Lu’u Lu’u 8

Takawa yayi a hankali ya tsaya gaban Ayam, haka kawai ya ji zuciyarshi na kakkarwa da jin d’ar d’in tambayarta, dan bai san me zata fad’a ba ita, karta fad’a musu abinda zai kashesu ma, k’wayar idonta yake kallo daga cikin gilashin nan sannan yace” Ke fa?”

Kamar sauran ita ma muryarta a sama tace” Zaki yallab’ai.”

Tsamm! Ya ji tsigar jikinsa ta tashi wani yam yam yam, sauran kam duk kallonta sukayi baki bud’e, dreba kan shi dake cikin mota zaune saida ya lek’o ta taga, jinjina kai yayi a ranshi yace” Na sani dama ita ce, me ma yasa na lek’o? Aljana kawai.”

Sake had’e rai yayi yace” Me yasa?”

Ba alamar wasa ita ma tace” Haka kawai yallab’ai, burina ne tun ina k’arama.”

A hankali ya janye gilashin daga idanunshi ya kalleta ido da ido ko hakan zai bata damar canza ra’ayi, d’an sakin fuskarsa yayi sannan yace” Zakin gaske kike son gani ? Ko kuma na teddy?”

A lokacin kallon fuskarshi tayi ta saki murmushi tace” Na gasken yallab’ai.”

Muskutawa yayi yana kallonta ta k’asan ido yace” Me yake birgeki a game da zaki?”

Sakin hannayenta tayi tare da gyara tsayuwarta ta shiga kallonshi tana dariya tace” Ka gane yallab’ai, wannan tafiyar tashi ta k’asaita, wannan yalwataccen gashin daya masa k’awanya, idonsa masu d’aukar hankali, ni kawai ina so na ganshi a zahiri sannan na shafa bayansa, sannan ina so na ga faffad’ar k’afarsa wacce ke iya illata sauran dabbobin da duk ta daka sau d’aya.”

Wani basaraken murmushi ta saki ta tafa hannayenta tace” Kai gaskiya zaki yayi, ina son ganinshi a zahiri idan da yiwuwa ma mu zama abokai.”

Mayar da gilashinshi yayi a d’an hassale yace” Ina wasa da ke ne da zaki zauna yi min wannan bayanin?”

Cike da fara’a tace” A’a yallab’ai, amma ai a wajen aji ne.”

Da mamaki yace” Kamar ya?”

Kallonshi cike da yanayin yarinta tace” Yallab’ai ai jiya kai ka fad’a a aji ne muke d’alibi da malami, amma a wajen aji ka ce zamu zama kamar abokai.”

D’aga girarsa yayi ya juya zai shiga cikin jejin yana fad’in” To to d’alibai a motsa…”

Ayam ce tace” Yallab’ai.”

Juyowa yayi ya kalleta, kamar wata sakara ta saki baki tace” Dama ka tambaye mu ne ba dan ka cika mana burin mu ba?”

Fuskantarta yayi yana sake cire gilashin yace” Me kike nufi? Zakin kin d’auka abun wasa ne?”

Turo baki tayi gaba tace” Na sani yallab’ai.”

“Dan haka ki manta da son ganinshi kawai.” Ya fad’a yana juyawa zai bar wurin, a sanyaye tace “Ba zan iya ba, zan had’u da shi ko ta halin yaya.”

A gadarance ya juyo yace “Kin tabbatar?”

Jinjina kai tayi tace “Na tabbata.”

Wani shak’iyin murmushi yayi yace “Shikenan zan nuna miki zaki, amma ki sani idan kika firgita ko kika suma a wurin nan, to tabbas ke zan mik’a mishi a matsayin abinda zai yi kumallo da shi, kin yarda?”

Murmushi tayi ita ma tace “Na yarda yallab’ai, amma fa idan ban tsorata ba?”

Zuba mata ido yayi yana kallo kamar ba zai ce komai ba kafin ya gyara tsayuwarshi yace “Zan miki kyautar da zata baki mamaki da zaran na tabbatar da gaskiya a kan ki.”

Shiru tayi ta k’ura masa ido kamar zata yi tunanin maganar sa, shi ma abinda ya fahimta kenan kamar zatayi tunani kawai yayi saurin fad’in “Jira ni.”

