Lu’u Lu’u 7

Shi ma tashi yayi tsaye yana sauke numfashi yace “Amma ta ya kake isar mata da sak’on?”

Ajiyar zuciya mutumin ya sauke kafin yace “Kana neman k’ureni ka sa na karya alk’awarin dana d’auka.”

Cikin rarrashi Haman yace “Kai kanka nasan za kayi farin ciki a ce yau farin cikin sarauniyarka ya dawo ta dalilinka, gimbiya Zafeera yarinya ce da muka fuskanci girman lamarinta, dalilin hakan rayuwarta ta shiga cikin had’ari mai girman gaske, muna son sani wani abu a kan ta dan bata kariya ne daga masu son cutar da ita.”

Jim yayi yana kallon Haman na tsawon dak’ik’u, muskutawa yayi yace” Na yarda da kai yallab’ai, ba dan komai ba sai dan abinda ka fad’a gaskiya ne cewa rayuwar gimbiya Zafeera na cikin had’ari.”

Numfashi ya sauke kafin yace” Zaka samu cikakkun bayanai inda suke a wajen wata tsohuwa dake k’auyen Larhjadin. ”

Cike da zumudi Haman yace” Me ye sunan tsohuwar? A wane gari ne?”

A nutse yace” Ruman, k’auyen *Tankara*.” (Mai Dambu ta mu ina godiya da wannan kyautar, Allah bar zumunci)

Hannu ya mik’a masa cike da jin dad’i yace “Nagode sosai,na ji dad’in had’uwa da kai.”

Jinjina kai yayi shi ma yace “Ni ma haka, fatan nasara.”

Murmushi yayi sannan suka saki hannun juna ya fita a lambun gaba d’aya, a hanyarshi ta zuwa k’auyen Tankara ya kira lambar Umad, dan yayi niyya yau zuwa gobe sai ya samo bakin zaren nan, dan sun jima suna doguwar tafiya saboda yarinyar nan, abinda ya fi basu wahala kuwa shi ne kafin su samu wanda zai iya basu bayanai a kan ta, da k’yar suka samu wata baiwa da sarki Musail ya ma ciki, amma saiya koreta saboda a lokacin yana cikin tashin hankalin neman Zafeera, ita kuma haushin yanda ya koreta bai sakata a layin k’wark’wararsa ba ma bare ta zama matarsa yasa ta fad’a musu bafaden da taji suna wani yare da su Habbee.

*Umad* na tsaka da jinjina k’arfin halin Ayam na marin da ta wa Zafreen ya ji k’arar wayarsa, da sauri ya d’aga ya d’ora a kunne amma bai ce komai ba, Haman da yasan komai ne ya fara fad’in “Kana ji?”

“Umm.” Ya fad’a a k’asan mak’oshi, d’orawa da “Na samu mutumin nan Umad, ya ban adreshin d’aya mutumin kuma na sameshi.”

A zabure ya tashi tsaye yace “To ya kukayi? Me ya ce?”

A tsanake yace “Ya fad’a min komai, yanzu haka zan je k’auyen Tankara ne.”

Da mamaki Umad yace “Tankara kuma?”

“E.” Ya fad’a kai tsaye, da alamar tambaya yace “To amma me yasa?”

Kamar yan1 gabanshi ya shiga girgiza kai yana fad’in “Umad lamarin nan fa ya wuce yanda kake tunaninshi, wai ma kasan da sarauniya Juman ita ce ta sa aka d’auke yarinyar dan ta kub’utar da ita?”

Da mad’aukakin mamaki Umad ya shiga zagayen d’akin hannunshi akan k’ugunshi yace “Idan na fahimceka sarauniya Juman ita ta umarci jakadiyarta Habbee da mijinta da su gudu da yarinyar, haka kake nufi?”

Jinjina kai yayi yace “Tabbas kuwa hakane.”

Wani shak’iyin murmushi Umad yayi sannan yace “Hummm! Sannu sannu dai, komai ya kusa fitowa fili.”

Zura hannunshi yayi aljihu yana takawa a hankali yace “Shikenan Haman, ka ci gaba da bincika mana komai a tsanake, Allah ya kiyaye ka.”

