MADADI 1-END

MADADI Page 51 to 60

Tana kuka tace”Wallahi ni ban zubar da cikin nan ba da kansa ya zube amma ni ban zubar ba.” a zabure! kafin kowa ya ankara ya kai mata wani bahagon mari! tasa kuka tana sake ‘boyewa a bayan Bash! Abbah magaji ya mike jikinsa na kyarma! yace.”Yaushe kika zama ‘yar iska Naja’atu irin tarbiyar da akayi miki kenan? ashe kina so ki zubar mana da mutunci a duniya da auranki kike rungume wani namiji! zaki fito daga nan ko sai na sumar dake a gurin nan.” Yakarasa maganar cikin hargagi!!! 

Bash ya mike tsaye da sauri ya janye shi daga gurin ya zaunar dashi kan kujera yace.”Alhaji duk wannan hargagin da kake ba zai taimake ka akan komai ba kawai kabi komai a sannu a hankali sai a samu maslaha na fada maka wallahi sai inda karfina ya kare akan wannan al’amarin dan ina son naja’atu itama tana sona babu wanda ya isa ya hanamu mallakar junanmu shi wannan tsohon mai zuciyar yara shi nake so ya yankewa kansa hukunci tun kafin a’lkali ya ‘kira shi.”

Abbah Magaji yaji wani irin kuttun bakin ciki da takaici ya tokare masa a makoshi tabbas zai zare hannunsa daga cikin al’amarin yarinyar kodan ya tsira da mutuncinsa gurin abokinsa… ya kalli Bash din da idanunsa wanda sukayi jajawur yace.”Yanzu zaka bani yarinyar nan ko kuwa ba zaka bani ita ba.”? Bash yace.” Sai abinda tace idan tana da ra’ayin bin ka gatanan a zaune ta fada maka.”

Abbah magaji ya tsirawa Naja’atu ido yana so yayi mata magana amma tsabar bacin rai ya hanashi cewa komai…

Kallonta kawai ya gaza furta kowace kalma ita kuma ganin haka yasa tace” Ni bazan koma ba har sai na tabbatar da cewar babu auran kowa a kaina sannan zan bika idan na koma zaku iya tursasani na koma gidan Wanda bana so…….Abbah magaji ya dauki wayarsa ranshi a bace ya shiga neman numbar abokinsa lokacin yana kofar na’isa tare da mahaifinsa suna tattauna maganar yana kuma sanar masa da irin hukuncin da ya yanke lokacin shi kuma Mahaifin nasa yake nuna masa ya janye hukuncin da yanke hakan bai dace ba……Wayar abokin nasa ya dauka yaji muryarsa cikin bacin rai yana sheda masa abinda ke faruwa… Kai tsaye yace ya bashi Naja’atun zasuyi magana da ita, da yake hands free ne Bash yana jin muryar Abbah Abbas din yana magana, Abbah magaji ya mikawa Naja’atu wayar da fadin “Gashi yana so yayi magana dake……’Kin kar’bar wayar tayi Bash ya kar’ba ya kara mata a kunnanta…jin muryar Abbah Abbas din yana magana yasa gabanta ya tsananta fad’uwa kiran sunanta yake ta gagara amsawa sai sheshshekar kukanta yake ji a kunnansa…..A nutse yace.” Kince ba zaki dawo gida ba sai anyi miki abinda kike so ko? shuru tayi ba tace komai ba. Ya dan sauke ajiyar zuciya yana sake jin wani irin tsanarta na d’arsuwa a zuciyarsa yace.”Kada ki damu tun ranar da kika tura min text na datse igiyar aurena guda daya dake kanki ina fatan Allah yasa hakan shi yafi alkairi kiyi hakuri ki dawo gida saboda samun kwanciyar hankalin iyayenki.” Jin abinda yace yasa taji wani sanyi na saukar mata a zuciya shima bash dake kusa da ita murmushi yayi kawai ya cire wayar daga kunnanta ya kashe ya mikawa me ita…Abbah magaji rasa bakin magana yayi ya dinga binsu da kallon takaici…..Bash ya mike da fadin “Bari nayi wanka ina tsammanin tare zamu tafi inaso naje na nuna kaina a matsayin wanda zai auri Naja’atu.” Abbah magaji uffan bai ce masa ba har ya shiga toilet dinsa…..Naja’atu ita da Munira suka fita daga dakin cike da farin ciki bukatarsu ta biya, shi kuwa bayan fitarsu daga dakin guri guda ya tsirawa ido kawai yana kallo babu shakka hukuncin da abokin nasa ya yanke baiyi masa dadi ba ko kadan! to amma yana adduar Allah yasa haka shine yafi alkairi Naja’atu kuwa ya tabbata da cewar sai ta girbi abinda ta shuka da hannunta yanzu shi dai zaiyi kokarin sadata da iyayenta shikkenan sai ya zare hannunsa daga kanta idan Allah ya kaddara auranta da Bash to shi kam dan kallo ne babu abinda ya shafe shi duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan doka.

