ne yasata jin ta sake takura, ya fara takowa a hankali cikin nutsuwa zuwa gareta.
     Bata iya motsawa ba, dan tanajin kunyar ta juya baya saboda towel ɗin jikinta, kasantuwarta mai ɗan jiki ya ɗaga daga baya sosai fiye da gaba. Rumtse idanunta tayi da ƙarfi saboda jin tsayuwarsa gabanta gab da ita sosai har tana iya jiyo saukar numfashinsa.
          Sunkai minti biyu a haka kowa ya kasa yin abinda ya dace, ita dai kunyace da takaici, shiko tsabar miskilancine da kasalar dake saukar masa a hankali.
      Ya turo numfashi kaɗan tare da zare hannayensa daga aljihu ya ɗora bisa kafaɗar Ummukulsoom.
   Ko motsi bataiba balle ta ɗago ta kallesa, sai dai salon bugun zuciyarta ya sake canjawa.
     Ganin haka sai ya nufi takalar magana, yakai hannu zai kwance towel ɗin.
   Babu shiri Ummukulsoom ta ɗago a harziƙe tare da riƙe hannunsa.
    Jaa yay kamar zai sunce saboda hannunsa na riƙe da tawul ɗin. Ganin bata da mafita sai kawai ta faɗa jikinsa ta ƙanƙamesa iyakar ƙarfinta.
        Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana wani munafikin moso tare da saka hannayensa biyu duka a bayanta ya zagayeta yana ƙara mannata sosai da jikinsa tare da lumshe idanunsa, duk illahirin tsigar jikinsa na tashi.
      Saida sukaja wasu mintuna a haka kafin ya iya buɗe baki da ƙyar yana faɗin, “Ke da baki fara ɗaukar karatunba, amma kike yima wanda yashiga makarantar dariya ko?”.
        Sosai gabanta ya faɗi, tai ƙoƙarin janye jikinta ya kuma matseta.
     “Ni sakeni, banason haka”.
    Babu musu ya saketa, tai saurin barin wajen tana harhaɗe hanya saboda kunya, shiko ya bita da kallo da mayun idanunsa harta ɗauki hijjab ta saka. Numfashi ya sauke a hankali ya zauna akan stool ɗin mirror ɗin.
      Bata kulashi ba, ta buɗe akwatinta guda ɗaya da aka kawo ta ɗauki kaya, bayi ta shiga.
    Baice komaiba sai kansa da ya dafe, yanason Ummukulsoom, amma yasan ita bata sonshi, amincewarma da tayi ta dawo garesa saboda mahaifin sane. Duk sanda ya tuna shifa kaɗai yake shirmensa a sonta jikinsa yakanyi sanyi ƙalau, haka zuciyarsa take, idan har ta tashi son abu bata ɗaukarsa da wasa, hakama idan ta tsanesa bata ma abun ƙin sauƙi. Iska yaɗan huro a bakinsa ya miƙe ya fice a ɗakin, dama ya shigone dan ya tadata tayi breakfast ganin rana tayi, saiya isketa tana waya da bily.

     Lokacin da Ummu ta fito Amaan ya fice, taja siririn tsoki tana zama tai ƴar kwalliya mara yawa, tare da ɗaura ɗankwalin daya zauna ɗas a kanta, ta birkiɗe jikinta da ƙamshi na musamman, daka ganta kaga amarya ta gaske, mayafi ta ɗauka a hannu da wayarta ta fito falon.
        Amaan na kwance cikin kujera idonsa a lumshe tamkar mai barci, sai dai idonsa biyu, ya tafi duniyar tunanine kawai a sashen aiki.
    Kallo ɗaya Ummukulsoom tai masa ta zauna cikin kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta fara latsa waya.
