Lu’u Lu’u 8

*8*

Cikin yaren Italy tace “E tu? Il figlio verde o uno dei loro cortigiani (kai kuma fa? D’an korensu ko d’aya daga cikin fadawansu?”

Zaro ido yayi a tsawace cikin b’acin rai yace “Silenzio! Omicidio cosa ci dirai, pazzo (shiru ! Ki dinga sanin me zaki fad’a mana, mahaukaciya).”

Cike da shak’ihanci ta gyra tsayuwa tace “Kai ma ka dinga sanin sunan da zaki dinga kirana dashi malam.”

Girgiza kai yayi irin na takaicin nan yace “Nonsense (shashanci).”

Murmushi tayi tace “I’m not talking about nonsense, I’m telling you so i can do what you don’t expect (ba ina magana bane akan shashashanci, ina fada ne dan zan iya yin abinda baka tsammani).”

Da mad’aukakin mamaki yace “How do you change language like this? Who are you (ta ya kike iya canza yare haka? Wacece ke)?”

Sunkuyar da kan ta tayi tana murmushi tace “Tu me prend juste comme tu me vois, je ne sais m锚me pas, c’est juste moi (Ka d’auke ni a yanda ka ganni kawai, ni kai na ban sani ba, ni ce kawai).”

Juyawa tayi a sanyaye zata tafi ya bita da kallo, gyara tsayuwa yayi har ga Allah jiri yake ji na son kwasarshi ya jefar a k’asa, yarinya kamar aljana ko wata matsafiya, da sauri ya girgiza kan shi ya kawar da abinda zuciyarshi ke sak’a mishi a kan ta, takawa ya shiga yi da k’arfi k’arfi har ya isa garesu inda suke tsatsaye.

Ganinshi ya taho yasa d’aliban duk suka dinga shiga cikin motar wasu ta k’ofar gaba wasu ta baya, Ayam ma na daf da shiga ta ji an ce “Gimbiya ta.”

Da farin ciki ta kalli inda ta ji sautin kuma ta gane sautin waye, da gudu ta sauko a matakalar ta nufeshi tana fad’in “Pah.”

Tana zuwa ta bud’e hannaye zata fad’a jikinshi kawai ya rusuna kamar yayi ruku’i, hakan ya k’ara saka Umad ghara tsayuwarshi yana kallonsu.

Marairaicewa tayi ta turo baki tace “Pahhh? Me yasa?”

D’agowa yayi yana dariya yace “Tuba nake, ai ba laifi nayi ba dan na kira gimbiya ta da gimbiya.”

K’arasawa tayi ta bud’e hannayenta ta rumgume shi tsam tana sauke ajiyar zuciya, bai yarda ya rik’e jikinta ba, dan wanda tayi ma suna d’aukan hakan wata alfarma ce garesu, su suka raini yarinyar tun tana k’arama, sun sha al’ajabi da mamaki a game da abinda ya shafeta, har wasu lokuta sukan shiga yanayi na tsoro da fargaban ko dai ba mutum bace, lallai sun yarda rashinta a msarautar nan shi ne yafi alkairi.

Hannunshi dake b’oye a bayanshi ya fito da shi cikin murmushi yace “Gimbiya ga kyautar ki.”

D’agowa tayi ta kalleshi tasa hannu biyu ta karb’a tana dariya tace “Amma Pah ai gobe ne ranar, me yasa ka kawo min kyauta yau?”

Da fara’a a fuskarshi yace “Maman ki ta fad’a min kin je bana nan, kuma kin kira kika tambaye ni, shiyasa na kawo kai na kafin ki sake nema na.”

Fad’ad’a murmushinta tayita sake rumgume shi tace “Thank you Pah, I’m so proud of you.”

Kallonta yayi a ladabce yace “Na sha fad’a miki bana gane kowane yare bayan na slovaque da azharbaijan, ban fahimci me kika fad’a ba.”

Had’e murmushinta tayi tace “Pah, dama ina so na tambaye ka, wai me yasa sai na dinga yin yaren da ni kaina ban sani ba? Na lura hakan ya fara tsorata mutane game da ni.”

Girgiza kai yayi yace ” Ban sani ba, bansan komai akan haka ba, ina ga baiwarki ce haka.”