 Abbah magaji yana zaune Bash ya kintsa jikinsa cikin sabuwar shadda galila mai kalar sararin samaniya (sky blue) dinki tazarce da dogon hannu mai link yasa hula irin ta kanawa sai kace wani mutumin arziki yayi wani irin kwarjini da kamala, Abbah magaji na zaune yana ta mamakinsa babu shakka yaron ya shirya tsaf domin zuwa ya yaudari su baba malam to idan ba hakaba meye nasa manyan kaya harda hula, Bash na daura agogo ya kalli Abbah Da murmushi a fuskarsa yace.”Nasan duk wanda ya gan ni cikin famliy naku zai yaba dani da cancanta ta a matsayin wanda zai auri Naja’atu ina fatan kai ma a matsayinka na makusancinta ka sanya mana albarka a cikin al’amarin.”

Abbah Magaji na kallon rashin kunya da tsabar jahilci shikkenan daga anyi saki kuma sai a shiga neman aure ai ya bari yarinyar tayi iddah tukkuna….Yace.”Bashir da alama baka da ilimin addini waye yace maka ana neman aure cikin iddah ai ka bari yarinyar tayi iddah tukkuna in yaso sai kayi wata magana….Bash yace”A’a da zafi zafi akan bugi karfe alhaji gwara naje na gabatar da kaina in yaso koma meye sai ya biyo baya.” Abba magaji ya bishi da ido cike da tsantsar mamakin maganarsa gaskiya jahilci bai yi ba.

Abbah Magaji motarsa ya shiga a maimakon Naja’atu tayi masa kara ta shiga motarsa sai ta nuna jin tsoransa yana kallo ta zauna gaban motar Bash ko kallonsa ta’kiyi takaicin haka yasa yaja motarsa da karfi… ya bar gurin.. Bash na murmushin samun nasara yaja tasa motar suka dauki hanya……sai da sukayi nisa sosai ya kalleta yace.”Baby wannan dan uwan naki fa na fahimci baya k’aunar alaqa ta dake ko kad’an!.” murmushin takaici tayi tace.”Bash bana tsammanin Abbah magaji zai kaunace ka dan shine babban abokin Abbah Abbas to kaga kuwa dole ya tsaneka.” Cike da rashin damuwa yace.”Hakan bai dame ni ba mutukar kina sona iyayenki sun amince dani ai bukata ta biya.” Jin abinda yace yasa gabanta ya fadi addua ta shigayi kan Allah yasa su baba malam su amince mata da auran Bash dan yanxu gabadaya shine babban burinta.

Alhaji Sama’ila da Baba Malam dashi uban gayyar ne a zaune a guri daya suna tattaunawa kan al’amarin da yake faruwa. Alhaji Sama’ila yana ta nuna rashin jin dadinsa dangane da hukuncin da d’ansa ya yanke a kan naja’atu shi kuma Baba malam yana nuna masa hakan ba laifi bane dan Abbas ya saki naja’atu domin samun maslaha ga junansu ya kuma nuna masa shi bai ji takaicin faruwar hakan ba dan dama ya riga ya barwa Allah al’amarin yana ganin tunda hakan ya kasance to shine alkairin……….Dukaninsu suna zaune suna jiran tsammanin dawowar Abbah magaji tare da Naja’atun………To Sai daf da magariba suka iso, Abbah magaji bai saurare su ba ya gyara parking na motarsa ya fito ya nufi massalacin dake jikin gidan Alhaji…..Naja’atu da kyar ta iya fitowa tana ta ‘boye kanta a cikin mayafi gabanta kuwa sai faduwa yake…Bash ganin Abbah magaji na alwala a cikin massalaci sai shima kamar gaske ya nufi inda yake Naja’atu kuwa tsayuwa tayi ta rasa ina zata shiga gidan Alhaji ko idan baba malam…Munira tace”Wai tsayuwar me mukeyi ne? haba duk kinbi kin damu kanki dan Allah ki daina jin tsoron abinda zai faru babu fa wanda ya isa yayi miki abinda Allah be miki ba ki saki jikinki dan Allah.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button