       Ƙamshin mayen turarenta dake rikita lissafinsa ya mamye dukkan hancinsa da zuciyarsa, duk yanajin motsinta, sai dai yaƙi nuna hakan, kaɗan ya buɗe idanunsa a kanta yana ƙarema ƙwalliyar tata kallo, ta masa ƙyau sosai dan a asalin bahaushiyar tata take.
       Sai da ya gama ƙare mata kallo son ransa sannan ya buɗe idonsa sosai a kanta yana mata kallon kai tsaye.
   A jikinta taji ana kallonta, dan haka taɗago fararen idanunta tana kallon sa ba tare data ajiye wayarba.
    Gira ɗaya ya ɗaga mata. Ita kuma ta hararesa ta ɗauke idanunta.
        Janye nasa yayi shima ya maida ya lumshe, kusan seconds 10 ya sake buɗewa, wayarsa ya ɗauka ya shiga WhatsApp, kai tsaye inbox na Ummu ya shiga, ilai kuwa tana online, dama yayi zargin hakan ne, danya duba wayarta yaga ba kowanne chart takeba.
      Saƙo ya tura mata.
Tsabar mamakinsa saida ta ɗago ido ta kallesa, wato gata gashi zaune a waje ɗaya, tsabar bazai iya buɗe baki ba shine ya turo mata wai ta tashi suje su karya. Shareshi tayi.
   Ya sake tiro mata “Please mana Babie”.
      Leɓenta ta ciza na ƙasa, cikin son ƙureshi ta tura masa, “Indai bazaka faɗa da baki ba a barsa kawai”.
     Hannu ya kai saman kansa, dan wlhy ciwo yake masa saboda hayaniya, shi a ganinsa ba ƙaramin sake mata yakeba, yama kai maƙurar da yake ganin yazama mai surutu tsakanin jiya da yau.
   Wayar ya ajiye ya miƙe zuwa inda take, ya zare wayarta ya aje gefe, ɗago ido tayi ta zuba masa cike da tsiwa, sai dai yanda ya kafeta da nasa shima sai bakinta ya kasa furta komai. Ba tare da ya janye idanunsa ba ya ranƙwafo gaba ɗayanta ya ɗauka. Kallon kanta tayi ta kallesa da mamaki, ya lumshe mata idanu a hankali, dukda yaji tanada nauyi bai sauketa ba, sai takawa da ya farayi zuwa ga dani ɗin.
        Ya jawo kujera da ƙafa ya ɗorata akai yana ɗan sauke numfashi kaɗan alamar dai tanada nauyin.
        Ummu dai tsiwa ta koma ciki, sai kallon mamaki da take binsa dashi har shima ya zauna kujerar dake kallon tata, hannayensa duka ya saka cikin nata yana mai kafeta da idanu, duk yanda taso karsu haɗa ido hakan ya gagara, dan idanun nasa tamkar mayen ƙarfe haka suke, ba tare da tayi zato ko tsammani ba taji yace, “Ina ƙaunar ki Ummukulsoom, so irin wanda nake fatan mu kasance har a aljann…”
    Da sauri tai yunƙurin zare hannunta yay azamar sake damƙewa.
     Sosai ta kuma haɗe rai fiye da yanda tashi fuskar take shima, “Amaan karka yaudari kanka da wannan kalmar, domin Ummukulsoom ɗinnan ce dai ƙwaila mara ilimi daka sani, ba soyayya ta maidoni gidanka ba, na dawone danna rama *ALKAIRI DA HALLACI* ne kawai”.
     Tuni idanunsa sun fara canja launi, dan ya gama ƙosawa da yawan magana, daurewa kawai yakeyi saboda itace.
    Cikin halin ko in kula Ummukulsoom ta janye hannunta da idanunta ta hau buɗe abincin dake dani ɗin. Lafiyyen breakfast ne na musamman da Momcy ta shirya musu da hannunta, da kanta ta zuba masa ta tura gabansa, itama ta zuba nata.
