Lu’u Lu’u 6

*6*
Fitowarsa tayi daidai da k’arasowar su Zafreen zasu je b’angaren su Ayam dan ganawa da wata k’awarsu, zasu wuce shi ma zai wuce kawai Zafreen ta k’ura masa ido, baki da hanci ta saki tana binshi da kallo, cike da birgewa ta juya saboda har yayi gaba ba tare da sanin me take ba tace “Wow! Amma malamin nan ya had’u.”
Laika ce tayi saurin kallonta tace “Gimbiya Zafreen, kina nufin ya birgeki ne?”
Juyawa tayi ta kalli Laika tace “Sosai ma, idan har zan iya yin aure to shi ne mijina.”
Murmushi ta saki ta kalli k’wayar idon Laika tace “Ina zuwa.”
Kafin Laika tayi wata magana har Zafreen ta tafi da sauri tana fad’in “Malam, malam ji mana.”
Tabbatarwa da yayi da shi ake yasa shi dakatawa ya juya, a tsanake ya shiga k’are mata kallo, tabbas kyakyawa ce data amsa sunan kyakyawa, komai na ta yayi kuma y had’u, bata da makusar da duk namiji mai son more rayuwa ba zai so samunta ba.
Kayan jikinta sun nuna mishi a wani b’angaren take nata karatun, ga kuma wani yankakkan gashi dake kan ta mai kalar ruwan d’orowa wanda haka kalar idonta ma suke.
Iya fatar jikinta ta nuna masa ita ma yar hutu, ko ‘yar hamshak’in mai kud’i, ko ‘yar mai iko ko kuma sarauta, tana k’arasowa ya sake gyara tsayuwarsa.
Saida ta zo daf da shi sai kuma sai ta ji wani kwarjininshi ya kamata, kanta sadde a k’asa ta shiga doka murmushi, cikin sanyayyar murya tace “Malam barka.”
Fuskar nan a had’e ya amsa da “Uhum.”
Duburburcewa tayi ta shiga rausayawa kamar zata taka rawa, kame-kame ta fara tace “Am.. Dama dai… Ni sunana Zafreen Musail, gimbiya Zafreen Musail.”
Tsura mata ido, da fari dai ya d’auka mai hankali da ilimi ce, ashe ba haka bane. In banda abinda me ye abun birgewa a cikin nuna kai waye kai tsaye? Saidai yayi farin ciki da haka, dan tabbas idan bai samu ‘yar uwar ta Zafeera ba, to kan ta zai *d’auki fansa*, dama ya fi son d’aukar fansar ne ta hanyar Zafeera saboda ita yaga an fi cin buri a kan ta, amma wannan ma zai iya maleji da ita madadin yayi biyu-babu.
Wani d’an siririn murmushin mugunta ya sakar mata a dak’ile yace “Barka princezna, haka kuke fad’a a yarenku na slovaque ko?”
K’ara washe baki tayi kamar zata fad’a masa tace “E yallab’ai, ka iya yarenmu kenan?”
Shu’umin kallo ya mata yace “E, yanayi ne yasa na iya.”
Sake fad’ad’a murmushi tayi tace “Am…Yallab’ai, zan iya rok’on wata alfarma?”
Da ido ya mata alamar “Ina jinki.”
Mamaki ne ya kamata ganin wannan ma yana neman ya fi ta shan k’amshi, basarwa kawai tayi tace “Zamu iya zama abokai?”
Yatsina fuska yayi kamar ya ga abun k’yama yace “Hakan ai ya sab’awa dokar kowace makaranta.”
Tab’e baki tayi tace “Karka damu yallab’ai, indai ka amince wannan ba matsala bane, mahaifina shi ne sarkin Khazira, duk wata masarauta a k’asar nan a k’ark’ashin ta mu masarautar take, dan haka zan iya yin komai da nake so.”
Sake b’ata rai yayi yana mai jin wani takaici fiye ma da wanda ya ji yayin had’uwarshi da waccen tamatsirin, dan gaba d’aya wannan magana take ta alfahari da d’agawa wacce babu tunani a cikinta.
Girgiza kai yayi ya d’an juya zai bar mata gurin, da sauri tace “Yallab’ai ya haka kuma? Baka ban amsa ba.”
Juyowa yayi a kasalance ya kalleta, lumshe ido yayi yace mata “Kiyi hak’uri.”
Juyawa ya sake yi yai tafiyarshi ya bar ta nan tsaye, haushi ne ya kamata ganin yanda ya cizgata a gaban mutane, fuska a kumbure ta juyo ita ma rai b’ace ta nufi wajen su Laika dake tsaye suna kallon komai daya faru.
Tana isowa ganin yanda take cika tana batsewa yasa a cikinsu babu wacce ta tambayeta lafiya? Dan zata iya juyewa a kan su, a tsiyace take tafiyar kamar zata tashi sama inda suma suke biyarta a haka.
