MADADI Page 51 to 60

Cikin wani irin tantiranci ya bashi bayan hannu wai su gaisa! Abba Magaji ya girgiza masa kai had’e da bashi tafin hannunsa da fad’in”Salamu alaikum.” Bash yayi ‘yar dariya yasa hannunsa cikin nasa ya amsa da “Amin wa’alaikasalam.” Abbah Magaji yace.”Ashe kasan da haka me yasa za kayi min gaisuwa irin ta kafurai.”?
Dariya bash yayi yace.”Afuwa na riga na saba ne wallahi ya gida ya hanya ya ka baro iyalinka.”?
Abbah Magaji yace.”Kowa lafiya kalau abokina amma banta’ba tsammanin ganin ka haka ba.” Bash ya sosa tarin sumar dake kansa yace.”Saboda me kace haka.”? Abbah yayi murmushi a nutse yace.”Yanda kake hausa yasa na fahimci cewar kai bahaushe ne kuma musulmi to amma ganin da nayi maka a yanzu yasa na d’ora ayar tambaya a kanka.” Bash yasa dariya yana kallon Abbah magaji kafin ya d’aga kafad’arsa sama yace.”Kamar yanda kake tsammani eh hakane ni musulmi ne gaba da baya cikin famliy na babu tubabbe dukkaninmu a cikin musulunci muka taso yanayin dressing d’ina da yawanci wasu abubuwa nawa ra’ayina ne hakan so ina ganin hakan bazai shafi addinina ba.” Abbah Magaji ya shiga girgiza kansa yana nazarin maganar……..Bash yace.”Muje gida na sadaka da kanwarka amma zaka bar motarka anan zamuje cikin motata.” Abbah magaji yayi saurin juyawa domin kulle motarsa yana fad’in “Babu damuwa hakan yayi.”
Abbah Magaji yana ta mamakin yanda Bash ke amsa wayoyin jama’a shi dai tunda ya zauna a cikin motar ba zai iya irga iya adadin mutanan da Bash ya amsa wayarsu ba, Nazarin motar kawai yake yana mamakin irin kwalaben giyar dake ciki ga tarin takardun wiwi nan da sauran kayan maye duk da motar na kamshin freshnar hakan bai hana shi jin warin kayan mayen dake ciki ba, haka dai ya daurewa zuciyarsa har suka isa gidan……
*MANZIR _ALWAFIR ABUJA????????*
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya ‘kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_
Mddbhrmbn47
*Bash* bai sauki Abbah Magaji a ko’ina sai a dakinsa Abbah Magaji ya samu guri ya zauna a nutse yana bin dakin da kallo..Bash ya bude fridge ya dauko masa ruwa da lemo masu sanyi a ajiye a gabansa Abbah magaji yace.”Nagode.” murmushi kawai yayi ya juya ya fita daga dakin ba tare da yace wani abuba. Abbah Magaji bai dauki lemon yasha ba dakin kawai yake kallo sa’ko da lo’ko gabadaya ya tsargu da yaron dan daka gani ba mutumin arziki bane! a hankali ya dauki ruwa ya bude ya d’an sha ya mayar ya ajiye, jin kira ya shigo wayarsa yasa yayi saurin dubawa abokinsa ne Ya kara wayar a kunnansa had’e da yi masa sallama, Abbah Abbas ya amsa a nutse yake sheda masa cewar sun sauka yanzu. Abbah magaji Yace masa shima yanzu haka yana inda yake tsammanin samun Naja’atun. Abbah Abbas yace.”To Allah yasa adace.”Sallama sukayi da juna Abba magaji na kashe wayarsa Bash da Naja’atu da Munira suka shigo dakin, Naja’atu sai ‘buya take a bayan Bash tana sinne kanta kunyar hada ido take da dan uwan nata…Shi kuwa Abbah magaji tunda suka shigo yake binta da kallo yana mamakin irin kwalliyar da tayi wato su suna can hankalinsu a tashe ita tana nan tana ado da kwalliya..Kafin ya ankara yaga Bash ya rike hannunta ya zaunar da ita a kusa dashi. ya bisu da wani irin kallon mamaki! kujera ce 1sitar amma sun nani’ka da junansu. Kunyar hakan yasa ta sunkuyar da kanta ‘kasa murya na rawa take gaishe shi shima a sanyaye ya amsa ganin abinda yafi karfinsa to hakan me yake nufi? ina kuma Naja’atu ta baro auranta? bashi da mai bashi amsa sai kawai ya zuba mata ido ya kasa cewa uffan! ganin irin kallon da yake mata ne yasa jikinta yayi sanyi sai ta fashe da wani irin kuka hade da had’a hannuwanta guri daya tace”Abbah magaji dan Allah kada kuga laifina dangane da faruwan wannan al’amarin wallahi ba laifina bane laifinku ne tunda tun farko na fada muku cewar bana sonsa bana sonsa kuka kasa ganewa har sai da kuka daura min aure dashi sabida haka yanzu duk wani mummunan abu daya biyo baya kune kuka janyo ni bani da laifi.”
