MADADI Page 51 to 60

Da sauri ta ri’ke hannunsa tana girgiza kai tace”Wallahi ba haka bane ban hanaka ka kira yayana kuyi magana ba amma kada ka zageshi ko ka fada masa mummunar kalma.” Yace.”Okey na fahimce ki insha Allah zan kiyaye.”
Abbah Magaji na kokarin shiga motarsa kira ya shigo wayarsa koda ya duba sai yaga sabuwar numbar, zama yayi cikin motar tare da kara wayar a kunnasa…..Bash yace.”Sunana *Bashir Aminu dan jarida Jos!* Abbah magaji jin an kira sunan Jos yasa yayi saurin amsawa da fad’in “Malam Bashir ni kuma sunana Magaji Sani ina garin kano ina fatan naji kyakkyawan labari daga bakinka.
Bash yace.” Inaso na sheda maka cewar ‘Yar uwarka mai suna Naja’atu tana hannuna yanzu hakama tana kusa dani.” Abbah Magaji cikin farin ciki yace.”Alhamdullhi Allah mungode maka daka bayyana mana wannan yarinyar dan Allah inaso ka bata wayar zamuyi magana.
Bash yace.”Wannan lokacin baizo ba tukkuna Alhaji Magaji shin mai yasa kuka d’aurawa yarinyar nan aure da wanda bata so? kun san illar dake tartare da irin wannan auran kuwa.'”? Abbah Magaji yayi kasa’ke! jin irin maganganun da Bash din ke masa.” Katse shi yayi ta hanyar fad’in “Kaga mu bar wannan maganar tukkuna domin yanzu mu ba itace a gabanmu ba ganin yarinyar nan da sanin halin da take ciki shine a gabanmu maganar aure dole bata taso ba.”
Bash yace.”Naja’atu na nan kalau kamar yanda kuke fata sai dai kuma cikin da take dauke dashi ya zube!!!
Abbah Magaji yace.”Subahanallahi garin ya akayi haka ta faru.”? Bash yace.”To muma bamu san ya akayi hakan ta faru ba dan kafin tazo garemu al’amarin ya kasance.” Cikin jimami da damuwa Abbah Magaji yace.”Allah ya mayar da alkairi ku kuma Allah ya saka muku da alkairi insha Allahu gobe da wuri zan dauko hanya inaso ka bani cikakken address d’in inda zan same ku.”
Bash yace.”Babu damuwa zan baka address din inda muke a garin jos zuwa anjima zan tura maka text sai ka duba.”Abbah Magaji yace” To nagode sosai Allah ya saka da alkairi.” Sallama sukayi da juna kowa ya kashe wayarsa.
Abbah Magaji jikinsa a sanyaye ya nemi numbar abokinsa domin ya sheda masa cewar anga matarsa amma kuma baya tsammanin zai iya fad’a masa cewar yarinyar ta samu nasarar zubar masa da jiki, shi yanzu gabad’aya kunyar abokin nasa ma yake wallahi hakika da yasan Naja’atu zata basu kunya da baiyi ruwa da tsaki ba gurin ganin tabbatuwar auran! yanzu dai bashi da wani abinda zaice da abokin nasa dangane da abubuwan da suke faruwa sai dai kawai ya cigaba da bashi hakuri duk hukuncin kuwa da ya yanke a kan yarinyar hakan ba zaiyi masa ciwo ba saboda yasan itace ta janyowa kanta babu shakka ba kowane mutum ne zai yarda a zubar masa da ciki ba bai dauki mataki ba……A nutse suka gaisa da juna kafin Abbah Magajin ya sheda masa cewar an samu labarin ganin Naja’atu a garin jos…Abbah Abbas ya nuna bai san komai ba sannan kuma ya nuna farin cikinsa sosai kana kuma yace kafin dawowarsu gobe lallai Abbah Magajin yayi kokarin zuwa domin daukota.Sallama sukayi da juna kowa na danne abinda ke cikin
zuciyarsa.
Mutanan kofar na’isa sunyi farin ciki sosai da labarin da Abbah Magaji yaje musu dashi na bayyanuwar Naja’atu dake garin Jos ya kuma sheda musu da cewar su sake kwantar da hankalinsu yana tsammanin tana hannu nagari, amma kuma koda wasa bai sheda musu lalacewar cikin jikin da take dauke dashi ba.