      Sam taƙi yarda su kalli juna, abincinta takeci a nutse cikin kwanciyar hankali. Gani. taci kusan rabin nata shi baiko fara ciba sai ta kallesa, batare da tace Uffan ba ta janye idanunta tana taɓe baki.
    Tashi yay yabar wajen, ta bisa da kallo ƙasa-ƙasa harya shige bedroom.
     Baki ta taɓe taci gaba da cin abincinta hankali kwance. Tana kammalawa baƙi na shigowa, ashe ƴan buɗar kai har sunzo, saboda baki ƴan nesa da zasu wuce.
         Jitai gaba ɗaya damuwarta ta gudu ballema su murja ne dasu Nusaiba, duk sun fita a kamanninsu, idan ka gansu zuwa yanzu saika ɗauka sun kusa haihuwar kamar Ummukulsoom, dukda kasantuwarta mai jiki kuwa. Su kansu a duk lokacin da suke gabanta duk sai su raina kansu, sunsan Ummukulsoom tayi gaban da za’a daɗe ba’a cimmata ba, su Zeenat suna matukar yin takaici idan suka tuna sune suka cuci kansu da iyayensu, da yanzu suma suna tare da Ummukulsoom, amma gashinan ko ƴar secondary ɗinma basu kammala ba, dukda suna aure a birni babu wani cigaba a tattare dasu, tamkarma basuyi aji uku na makarantar ba.
        Tsokanarta suka shigayi sosai tana biye musu, dan sam Ummu bata da girman kai ko kyankyamin ƴan uwanta, ni’imar da ALLAH yay mata bata sakata bijirema gaskiya ba a mu’amulanta da kowanta.
      Wani abincin ta sake ɗibarma Amaan ta dora a babban tire, dan duk abinda ta tanadi masa bazata yarda ita ta cutar dashi ba, sauran abincin ta kawoma su murja, taje ta ɗauki nasa ta nufi bedroom ɗin.
    Hakanne ya saka su Hassatu fahimtar angon yana ciki kenan.
      
    Kwance ta iskeshi kan gado ya ɗora filo saman kansa ya rufe fuska, ta ɗanyi murmushi tana ajiye tiren a dirowar gefen gado. sannan ta zauna a gefen gadon kusa dashi kaɗan.
     Tunda ta shigo yana jinta, amma baiko motsa ba.
        “Karka ce zakayi fushi da abinci a kaina dan nikam babu ruwana, abinda kawai na sani shine bai cancanci zuciyarka a yanzu taso ƙwaila ba mai karancin ilimi a matsayin matar aure, dama matsayin yaya da ƙanwane zaifi dama-dama Alhaji, ga abincinan kaci, kokuma naje na sanarma Dad…”
    Ta ƙare maganar da miƙewa…
    Caraf ya riƙo hannunta, juyowa tai ta kallesa babu shiri, har yanzu kansa na cikin filon, zatai magana ya fisgota ta faɗo kansa gaba ɗayanta. Janye filon yay tare da ɗora ɗayan hannunsa saman bakinta jin zatai magana. Ya mirginata ta kwanta saman gadon sosai, yayinda shikuma ya maida rabin jikinsa a kanta yana zuba mata dukkan idanunsa cikin nata.
      Sosai tsoro ya shigeta, dan bata taɓa ganinsa a irin wannan yanayinba, idanunsa gaba ɗaya sun koma wani iri, hakama fuskarsa a matukar ɗaure take.