Murmushi yayi yace “Nagode, sai na kiraka.” Lumshe matsakaitan idonshi yayi alamar to kamar suna kallon juna.

*Khazira*

Hankali tashe babban malamin ya iso fada, sai ga sarki Musail na ta kewayar d’akin ya cire babbar rigarshi ya aje sai zufa yake, cikin tsawa da hargagi ya kalli malamin yace “Babban malami ta ci amanata, Juman ta ha’ince ni, shin soyayyar dana nuna mata ce ta gagara? Ko kuma butulci ne irin na mace?”

Jim ya d’anyi kamar zai ba wani damar fad’an wani abu, sai kuma yay saurin fad’in “Yanzu me ye abun yi baban malami? Ya zanyi na samota ta dawo gareni? Ina so na kamata da hannaye na, Dhurani bana so na mutu yanzu.”

Ya k’arashe maganar yana d’aga murya, cikin rarraba ido Dhurani yace “Sarki na, wannan ai abu ne mai sauk’i, mu takura gimbiyar mu har sai ta fad’a mana.”

Khatar ne yayi saurin fad’in “Da zata fad’a ai da ta fad’a, shekaru ashrin fa muka d’auka muna bilinbituwar nemanta, a gaban idonta muke yi da me ta tab’a taimaka mana?”

Sarkin yak’i Adah ne ya d’an jinjina kai duk da ba’a buk’ace shi ba yace “Gaskiya ne, amma ko bata fad’a da bakinta ba mu zamu nemota.”

Kallonshi sarki Musail yayi yace “Adah bana son wasa, wane irin nema ne baku mata ba ? Tun kana da k’ruciya kake yawon nemanta, sai yanzu ne zaka ganta?”

Sunkuyar da kai yayi yace “Sarki na, sa’ilin da zamu kai sarauniya kurkukun sabah sun yi wani yare ita da d’aya daga cikin bayinka, bana tamtama cewa maganar da sukayi ta shafi gimbiya Zafeera.”

Da saurin bala’i sarki Musail ya tunkareshi yace “Wanene shi? Me suka tattauna?”

Girgiza kai yayi yace “Ban sani ba ya shugabana, dan kafin ta masa magana saida ta canza harshe.”

A bala’in tsawace yace “Waye shi a gidan nan, je ka kawo min shi nan.”

Sunkuyawa yayi alamar amsawa sannan ya juya cikin takon k’arfi yaf fita a falon, bai d’auki lokaci ba ya dawo waccen bafaden na bayanshi, gefe sarki yak’i Adah ya tsaya shi kuma ya zube har k’asa yana gaishesu, saidai a zahirinshi da bad’ini hankalinsa a tashe yake, ba ka da abun zargi ma ka ji tsoron amsa kiran sarki Musail bare kuma shi da yake ji a jikinshi asirinsa ne ya tonu.

Cikin daka tsawa sarkin yak’i Adah yace “Kai k’ask’antaccen bawa, sarki yana so ya ji abinda kuka tattauna tsakaninka da sarauniya Juman?”

D’aga kai yayi ya kali sarkin yak’i jikinshi na makyarkyata, kame-kame ya fara ya rasa me zai ce da shi, a sukwane sarki Musail yayi kan shi, kafin ka ce me ya saka k’afa ya hankad’ashi ya fadi kwance, kafin ya tashi yasa k’afar ya take masa k’irji, cikin k’araji yana zazzaro ido yace “Zaka fad’a min ko sai na kasheka a banza? Ka sani duk wanda yace zai shiga tsakani na da cikar burina kamar wanda zai taimakawa mak’iyana kyautar takobi ne dan yak’ata, dan haka ba zan bar shi a raye ba, yanzu fad’a min me ta fad’a maka?”

Cikin tashin hankali da tsananin tsoro yace” Sarki na, shugaba na ka min rai karka kasheni, ta ce ko ta halin yaya na isar da sak’onta, na fad’a mata ta ninka saka ido akan gimbiya.”

A tsawace ya sake fad’in” Wacece? Kuma a ina take?”

Cikin rawar jiki yace” Wata tsohuwa ce, a k’auyen Tankara.”

“Me sunanta?” Dhurani ya tambaya daga gefenshi, cikin rawar leb’e yace “Ruman, Ruman ne.”

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button