Lu’u Lu’u 6

Wani bahagon kallo Ayam ta mata tare da nunata da yatsa manuniya, cikin sanyayyar murya kuma a tausashe tace “Karki sake d’aga min murya, ni ba ‘yarki bace.”
Jakarta ta d’auka wacce ta aje akan tebur d’in da wayar tangarahon ke kai, ko rataya ta batayi a bayanta ba ta juya a sukwane ita ma ta bar wurin a dole suka bi bayanta cike da zulumi da jinjina isa irin ta Ayam.
*Egypt*
Cikin girmamawa yaron na shi ya kalleshi cikin d’ard’ar d’in ta yanda zai karb’i abinda ya zo masa da shi yace “Shugaba na, sak’o ne daga Giobarh daga sarki Wudar, ka min izinin karanta maka abinda takardar ta k’unsa?”
Duk da ya ji shi sarai amma ka rantse bai ji me yace ba, ci gaba yayi da wasarshi da wani k’aramin k’wallo na kwalba mai kamar *Dutsen Diamond*, matar dake zaune gefenshi cikin fararen kaya na yadi da kambunta a kai mai kalar gwal ce ta kalleshi a tausashe tace ” *Bukhatir*, ka saurari abinda ya zo maka dashi mana, ka lamunce masa ya karanta maka me takardar tak’unsa, daga sarkin Giobarh fa sak’on ya zo.”
Ita ma banza ya mata sai ma ‘yar wak’ar daya shiga rerawa yana fad’in “Lu’u lu’u ki dawo gareni, lu’u lu’u ki dawo gareni, idan babu ke a rayuwata, ji nake kamar ma na mutu.”
A mugum hassale matar ta mik’e tana daka tsawa da fad’in “Ina! Ba zai yiwu ba, Bukhatir ka fara wuce gona da iri fa, wannan wace irin rayuwa ce ? Me kake neman ka mayar da kan ka ne ? Lu’u lu’un banza da…”
Tassssss! Ya d’auke fuskarta da mari, tuni bafaden dake tsaye ya rintse ido dan yasan dama haka zai faru, shi yasan yanda Bukhatir ke masifar son wannan lu’u lu’u, dan haka shi ma yake kaffa-kaffa indai abinda ya shafeta ne.
Tunda ta sunkuya ta dafe kunci kasa d’agowa tayi, a nutse kuma a ikonce tsabar yana ji da kansa da burin mallakar masarautar Egypt ya nunata da yatsa ya mata alamar ta fita a nan, d’auke hannunta tayi daga kunci ta kalleshi da ido sun mata jajir, cikin shashek’a tace “Ni ka mara saboda na zagi wata ban…”
Tauuuuu! Ya sake d’auketa da wani marin kuma, yanzu kam a hassale kuma a gigice cikin d’aga murya yace “Ki b’ace min da gani *Zeyfi*, kuma kar ki sake gigin tab’a kimar lu’u lu’uta, idan kuma kika sake to a bakin aurenki.”
Zaro ido tayi baki bud’e, ai da gudu ta fita a d’akin rigarta na jan k’asa, saida ya ga ficewarta yaja wawan tsaki, kallon bafaden yayi yace” Me ye? Me yace? ”
Jiki na kakkarwa ya shiga warware takardar, saida ya bud’e ya fara karantawa kamar haka _” Mai girma Bukhatir, wannan takardar d’amba ce ta neman sulhu tsakanina da kai, bisa tabbatarwa da mukayi mu da kai abu d’aya muke nema, zai fi idan muka had’a k’arfi da k’arfe wajen cimma burinmu, dukanmu manufa d’aya garemu a kanta, manufar kuwa ita ce *d’aukar fansa* ga sarki Musail, zanyi farin ciki idan ka had’a hannu da ni, hakan kuma zai zama k’aruwarka, idan ka amince da buk’atata ka turo min da sak’on gayyata zuwa fadarka, sak’o daga sarki Wudar.”_
Zaune yayi ya tsunduma tunani, ya d’an jima haka kafin ya kalli bafaden yace “Me kake tunani game da hakan?”
Cikin ladabi yace “Shugaba, a gani na wannan wata dama ce ta cimma abinda muka jima muna nema, duk da abu d’aya muke nema da su, amma ba kamar yanda sarki Wudar yake tunanin manufar d’aya bace.”
Jinjina kai Bukhatir yayi yace “Gaskiya ne, idan har muka had’a hannu da shi muka sameta, a dalilinta zan hau k’aragar mulkin kakan Zafeera ma’ana mahaifin mahaifiyarta Juman, idan haka ta kasance kuwa zan zama mai sa’a a doron duniya.”
Jinjina kai bafaden yayi tare da fd’in “Hakane shugaba na.”