        Murya can ƙasan makoshi ya fara magana, “Duk abinda naso harna iya bayyanasa ga duniya koda a kan fuskata ce to lallai wannan abun mai matuƙar darajane a gareni” ya kama hannunta ya ɗora saman ƙinrjinsa “Saurara kiji yanda zuciyata ke nata gudun, ke lauyace, ko ban faɗaba ya dace ki fahimci mijinki a yanzu. ki kuma yafe masa laifinsa na baya, badan na wulaƙantaki na faɗa miki wancan maganarba, nayine domin ki zuciya wajen maida hankali a neman ilimi, wanda suke tunanin baki kaiba susan kinma wuce, ki tabbatarma da duniya babu wanda yafi wani ta hanyar dukiya ko ilimi sai wanda yakasance mai rinjayen tsoron ALLAH, sai dai ina roƙonki karki tambayeni dalili, dan sirrin wadda bazan iya tonawa asiri bane har ƙarshen numfashina, sai dai ki sani, ko wayar gari akai babu raina to *SON* kine sanadi Ummukulsoom”.
     Yana gama faɗa ya miƙe daga jikinta, baiko kalli abincinba ya fice daga ɗakin.

      Lumshe ido Ummukulsoom tayi a hankali maganganunsa na shiga kowanne sashe na jikinta, Amaan ɗane na ƙwarai da kowanne iyaye zasuyi burin samu, bai yarda ya zubdama mahaifiyarsa mutuncinta ba da ƴan uwansa a gaban matarsa, itama bayasan tozartata shiyyasa ya zaɓi shiga ƙuncin, maganar baba gaskiyace da yake sanar mata aduk yanayin data tsinci kanta ta kalli na ƙasa da ita bana sama da itaba, inhar bazata zama mai afuwa ba to itama baza a taɓa mata afuwa ba, kuma zuciyarta zata zama mai ƙishirwar samun salama a kowanne motsi na rayuwarta, da Amaan bason gaskiya yake mata ba bazai taɓa cigaba da bibiyar rayuwarta ba a ɓoye, da bazai kamu da ciwon hawan jini ba, dan kuwa Attahir ya bata result ɗin gwajin farko da akaima Amaan akasan yana da hawan jini, bayan ya saketa ne da wata ɗaya, damuwar da ya shiga ya sakashi kwanciya ciwo a syria, ga aiki da sukazoyi a gabansu, shine ya kaisa asibiti aka tabbatar masa yanada hawan jini, saida Attahir yayta ƙwalƙwalarsa da ƙyar ya sanar masa abinda ke damunsa akan rabuwasa da Ummukulsoom, amma sam sai yaki saurarensa a lokacin shima dan kawai ya horasa, har suka baro Syria Amaan hankalinsa baya tare da tunaninsa, ba komai ke kuma tada masa hankaliba sai ganin ya zalunceta, abinda yay mugun tsana fiye da komai kenan a rayuwarsa……..
       Saƙon daya shigo a wayarta ne ya maidota hayyacinta, ta ɗauki wayar ta duba duk zatonta ko bily ce, amma sai taga Amaan ne, da mamaki ta buɗe saƙon.
     *_“Ba kowace zuciya bace zata fahimceni, ba kowane tunani bane zai fassara manufata, ba kowanne alƙali bane zai adalci a shari’ata, ni kaina nasan na cancanci Ummukulsoom ta tsaneni, dan babu mace data san darajar kanta da za’a jefeta da kalmar ƙwaila mara ilimi bata zafeta ba a rai da rayuwa, ni kaina dana faɗa a tsawon shekara shidda kalaman sunamin zafi balle ke dana faɗawa, kunyar furtasu ce yasa na ɓadda kama nazo miki matsayin Abdul-Waheed, bazan tilastaki ki soniba Ummukulsoom, sai dai ina roƙonki dan ALLAH ki yafemin ƙuntata miki danai da waɗannan kalaman, har abada bana sha’awar rayuwa ko mutuwa da haƙƙin wani a kaina koda da mummunan kallone….”_*  
        “Lokaci yayi da zaki manta komai ki karɓi Amaan Ummukulsoom”.
    Maganar Maman Ahmad ta doki dodon kunnenta, a firgice ta kalleta, saita ganta zaune kusa da ita alamar tare suka karanta saƙon.   “Aunty Hafsat yaushe kikazo?”.