Cike da gamsuwa ta saki fuskarta tace” Pah, ce wa nayi nagode sosai, kuma ina matuk’ar alfahari da kai.”

Kan shi ya rusuna dake nuna ya ji dad’in abinda ta fad’a a matsayinta na shugabarshi, kamar katari sai kuwa ya had’a ido da Umad dake tsaye yana kallonsu idonshi cikin bak’in glass, duk da basa kallon juna ido cikin ido, amma sai Utais ya k’ureshida ido, lura da inda yake kallo yasa Ayam juyawa, da sauri ta kalli Utais tace “Pah, ni zan tafi, zamu fita ana jira na.”

Hannu ta d’ora a kafad’arshi ta sumbaci kumcinshi tace “Pah zan kiraka, kar fa kayi nisa da gida.”

Bai kula da abinda ta fad’a ba dan hankalinshi ya tafi kan Umad, saida ta juya zata tafi yace “Waye shi?”

Juyowa tayi ta kalleshi ta kuma juyawa ta kalli Umad, gimtse fuska tayi tana jin haushin yanda ya tsaya musu haka kamar mai son ganin me zasuyi, kallon Utais tayi tace “Sabon mai horar da mu ne Pah, kar ka damu ka je kawai.”

Jinjina kai yayi ya gyara tsayuwarshi ya bita da kallo, saida ta shiga motar rik’e da kwalin kyautarta sannan Umad ya shiga ta d’aya k’ofar, tayar da motar akayi hakan yasa Utais ya shiga d’aga mata hannu ita ma daga ciki tana d’aga masa hannu kamar zasu rabu, saida sukayi nisa sosai har sun kusa fita a makarantar ya daina d’aga musu hannun, numfashi ya sauke a hankali ya furta “Wanene shi? Ya aka yi ya min kama da wanda na sani da jimawa?”

D’aga kafad’a yayi ya shiga takawa shi ma dan dama idan ka zo ganin wani baka shiga da abun hawanka idan ba kai d’in wani bane, bare kuma shi da bus ya hau ya zo nan d’in kuma ita zata sake maida shi inda ya fito.

Tunda motar ta fita a harabar makarantar d’aliban suka kwashi rera wak’ar da suka saba yi a irin wannan lokacin, amma Ayam hankalinta ya karkata kan mahaifinta, zuwan nan da yayi ya sata jin wani abu daban, bai tab’a zuwa a irin wannan lokacin ba, yanda ya sunkuya mata ga da ga kuma ya jadadda mata da dan ya kira gimbiyarsa da gimbiya me ye a ciki ?

Ajiyar zuciya ta sauke ta sake k’amk’ame kwalin kyautar daya bata, Umad na zaune a kujerarshi a baya yana k’arewa yanayinta kallo daga cikin glass, wata zuciyar ce tace masa “Akan me zaka mayar da hankalinka kan wannan yarinyar? Ka duk’ufa neman abinda ya kawoka mana.”

D’auke kan shi yayi haka har suka isa jejin mai abun al’ajabi da tsoratarwa, fitowa sukayi suka kama layi a jere, gabansu ya tsaya hannayenshi goye a bayanshi cikin d’aga sauti yace” Shin a cikinku akwai mai sha’awar ganin wata dabba ne a zahiri?”

Bakwai a ciki ne suka amsa da” E yallab’ai.”

Hannun damansa ya kalla ta farkon ya tambaya da” Me kike son gani?”

Cikin d’aga murya ba tare da idonta ko gangar jikinta ya motsa ba tace” Alfadari yallab’ai.”

Kallonta yayi yace” Me yasa?”

Tana yanda take tace” Ina so na tabbatarwa kai na lallai ana samar da shi ne ta hanyar had’a jaki da kuma doki suyi barbara.”

Jinjina kai yayi alamar gamsuwa ya kalli ta gaba ita ma ya tambaye ta, da haka duk suka fad’i kalar dabbar da suke son gani a rayuwarsu har aka zo kan Sabrine dake kusan Ayam tace” Dorina yallab’ai.”

Kallonta yayi ita ma yace” Me yasa?”

Tana kallon gabanta tace” Saboda jiya ka fad’a mana tana da kakkausar fata, ina so na tab’a na ji.” 馃槀

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button