Lu’u Lu’u 7

K’atuwar takobin dake k’ugun sarkin yak’i Adah ya jawo, kafin kowa ya ankara kawai ya sokawa bafaden nan ita a tsakiyar ak’ogwaronsa ta hudashi zuwa wuya, wani huci ya shiga saukewa ya mik’awa Adah wuk’ar yana fad’in “Duk wanda ya yi k’ok’arin hanani kasheta to shi ma kasheshi zan yi, sarkin yak’i.”

Da sauri Adah ya amsa yana rusunawa, juya baya yayi yace “Ka d’ebi wasu daga cikin mayak’anka ku nufi Tankara, idan tana nan ku taho da ita, idan kuma hakan ya gagara ku sanar da ni, ni zan je har inda take sannan na kasheta da hannu na.”

Amsawa yayi da “Angama Ranka shi dad’e.” Kafin ya kama hannayen gawar nan ya jashi k’iiiii har ya fice da shi a falon.

*Larhjadin*

Ba wani yammaci bane sosai, amma dake makarantar akwai wadatar shuke shuke sai tayi luf sai iska mai sanyi dake kad’awa, duka d’aliban mata suna tsatsaye bakin mota inda dreban ke jiransu, suna cikin shiga ta kakin ma’aikatan gandun daji, riga da wando kalar shud’i da babu kwalliya, saidai daga yanayin d’inkin da wasu ado da akayi ga rigar zai shaida maka masu tsaron k’asarsu ne, bak’ak’en huluna ne a kan su sun daidaita musu zama cikin k’warewa, ga kuma takalminsu bak’ak’e k’afa ciki sai k’yalli suke sun d’auresu tamau da d’amara.

Gyara tsayuwarta tayi tana murgud’a baki tace “Wai malamin nan bai san lokutan karatu dana hutu bane? Ya zai shanya mu a nan?”

Sergent d’in colonel ne ya tsaya gabansu cikin d’aga murya yace “Ayam Utais, yallab’ai canal (colonel) na san ganinki yanzu a ofishinshi.”

Waina idonta tayi ta kalli Deeyam da ita ma ke kallonta tace “Wai ni sai yaushe ne canal d’in nan zai barni na huta?”

Murmushi Deeyam tayi tana rik’e d’amarar k’ugunta a hannu tace “Ranar da ke ma kika barshi ya huta, ba ke kullum ‘yar masifa ba ce.”

Turo baki tayi gaba alamar rashin jin dad’i sannan ta nufi hanyar tafiya tana fad’in “Sai na je kuma yayi ta sadda kai k’asa kamar ya ga gyatumarshi.”

Yanda aka mata d’inkin daidai da zubin hallitarta yasa kayan suka karb’eta da kyau, duk da bata da wasu mazaunai na a zo a gani, amma dake ta d’aure da zanzaro sai hakan ya basu damar juyawa.

Motocin data gani da suka amsa sunansu masu bala’in kyau da kuma shek’i yasa ta k’ura musu ido a ranta ta ayyana “Ko dai bak’i a ka yi?”

Suna kai wa bakin ofishin ya ja ya tsaya ya nuna matata shiga, kallon shi tayi t tab’e baki sannan ta kama hannun k’ofar ta murd’a, k’afa d’aya ta fara zurawa ta shiga a matuk’ar nutsuwa da kuma wani irin kwarjini da izza, tana k’arasa shiga kamar dai mutanen ciki ita ma sai ta zuba idonta tana k’are musu kallo.

Canal dake kujerarshi ya had’e hannaye wuri d’aya sai rarraba ido yake, amma tana shigowa ya mayar da hannayenshi k’asan teburin ya koma kallon takardun gabanshi kamar wanda ya ga aljana. Waziri Khatar kuma na kujerar dake fuskantar ta canal d’in fuskarshi a matuk’ar had’e yanda zta gigita mai kallonta, ga shigar da yayi ta alfarma ita kad’ai zata sa ka rusuna mishi ka d’auka sarkin ne da kanshi.

Sai Zafreen dake tsaye bayan wazirin ta rumgume hannayenta ta k’urawa Aya d’in ido. Sai kuma wanda zata iya cewa shi bata san me ya kawoshi nan ba, dan in wannan yana zaune ne saboda marin da ta wa Zafreen, to shi kuma fa? Yallab’ai Umad kenan, gashi dai cikin kakinshi a shirye tsaf, amma kuma ya barsu suna jiranshi har yanzu gashi za’a zo a nemi b’ata mata rai.

