MADADI 1-END

MADADI Page 51 to 60

Hawaye ta d’an goge tace”Mu shiga gidan Alhaji munira ba zan iya shiga gidanmu ba ina jin tsoron Baba Talatu da Abbah Magaji kada ya shigo ya doke ni.” Munira tace”To muje gidan Alhajin tunda kinfi amincewa da nan.” Kai tsaye suka nufi gate gidan tana tafiya tana hard’ewa saboda matsatstsen siket d’in Munira dake jikinta gashi ba hijab bane mayafi ne a jikinta shiyasa duk ta tsargi kanta! Abbah Abbas da Alhaji sune suke kokarin fitowa daga gidan Naja’atu jin ‘kamshin turaransa yasa ta zabura! da sauri ta matsa gefe tana kauda kanta! Abbah Abbas karaf! idanunsa ya sauka a kanta duk da ta ‘boye fuskarta hakan bai hanashi ganeta ba kallon zatin jikinta kawai ya fahimtar dashi itace! cike da mamaki yake kallonta kwana uku kacal a jos ya mayar da ita watsatstsiya wane irin suttura ne wannan a jikinta sun fito mata da jikinta! da sauri ya kauda kansa ya wuce domin shiga massalaci…..Tana ganin wucewarsa ta zube ‘kasan gurin tana gaishe da Alhaji dake kokarin wucewa dan shi sam be ganeta ba, Jin muryarta yasa yayi saurin juyuwa yana amsawa da fad’in “Naja’atu kece.”? murya na rawa tace” Eh.” yace.”To masha Allah ku shiga cikin gidan mu zamu shiga massalaci domun gabatar da sallah.” A sanyaye tace “To” tana kokarin mikewa Alhaji kasa barin gurin yayi har sai da yaga sun shiga gidan tukkuna ya nufi massalaci zuciyarsa sam babu dadi dangane da faruwar al’amarin.

*Littafin na kudi ne..!*

Koda zaki ganshi a gruops to na sata ne idan kina bukatar biyan kudin karatu toga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300 account 0542382124…Binta umar gtbank..idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

*MANZIR _ALWAFIR ABUJA????????*

_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya ‘kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_

 Mddbhrmbn49

Halisa da Yaya Ramlatu ne a zaune a palon Hajiya sai hira suke cikin nishadi sunayi suna ciye ciye kana kallonsu zaka fahimci cewar suna cikin walwala da farin ciki…Hajia Abu lokacin ta hau sama domin daura alwala su kuma bayan barinta gurin ne suka tsiri gulmar abinda ya faru inda Yaya Ramlatu ke fad’in”Ai wallahi Halisa na sake gazgata al’amarin mutumin nan da ‘yar shagamu ta kai mu gurinsa kinga ni dai duk abinda ya fad’a zai faru gashi ya kasance gaskiya kiyi kokarin siyawa ‘Yar shagamu turaman atampopi muje tare dake gidanta mu kai mata domin mu sake nuna mata jin dadi da farin cikinmu sabida kin san hausawa nacewa dan towon gobe ake wanke tukunya nan gaba zamu iya zuwa mu sake neman wata alfarmar gurinta shiyasa nake so ki kyautata mata sosai dan itama taji dadi.”

