Lu’u Lu’u 8

Gyara tsayuwa Umad yayi sai ma ya rasa bakin magana, kallonta kawai yake ita kuma tana ganin haka ta kyab’e baki tace” Haka dayawa ke ta fad’a, wai ina tsoratasu, wasu ma sun daina kulani saboda launin ido na da kuma wasu abubuwan, kai ma idan ka tsorata zan saka a layin ragwayen maza.”

A karon farko da murmushi ya sub’uce masa a gabanta, sosai yayi murmushi har hak’oransa na bayyana a fili, ganin haka sai ita ma ta saki murmushin tace” Karka damu malam, ba zan yarda kowa ya ji major Umad matsoraci bane.”

Iskan daya fara kad’awa mai k’arfi had’e da k’ura da kuma k’arar jirgi a sama yasa Umad d’aga kan shi, ita ma d’aga kan tayi sama suna kallon jirgin helicopter d’in, da kai ya mata alama yace” Muje.”

Zaro ido tayi tace” Kai ka kira jirgi? Ina zamu je?”

Kallon shegantaka ya mata yace” Ba zaki kike son gani ba?”

Jinjina kai tayi alamar e, saka gilashin shi yayi a ido hakan ha k’ara fito masa da kyawusa, hannun hagu ya mik’a mata yace” Muje to.”

A hankali ta d’aga siririn hannunta na dama ta d’ora akan tafin hannun Umad, da k’arfi ya jimk’e hannuta sakamakon shock d’in da ya ji irin na ranar, sai ya bar hakan a matsayin dan bai cika tab’a jikin mace ba tunda ai ita bata ji komai ba a ganinshi.

Fuskarta ya kalla da kyau yana sake nanato kalaman malaminshi akan yarinyar daya fito nema, musamman inda yake fad’in _”Akwai b’oyayyar jarumta a tare da ita, abinda ya cancanci ya bata tsoro ba shi ke tsorata ta ba, wanda kuma kai zai iya kayar maka da gaba, sai ka ga ita abin ado ne a gareta…_”

Tabbas ya fara jin wani abu a kan yarinyar nan, inba haka ba ta ya zata amince da shi haka a sauk’ak’e, lallai da ita xe wacce yake nema sai yace mata “Jarumtarki ta ban haushi, amma kuma raunin da kika nuna na yarda da ni ya birgeni.”

Jan ta yayi suka nufi inda jirgin ya tsaya, suna isa k’ofar dama a bud’e take, taimaka mata yayi ta fara shiga sannan ya shiga shi ma, d’amara suka d’aura a k’ugunsu, tashin jirgin aka fara su kuma suka fara k’ok’arin saka abun sauraron magana a kunnayensu saboda basj damar jin maganar juna ba tare da k’arar iskan ta kawo cikas ba.

Zura kan ta tayi ta d’aya k’ofar tana hangen k’asa ta taga, murmushi ta shiga saki ita kad’ai musamman yanda ta ga bishiyu na kad’awa su kuma suna k’ara haurawa sama.

Kafad’arta ya daddab’a tana juyowa yace “Kin tab’a shiga jirgi ne?”

Girgiza kai tayi tace “Ban tab’a tsayawa gani ga shi ba sai yau.”

Girarshi d’aya ya d’aga sama da mamakin kuma shi ne babu tsoro a tare da ita? Tafiya suka yi mai nisa saidai duk a cikin dajin suke, saida suka kai inda aka saka allon sanarwa dan daga nan zuwa inda mutum zai k’ara a cikin had’ari zai yi shi, dan dabbobi ne iri iri masu cutarwa a wurin.

Jami’in tuk’in jirgin ne yace wa Umad “Yallab’ai a shirya sauka mun iso.”

Kallonta Umad yayi yace “Kin shirya?”

“E yallab’ai.” Ta fad’a da karsashinta, jinjina kai yayi sannan ya ba matuk’in umarnin sauka, saida ya tabbatar sun tsaya sannan ta ga ya zura hannu a k’asan kujerar da yake zaune ya d’auko bindiga, wacce ke k’ugunshi ta aiki ya aje ya duba alburansan waccen ya d’auka, d’anata yayi ya saita mata komai tana kallonshi baki sake, yanda yake wasa da bindigar sai ta ji ya birgeta, kallonta yayi yana shirin fita yace “Mu je.”

Shi ne ya fara fita, za ta diro shi kuma daidai ya juya tare da rik’o k’ugunta da duka hannayenshi bayan ya soka bindigarshi a k’ugu, cak ta ji ya d’agata ya sauko da ita, kunya ce ta rufeta dan hakan bai tab’a faruwa da ita ba, kaa had’a ido tayi da shi haka shi ma sai ya ji kamar yayi gaggawa a lamarin.

Bindigar ya ciro sannan ya kalleta da kulawa ya shiga mata kurmanci wanda dama dole suke koya saboda irin haka, dan wata dabbar sauti zata ji ta farmake ka wata kuwa sautin tafiyarka ma, jinjina kai Ayam tayi dan ta fahimci abinda ya fad’a mata wato ta biyoshi a baya a hankali sannan ta kula.

Cikin sand’a suke tafiya Umad na gaba tana binshi a baya sai kalle kalle suke, k’wari da k’ananan dabbobi kam suna ta had’uwa dasu wanda ba sa cutarwa, suna cikin tafiyarsu a hankali cikin ciyayi koraye ya mata alama da hannu cewa ta tsaya. Tsayawa kam ta yi tana lek’awa ta ga me ya gani, a wuyanta ta ji motsi daf da hular kan ta, da sauri ta zura hannu da niyyar d’an sosawa, tudun abun da ta ji mai tabbatar mata da k’waro ne yasa bata ankara ba kuma bata shirya ba ta kwamtsa k’ara iya k’arfinta.

 

*Alhamdulillah*

The post Lu’u Lu’u 8 first appeared on 2gNovels.com.ng.

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button