Wani k’ataccen murmushi ya saki ya gyara zamanshi k’afa d’aya kan d’aya yana wasa da yatsunshi yace “Tun ina k’arami nake son hawa kujerar mulkin nan, saidai sarautar a hannun yayan mahaifina take, hakan yasa shi ke mulkar gaba d’aya k’asar nan, hatta da mahaifina da suka fito ciki d’aya shi ma duk’ar da kai yake a gabansa, sannu sannu sai na fara karkata hankali na kan ‘yarsa k’waya d’aya tak, murmushin da take min na d’auka na so, ashe ita tana can tana soyayyarta da wani ba ni ba, hummmm! To me ya kamata na yi? Sai na zauna na zama d’an kallo kenan?”
Wani malalacin murmushi yayi tare da girgiza kan shi sannan ya mik’e ha shige uwar d’aka yana fad’in” Ka tura masa da takardar gayyata.”
Sunkuyawa yayi alamar amsawa sannan ya fice zuciyarshi cike da farin ciki dan bai yi tsammanin zai amince ba.
*Masarautar Khazira*
Zaune suke akan babban teburin cin abinci kamar na bak’i, suna had’a ido ya sakar mata murmushi yace” Sarauniyata.”
Had’e fuska tayi ta kawar da kan ta, murmushin gefen labb’a yayi yana kallon farantin gabanshi da babu komai a ciki yace” Kina hushi dani saboda na fad’a miki ni na kashe mijin da da zai aureki, to me yasa kike tunanin zan k’yaleshi? Ba rabonsa bace ke, ki manta kawai.”
Girgiza kai tayi cike da takaici tace” Baka da tausayi Musail, bayan shi mutane nawa ka kashe? Yanzu ma gashi saboda son zuciyarka ‘yata data rage min ina kallo ina jin dad’i, ka turata neman wata wacce ba zata tab’a samunta ba har abada.”
Cikin d’aga murya tace” Idan ta mutu ita ma sai na yi me kenan?”
D’aga kai yayi ya kalleta a sanyaye yace” To sai me? Ni ba mijinki bane? Ai zan iya sake baki wasu ‘ya’yan idan kina so.”
A hassale ta mik’e tsaye tace” Tirrr! Har abada ba zan bari ka sake rab’ar jikina ba, kuma ka sani burinka akan y’ata ba zai tab’a cika ba.”
Da mamaki ya kalleta yace” Me kike nufi Juman?”
Cike da gadara tace” Ina nufin yata da kuka yi yunk’urin kashewa kai da Dhurani, na san komai da kuka shirya a kan ta, ba zaku tab’a nasara ba ka ji da kyau.”
Tsaye ya mik’e yana mata wani kallo yace” Juman, ko dai ke kika tseratar da yarki?”
Ba tare da tsoro ba tace” K’warai, ni na kub’utar da ita, ka samota mana idan ka isa.”
Juyawa tayi zata bar gurin ya daka mata wata irin tsawa yace” Jumaaaaaaann.”
Dakatawa tayi ta juyo tana kallonshi, a sukwane ya nufota da babbar rigarshi, kallonshi ta dinga yi har saida ya zo kan ta, bai tsaya komai ba ya gaura mata mari, kafin ta ankara ya shak’i wuyanta da hannu d’aya, duk da shi ya shak’eta amma kuma idonshi sun bala’in yin jajir dasu duk sun fito tsabar takaici da b’acin rai, cikin fitar hayyaci ba tare da duba yanda take d’aukar numfashi ba kamar zata mutu yace “Sai na kasheki, sai na kashe ki Juman, ba zaki tab’a zama silar gurguncewar rayuwata ba kuma na k’yaleki.”
Hadimai biyun da suka taho da kwanukan abinci ne suka tsorata ganin wannan lamari, juyawa sukayi zasu fita inda babban bafaden sarki Musail *Adah* yayo kansu da gudu, hannayen sarkin ya rik’e yana bashi baki da yayi hak’uri ya sakeg’ta zata mutu.
Hadiman da suka fita ne suka had’e da waziri Khatar zai shigo ciki shi ma, ai a tare suka sake dawowa da hanzari bayan sun fad’a masa, yana zuwa shi ma kamawa yayi suka shiga k’ok’arin b’amb’areta, da k’yar sukayi nasarar k’watarta a hannunshi duk ta galabaita dan k’iris ya rage ta suma, cikin hargagi sarki Musail yake nunata da hannu yana fad’in “Ba soyayyar da kika tabbatar ina miki fiye da komai bace ta sa kika min haka ? Ai dai tak’amarki ina sonki dan haka babu abinda zai faru ko? To ki ji da kyau Juman sai na hukuntaki, ke baki san waye ni ba shiyasa, amma da sannu zaki sani tunda kika tab’oni, kuma bak’ar ‘yarki zan kamota abisa taimakawar bayina, a gaban idonki zan yanka wuyanta, dan ba zan bari yar dana haifa ba ta kasheni sannan ta rabani da mulkina ba.”