Yanda ta tsaya gaban tebur d’in yasa canal d’aga kai ya kalleta, suna had’a ido kawai sai ya ga kamar hararanshi ma take, da sauri ya mayar da kanshi ga d’aya daga cikin fadawa biyun da Khatar ya shigo da su yace “Rufe k’ofa.”

A ladabce bafaden ya rufe k’ofar a lokacin ta juya ta kallesu sannan kuma tasan da zamansu, maida kallonta tayi ga canal d’in tace “Yallab’ai ka ce kana son gani na.”

D’aga kai yayi ya kalli fuskarta, amma abinda Umad dake zaune yana tsare kowa da ido ya lura da shi shine yanda yake ta yawo da idon na shi ya kasa tsayar dasu a kan fuskarta bare ya kalli idonta, hakan yasa shi dasa alamar tambaya aka wannan lamari.

Cikin taushin murya yace “Ayam, me ye dalilin da yasa kika mari gimbiya Zafreen? Shin ban fad’a miki ki fita a sabgarta ba?”

Gyara tsayuwarta tayi ta juya ta kalli Zafreen d’in, sai kuma ta kalli waziri daya cika fam yana jiran fashewa, tab’e baki tayi ta kalli canal tace “Tun ranar ai na fita a harkarta, ita ce ta sake shiga hurumi na.”

Wata irin tsawa ya daka mata tare da buga tebur din ya mik’e tsaye yana fad’in “Ke d’in banza, wacece ke da zaki ja da ita? Kinsan matsayinta a makarantar nan kuwa? To ko yanzu ta so z…”

A hassale ta kalleshi gaba da gaba ta zazzaro idon ta wanda launin shud’i yayi wani kore-kore ga mai kallonsu, cikin tsiwa da fad’a tace “Waye kai da zaka min tsawa? Uba na ne kai ? Na sanka ne? Ka zo d’aukar mata fansa ne? To ina jira kayi yanda zakayi da ni.”

Sake k’ura masa ido tayi ta nunashi da yatsa manuniya tace “Malam murya k’asa, ni ba kowa bace amma haka kawai nake jin na tsani a d’aga min murya, kuma a jinina nake jin kamar ina da izzar da zan hukunta duk wanda ya min hakan cikin d’anyan kai.”

Juyawa tayi ga canal, tuni ya gyara zamanshi yana ta k’yak’yabta ido, tabbas da yana da addinin musulunci a lokacin daya shiga karanto addu’ar tsari da shed’anu, sam bai yarda da Ayam dan lamarinta tsoro yake bashi, shi fa babu kamar ma yanda jikinshi ke d’aukar b’ari idan ya hangeta kawai, har ya kan tambayi kan shi k’awayenta da sauran mutane basa jin hakane ? Sai kuma ya ba kanshi amsa watak’ila dan sun saba da ita ne shiyasa, dan sun fad’a mishi tun suna yara suke tare tun a makarantar *Ansawwd* (ma’ana *inganci*).

A sanyaye kamar ba ita ba tayi kalar tausayi tace “Canal yarinyar nan fa marin k’awata tayi, kuma ka sani kai ma bana son a tab’a min k’awayena, to me yasa zan k’yaleta?”

Cikin sub’utar baki yace “Gaskiya ne, na sani Ayam, yanzu kiyi hak’uri ki je na jiranki zaku tafi jeji.”

Wani k’ayataccen murmushi ta saki tace “Shukran.”

Sakin baki yayi a ranshi yace “Yau ma wani yaren?”

Juyawa tayi cikin takon k’arfi da salo ta fita a ofishin babu wanda yayi yunk’urin hanata, Umad dake zaune mik’ewa yayi ya sarawa canal d’in sannan yace “Yallab’ai da izininka zan tafi.”

Da hannu ya nuna masa k’ofa alamar ya tafi d’aya hannunshi kuma na share gumi da yayi, saida Umad ya fita Zafreen ta girgiza kan ta ta dawo hayyacinta, rarako idonta tayi tace “Kutumar can, wacece ita?”

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button