Alhaji Sama’ila dashi Baba malam sunyi farin ciki sosai kuma sun godewa Allah tabbas adduarsu bata fad’i a kasa ba…..Jama’a mutanan unguwa sai shigowa baba Talatu suke a cewarsu wai sunzo taya ta murnar bayyanuwar ‘yarta, to ita dai sai ta rasa ma a’ina mutane ke samun labari tunda dai duk abubuwan dake faruwa a tsakaninsu sukeyi amma abin mamaki kafin kice me jama’a har sunji suna shigowa gulma da munafurci! haka nan ta daure ta dinga kar’bar mutane wanda da yawa daga cikinsu gulma da munafurci ne ke kawo su ba wani abunba.
To har duhun dare ya shigo Abbah Magaji bai ga text din da Bash yace zai turo masa…..Sai bayan yaci abinci ya nutsu tukkuna ya sake neman numbar Bash din kawai sai akace masa layin baya aiki yayi ta trying wayar na katsewa anty maryam dake kusa dashi a zaune tace” Jikina baya bani cewar mutumin da ya kira ka mutumin kirki ne idan da gaske taimakon yarinyar zaiyi me yasa tun dazu da kukayi waya dashi ba turo maka cikakken bayanin idan zaka same shi ba, duba fa tun dazu kake kiran wayarsa na katsewa.
A sanyaye Abbah Magaji yace”Naga alama yana so yayi mana wasa da hankalinmu ne kuma nima na soma zargin rashin gaskiya a tare dashi idan ba rashin gaskiya mai zai sa ya cire layinsa daga jikin wayarsa bayan yasan ga yanda mukayi dashi.” aunty maryam tace”Gaskiya da akwai alamun rashin gaskiya Allah dai ya kare yarinyar nan daga fad’awa hannun ‘bata gari.” Cikin rashin jin dadi da tunanin neman mafita ya amsa da “ameen” shuru sukayi kowanne na tunani a cikin zuciyarsa
Da Asuba Abba magaji na dawowa daga massalaci ya kunna wayarsa ko minti biyu baiyi da kunnawa ba text din Bash ya shigo da sauri ya shiga yana dubawa! hamdala yayi a fili kana ya shiga kiran numbar Bash din…’Kin shiga wayar tayi kamar jiya yayi ta traying ta’ki shiga cike da mamaki yake kallon wayar tashi to anya kuwa guy nan bashi da wata ‘boyayyar manufa? me yasa baya bari a sameshi a waya…………Bash Layin kansa sunfi hamsin wayoyinsa kuwa sun kai koma saboda yanayin sana’arsa yasa baya barin layi ya kwana a wayarsa shikenan sanja layi yana basaja Bash ya iya taku shiyasa jami’an tsaro suka kasa kamashi.
Koda aunty maryam ta shigo dakin sai ya sheda mata cewar ya samu text din da suke tsammani yanzu ta kar’bi wayar ta duba tana godewa Allah……Abbah Magaji a gurguje ya shirya dan ko break ba tsaya yi ba ya fito aunty maryam ta rakashi har bakin motarsa tana masa fatan dawowa lafiya…..Abbah Magaji kafin ya isa garin jos sai da ya kira Abbah Abbas ya fad’a masa ga halin da ake ciki…….A Lokacin suma jirginsu na dab da sauka, cike da nuna komai ya wuce yayi masa fatan dawowa lafiya da kuma samun nasarar dawowa da yarinyar cikin koshin lafiya.
Naja’atu tun kafin Abbah Magaji ya sauka a gidan take cikin wani irin yanayi na damuwa tana tunanin ko da wane ido zata kalleshi, yanzu ne kunyar abunda tayi yake damunta hakika tasan ta aikata musu abunda zai zubar da kima da mutuncinsu a gari, to amma anata ganin ai sune suka janyo hakan ta faru tunda sun kasa fahimtar daidai sunbi son zuciyarsu.
Abbah Magaji daidai inda Bash yace ya tsaya anan yayi parking din motarsa ya fito da wayarsa tare da neman numbar Bash din yana adduar Allah yasa ta shiga kada ya barshi a cikin mota ba tare da yasan inda zai nufa ba……Abin mamaki kiran farko Bash ya daga suka gaisa yace masa gashinan zuwa.” Abbah magaji ya kashe wayarsa yana jiransa gabadaya jikinsa yayi sanyi da yanayin halin munafurci da guy yake nuna masa….Bash ya iso guri cikin wata lafiyayyar mota mai muguwar tsada.!
Abbah Magaji kallo daya yayi masa ya tsinke da al’amarin guy sai kace wani kafuri yayi wata iriyar shiga irin ta ‘yan iska hatta da gashin kansa ya sanja masa hallita ya dawo browan ga wani irin aski dake kansa irin na gararrun turawan america…..Cikin wata ‘yar iskar tafiya ya nufi motar Abbah Magajin, sai yayi saurin bude mota ya fito ya tsaya yana kallonsa har ya karaso!