Abbah Magaji maganganun da Naja’atu takeyi sunyi masa tsauri sosai har hazar yanzu ya kasa magantuwa sai dai ido kawai yake binta dashi mamakinta na kashe masa jiki…Bash ya dan rungume kafadarta yana rarrashinta wai tayi shuru ta daina kuka komai yazo karshe insha Allah, Abbah Magaji yana zaune yana kallon ikon Allan Bash sai matse masa ‘kanwa yake yi a gaban idonsa….Ransa a ‘bace ya buga musu tsawa da fad’in “Kai ka kiyaye fa wannan yarinyar matar aure ce musulunci bai baka damar ta’ba matar da bata kaba.” Bash ya wani sha kunu yana kallon Abbah Magaji da fad’in “A shirye nake dana d’aukaka ‘kara akan auran rashin adalcin da kukayiwa wannan yarinyar wannan ai son zuciya ne me yasa wai mafi akasari mutumin kano baida wayewar kai ne? meye amfanin auran dole da kukewa ‘ya’yanku tunda wannan yarinyar tace bata son mutumin nan to ya saketa mana dole ne.”? Abbah magaji yaji wani irin gumi na yanko masa bakinsa na rawa yace.” Waye yace maka auran dole akayi mata kuma kai meye ya shafeka da shiga cikin al’amarin da har kake maganar d’aukaka ‘kara shin kasan waye Alhaji Abbas kuwa.”? Bash ya zakud’a kafadarsa yace”Sanin waye Alhaji Abbas bashi ne a gabana ba abinda yake gabana anan shine ya saki Naja’atu na aureta shine abinda yake a gabana idan kuna ganin zaku yafe Yarinyar nan saboda ta bujirewa umarninku to ni Bashir zan ri’keta har ‘karshen rayuwarta ta duniya.” Abbah Magaji yace.”Inaso ka fad’a min meye manufarka akan yarinyar nan.”? Kai tsaye yace.”Munufa ta ta alkairi ce inaso in aureta bayan kun warware wannan auran da kuka ‘kulla.” Abbah Magaji yayi shuru yana ta nazarin maganar Bash din *Aure! Aure! Aure!* wane Uba ne zai dauki ‘yarsa ya bawa wannan lalataccen auranta duk wanda zai ga Bash mutukar mai hankali ne zaiyi kokarin nesanta kansa dashi saboda sam bai cancanta ma ka hada hanya dashi ba ballantana gaisuwa ta haka dashi!
Ya dago kanshi yana kallon Bash din gabadaya yanayinsa ya nuna yana cikin tashin hankali da damuwa yace.”Wannan maganganun da ka fada min suna nuna cewar da sanya hannuka gurin zubewar cikinta kun hada baki da ita kun zubarwa da abokina ciki domin ku cimma wata manufa taku ko.”?
Bash yayi murmushi hade da sosa kanshi yace.”Bana munufarci Alhaji idan da sa hannuna gurun zubewar cikin nan da tuni na fad’a maka sabida nasan da kai da abokin naka babu wani abu da kuka isa kuyi dan haka ka ma daina wannan maganar kafin Naja’atu tazo gurinmu cikinta ya zube a wani guri.” Abbh magaji ya shiga goge gumi yana kallon Naja’atu yace.”Yanzu meye ribarki ta zubar da cikin halak Naja’atu kin manta waye Alhaji Abbas a tare dake ko? Abokina Abbas bai cancanci wannan sakayyar daga gurinki ba.