 Halisa na shirin yin magana su Naja’atu suka shigo palon..Naja’atu ganin Halisa da Yaya Ramlatu a zaune yasa jikinta yayi sanyi da kyar suka shiga palon suka zauna cikin kokarin aro jarumta tace”Anty Halisa sannunku Yaya Ramlatu Ina wuni.”? babu wanda ya amsa mata a cikinsu Halisa sai binta da ido take tana ta’be bakinta, ita kuwa Munira ganin Naja’atu tayi musu magana basu amsa ba yasa ta kama kanta ‘kafarta ta d’ora kan d’aya tana taunar cingum had’e da duba tamfatsetsiyar wayarta….Yaya Ramlatu ta ri’ke bakinta tace”Oh! ikon Allah ke kuma Naja’atu garin yawon karuwancin naki kika samo wannan mara kunyar yarinyar daka ganinta ‘yar isaka ce da wasu idanunta a tsaye irin na marasa kunya.”!Munira ta zubawa Yaya Ramltu idonta ranta a ‘bace da jin irin mugwayen kalaman da take jifanta dasu. Za tayi magana Naja’atu ta rufe mata bakinta tace”Dan Allah kada ki kulata ki kyaleta duk wanda ya wulakanta wani kansa ya wulakanta.” Halisa tace”Ke Naja’atu Yaya Ramlatu kike kokarin gayawa magana? ai gaskiya ta fad’a a kanki dake da kawarki idan ba yawon karuwanci kika tafi ba to me ya had’a ki da wannan me wankakken idon.” Munira ta nuna Halisa da hannu tace”Wallahi kika sake kirana da wannan kalmar sai na wanke ki da mari zan nuna miki tsageranci na yanzu.” Halisa ta ri’ke bakinta tana kallonta tace”Sai ki mareni mara kunya kawai. Naja’atu tace”Kinga Halisa mu ba tashin hankali ne ya shigo damu gidan nan ba saboda haka dan Allah ki fita daga sabga ta kada ki sakeyi min magana tunda dai yanzu bani da al’aka dake.” Da sauri Ramlatu tace”To dan ubanki tashi ku fice mana daga gida tunda da bakin ki kin fad’a baki da al’aka damu ubanki kika shigo kiyi mana a gida.” Naja’atu jin zagin yayi yawa yasa ta fashe da kuka da fad’in “Ki daina zagina dan banga abin zagi ba anan.” Ai kamar ‘kara tunzura ta take ta dinga zabga mata zagi tana ambato sunanan Baba Malam tana cusa masa ashar! Munira tace”Amma ke kam anyi tsuhowar banza.” Yaya Ramlatu ta fusata ta fitar da hannu ta tsinka mata mari wanda yayi dai-dai da sakkowar hajia daga sama kuma duk akan idonta komai ya faru…Cike da bacin rai ta zauna tana kallon Ramlatu tace”Yanzu meye amfanin abinda kikayi da girmanki da komai kina shiga sabgar yara.”

Sai kawai ta fashe da kuka da fad’in” Wallahi hajia raina ne ya ‘baci! shiyasa na kasa daurewa wai yarinyar nan itace take fad’a mana cewar dasa hannunta gurin zubewar cikin Naja’atu ko kunyar idona ba taji ba take fadin haka ita kuma Naja’atun na sake tabbatar mana da gaskiyar magana harda cewa wai yanzu bata da wata al’aka damu tunda ta rabu da auran jaraba ciki kuma ta zubar duk abinda zamu yi sai dai muyi.”

Naja’atu da Munira kasa magana sukayi suna mamakin iya sharri na matar sai kuka take tana fyatar hanci kamar gaske…..Halisa kan dariya kawai take cikin zuciyarta itama mamakin iya sharri na ramlatun take.

Hajia Abu ta kalli Naja’atu tana so tayi magana sai ta riga tana kuka tace”Wallahi hajia ba haka bane sharri ne ni ban sha wani abu domin na zubar da ciki ba da kansa ya zube amma wallahi duk cikin magabar da Yaya ta fad’a babu gaskiya a ciki.” Ya Ramltu tace”Ubanki ne yake miki karya kaji ni da mara kunyar yarinya wa zaki yaudara? ashe har kin manta irin maganganun da kika fad’awa Salim to idan ke kin manta mu bamu manta ba munufuka kawai kin bar zuriarmu har abada.”

Hajia tace”Ya isa dan Allah duk zancan tashin tashina bai taso ba abinda ya faru ya riga ya faru kuma zamu ajiye shi a matsayin kaddara haka Allah ya hukunta sabida haka kada na sake jin kin zagi naja’atu ko kin fadi mummunar kalma a kanta Naja’atu bata isa ta tsarawa kanta abunda take so ba komai ya faru da rayuwarta kaddara ce ciki kuma da ya zube dama can Allah ya hukunta ba zai taka kasar duniya ba munafatan Allah yasa haka shi yafi alkairi.”

Yaya Ramlatu ‘kus! tayi dan ba tayi tsammanin hajiyan zata goyi da bayan yarinyar ba ganin yanda ta nuna ‘bacin ranta lokacin da taji labarin zubewar cikin..Halisa da yake neman gindin zama take a gurin hajiyan sai ta ‘kaskantar da kanta kamar mutuniyar kirki tace”Wallahi kuwa hajia ai nima haka nace duk abubuwan da suke faruwa kaddara ce Allah yasa Auran Abbah Mufida da yarinyar ba zaiyi tsayi ba shiyasa duk haka ta faru amman mu munso Auran yayi albarka ya zama mutuwa ce zata rabasu kamar yanda ta ratsa tsakaninsa da Halimatu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button