     “Tun sanda kika fara karanta saƙonnan Ummu, dan kuwa nazo zan shigo naga Amaan ya haɗa kai da mota a harabar gidannan, hakanne yasa na fahimci akwai matsala, halan rashin kirki kika gwada masa a daren jiya?”.
     Jiki a sanyaye Ummu ta girgiza mata kai, “Wlhy banyi masa komaiba ni, kawai dai da safennan ya furta kalmar yana sona nikuma nace mizaiyi da ƙwaila mara ilimi”.
      “Banga laifinkiba da kika furta masa hakan, dan yanada ƙyau yakuma sanin darajarki, sai dai shawarar dazan baki Ummu ki ture komai a ranki ki zauna lafiya gidan aurenki, duk wani mutunci da kike tunanin kankaroma kanki ga Amaan mahaifinsa ya gama kankaro miki shi a gaba ɗaya ahalin Amaan ba Amaan kawai ba, ki kalli ƴan uwanki kawai kiga yanda kikai musu rata, Amaan mutumin kirkine, baya shaye-shaye ko neman mata, baya duk wani ashararanci da sunan wayewa, a zamanku bai taɓa cuta mikiba ko muzguna miki, rashin kulawa dake kuwa auren haɗi akai muku, ku duka babu wanda ke kula juna k da shi, iya jigata Amaan ya jigatu akanki, tun bayan rabuwarku bai sake sukuniba, dan ALLAH ki yafe masa dan nasan kema wlhy kina sonshi Ummukulsoom, kina dannewane kawai”.
      Shiru Ummukulsoom tayi tana haɗiye wani yawu mai kauri a maƙoshinta, duk abinda Maman Ahmad ta faɗa gaskiyane, dan irin haka Hajiya yaya da Gwaggo hinde suka faɗa mata, irinshi Inna laraba da Ummi da bily da Attahir suka faɗa mata, irinshi babanta da Abba suka faɗa mata, to mizaisa ta cigaba da kafewa akan abinda baikai ya kawoba, kowa yana kuskure ai a rayuwa ko, sam batai zaton yanada sauƙin halima irin hakaba, dan daga jiya zuwa yau da aka kawota gidan duk da rashin son maganarsa haka yaketa ƙoƙarin lallaɓata domin kawai ta fahimcesa……
     “Ummu karki ƙuntata ranki inhar bakison Amaan, tashi muje ke ake jira, dama kiranki nazoyi”.
     Ummu batace komaiba ta tashi, fuskarta ta gyara kamar yanda maman Ahmad ta umarceta suka fita.
     A mamakinta su murja duk sunbar falon, sai Amaan kwance cikin kujera Attahir na gefensa, da alama dai akwai matsala, dan yanda Attahir ya watsa mata harara kawai ya isheta amsa.
         Risinawa tai ta gaida Attahir, ƙin amsawa yay ya ɗauke kansa, Amaan na jinsu, sai kuma yaji babu daɗi da Attahir bai amsa mata gaisuwarba, amma baice komaiba.
       Jiki a sanyaye tabi bayan maman Ahmad suka fice.
     Saida Maman Ahmad ta fara rakata ta gaida dad da Momcy sannan aka maidota tsakar gida inda buɗar kai ya gudana, ba wani lokaci aka jaba, rabone kawai sai nasiha da aka ƙara mata, harda ƴan ƙwallanta da zasu tafi kuwa, sauƙintama anan aka bar maman Ahmad, sannan ba’a maidata sashen taba tana wajen Momcy daketa nan nan da ita kamar ƙwai ɗaya a miya.
      Suma wasu cikin ƴan Ajiwa aranar suka tafi, sai makusanta sosai aka bari, dayake zuwa yanzu Momcy karɓar mutunci take musu, dan sunga canji sosai a wannan bikin, waɗanda basusan abinda ya faruba sunata mamakin canjawarta…………✍????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button