Waya ya ciro daga ajihunshi suna kallo yayi nesa da su yana amsa waya, bai fi minti uku zuwa hud’u ba ya dawo garesu ya tsaya, cikin karsashi ya shiga nuna musu yana fad’in “D’alibai, ku nutsu sosai sannan ku kula, bindigogin dake jikin d’amararku ba sa d’auke da alburusai na kisa sai na kashe jikin kowace irin dabba, shi ma zaku harba ne idan kun shiga had’ari, sannan ina so ku maida hankalinku kan bishiyoyin wajen, sannan ku yi taka tsantsan d kuma lura da inda zaku saka k’afarku, dan a jejin nan an fara samun b’ata garin dake shigowa wasu suna kashe dabbobi masu wuyar samu, wasu kuma suna karya itace suna shiga da su cikin gari, dan haka ku kula sosai ku tuna da shekararku ce ta k’arshe wannan.”

Sara masa sukayi da buga k’afafunsu suka amsa da” To yallab’ai.”

Da k’arfi sosai yace” Kun gane?”

” E yallab’ai.” Suka sake fad’i a tare, jinjina kai yayi yace” Ku yi gaba zan zo a bayanku, zan fara nunawa shed’aniyar nan abinda ta nema, kuma bana son saka rayuwar d’aya a cikinku had’ari.”

Da k’arfi ya sake fad’in” Kun gane.”

“E yallab’ai.” Suka amsa da shi, sake jinjina kai yayi yace “To to ku motsa, kuyi aiki cikin had’in kai.”

Rarrabuwa suka fara yi suna gudu wasu su biyu wasu uku duk suka famtsama zuwa cikin jeji, juyowar da zaiyi ya ga ashe shi take kallo, kallo mai ma’anar “Ina jin kunyar ka fa malam.”

Yatsina fuska tayi tace “Na fad’a maka ka kiyaye kirana da kowane suna.”

Cire giashin yayi yana murtuke fuska yace “An fad’a, me zakiyi ? Wai ma ke ya akayi kika raina ni?”

Kawar da kan ta tayi tana wuwulasu tace “Ni ba mace ba ce, kawai ina ga fa so na kake shiyasa kake tunanin haka.”

Wani irin yatsina fuska yayi ya ja baya yace “Ke? Me? So? Da ke kuma?”

Girgiza kai yayi yana ci gaba da yatsina fuskar nan yace “Allah ya sawak’e min wahala.”

Da sauri ta kalleshi da mamaki a fuskarta tace “Allah ka ce? Waye shi?”

Ba alamar damuwa da tambayar data masa ya gyara tsayuwarshi yana d’auke kan shi daga kan ta yace “Allah shi ne wanda ya hallice ni, ya hallice ki kuma y…”

Da sauri ta katseshi da fad’in “Shi ya hallici sama d k’asa? Da duk wannan tsirren dake cikin jejin nan? Shi ne ya k’agi tekunan da suke ambaliya a doron k’asa?”

Da mamakin tambayarta yace “E hakane.”

Gyad’a kai tayi ta tafa hannunta tace “Dama na ce, na sani akwai wani dake juya duniyar nan wanda buwaya da izzarshi ta fi gaban wasa, amma ba wani banzan abun bauta Ghira ba wanda ko jini babu a jikinshi bare ya anfani wani.”

Kallon Umad tayi irin kallon tsanake ta sauke numfashi tace “Wane addini ne wannan? Ya ake a shiga? Ina so ni ma na zama d’aya daga cikin mabiyansa, na fi son ubangijin da zan bautawa ya zama mai jin buk’atuna, zan so ubangijin da zan bautawa ya zama shi ne ya samar da ni ba wai wanda kakanninmu suka samar ba, zan so ubangiji na ya kasance a tare da ni a ko yaushe ba wai sai na sha wahalar d’aukarsa a cikin jakata ba, kuma ina so ubangiji ya zama mai amsa rok’ona a sanda na rok’eshi, kuma wanda ba ya gajiya da amsa buk’ata ta bare ya min gori wata rana, wannan ubangijin nake da buk’ata, shiyasa ban tab’a bautawa kowa ba.”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button