Daf da bakin k’ofar shiga su Ayam su kuma zasu fita rakata kiran Momma, a rashin sani Sabrine da Zafreen suka bangaji juna, da k’arfi Sabrine tace “Aouch!”
Zafreen kuma a mugun tsawace tace “Ke!”
Kafin kuma kowa ya ankara Zafreen ta kwad’awa Sabrine wani wawan mari, ihun da tayi a firgice yasa Ayam waro ido ta sauke akan Zafreen d’in, a karo na biyu Zafreen ta sake d’aga hanu zata mari Sabine tana fad’in “Ke har wace…”
Cak maganar ta tsaya mata, dan bata san lokacin da Ayam ta rik’e hannun na ta ba kuma har da nasarar marinta a fuska.
Dafe kuncinta tayi tana kallon Ayam dake dafe da kafad’ar Sabrine tana fad’in “Kiyi hak’uri kinji, ke ma ai kina da gata.”
Kamata tayi zasu wuce ka rantse da Allah bata san me tayi ba, duk k’awayen kuma sun yi mutuwar tsaye saboda ganin girman lamarin, musamman ma Laika ta fi kowa tsorata, a sukwane Zafreen ta shak’i wuyan rigarta cike da masifa tana fad’in “Ke kin…”
Yanda Ayam d’in ta zuba mata ido ta kalleta sai abun ya gigita Zafreen, yanda idonta masu launin nan mai ban tsoro suka samu sirkin launin ja na b’acin rai, sai kawai ta ji gabanta yayi wata mummunar fad’uwa, kamar wacce mai fad’a a ji ya bata umarni sai ta shiga zame hannunta a jikin rigar Ayam d’in, hakan ya ba su Ayam d’in damar k’arasa ficewa a wurin.
Da kallo suka bisu har da ita Zafreen d’in data sake dafe kunci tana murzawa a hankali, ta ji zafi sosai na marin nan, yau ma sai suka fasa shiga kamar dai jiya suka juya da sauri suka bi bayan Zafreen dake tafiya har da gudu gudu.
*Shigarsa* ke da wuya d’akinshi ya bud’e taga kenan ya hangi Zafreen zata mari Sabine a karo na biyu Ayam ta rik’e hannun kuma ta mareta, duk da b’angaren malamai da b’angaren su Ayam d’in ba wai yana kallon juna bane, kamar kusan a jere ma suke saidai akwai ginin babban ofishi a tsakaninsu (zauran malamai).
Yanda ya ga wannan abu da tuna had’uwarshi da Zafreen d’in sai ya ji gabanshi ya fad’i, a yanayin da bai saba da shi ba ma’ana tsoro yace ” Wai *wacece ita*?”
D’ora hannunshi yyi a kai yace “Tsarki ya tabbata ga Allah.” Maganar gaskiya ko shi da ke namiji ba zai iya marin Zafreen ba, dan tana da kwarjini da izza wacce kana gani kasan ta samo asali ne daga gidan sarauta, musamman ma ita da mahaifiyarta Juman ‘ya ce ga sarkin Egypt (Ya akayi ka sani? 馃), sannan mahaifinta ma sarki d’an sarki kuma jikan sarki.
*Ayam* kam suna fita Deeyam a mugun tsorace ta rik’o hannun Ayam tace “Ayam kinsan me kika aikata kuwa? Ita ce fa naji ana rad’e-rad’in gimbiya ce.”
Saida ya zage hannunta daga na Deeyam tana karbar wayar da mai kula dasu ya mik’o mata ta d’ora a kunne tace “Then.”
Da mad’aukakin mamaki Deeyam tace “Ayam ba wasa nake ba fa, gaskiya nake fad’a miki.”
Cikin muryar kuka Sabrine da marin ya gama gigitata tace “Gaskiya Ayam da baki mareta a kai na ba, zaki iya shiga matsala.”
Ko kulasu ba tayi ba sai ma saka lambobi da tayi suka ji tace “Yes Momma na, barka.”
Jim tayi alamar tana saurare daga gurinta kafin tace “Momma ina Pah?”
Kyab’e fiska tayi tace “To gaskiya ni dai ki fad’a masa ba zan hak’ura sai ya zo gobe ya kawo min kyautar k’ara shekarata.”
Yanda Momma ta amsa mata yasa Ayam yin jim, sau da dama tana mamakin wasu abubuwa da iyayen na ta ke yi mata, da zaran zata fara tunanin haka kuma sai suyi gaggawar katseta, yanzun ma dai yanda ta bata amsa da dole ma ya amsa kiran sarauniyarshi ba shi ya d’auki hankalinta ba kamar yanda ta ji k’amshin gaskiya da kuma b’ari na tsoro a muryarta.
A daddafe ba tare da karsashin da suka fara magana ba ta yanke kiran ta aje wayar, dafe gaban goshinta tayi zata tsunduma tunanin me hakan ke nufi ? Kawai Deeyam data damu sosai cikin d’aga murya tace “Ayam, hanklinmu a tashe amma ke waya ma kik…”