MADADI Page 51 to 60

Hajia tace”Ke da yake mai hankali ce kin gane yanda lamarin ubangiji yake amma ita waccan da girmanta da shekarunta tana abubuwa irin na yara.”
Yaya Ramlatu sunkuyar da kanta tayi kunyar duniya ta isheta hajia ta kunyatata gaban yara kananu ita kuma halisa da yake ta fita dubara ta wanke kanta kasa d’ago kanta tayi dan tana jin kunyar had’a ido da yaran Munira kuwa sai dariya take ‘boyewa taji dadi sosai da hajiyan tayi wa matar wankin babban bargo.
Sai bayan sun fito daga sallahr isha’i ne suka samu zama gabadayansu a kofar gidan baba malam da yake dogon dakali ne mai fadi da tsayi kuma yana sawa kullum a share a shimfida katuwar tabarma saboda masu daukar darasu! Suka zazzauna harda Bash da yake ta wani sunkuyar da kansa, cikin nutsuwa yabi kowansu yana mik’a masa hannu har yazo kan wanda yake tunanin shine abokin adawarsa Abbah Abbas ya rike hannunsa suka gaisa cikin kulawa da mutunta juna sabida shi bai san abinda ke tsakaninsa da tsohuwar matar tasa ba to koma dai ya sani bashi da abinda zaice tunda ba huruminsa bane….A nutse Bash yayi musu bayanin yanda akayi Naja’atu tazo garesu ya kankantar da kansa sosai ya nema mata afuwa a gurinsu gami da cewar su dauki dukkanin abubuwan da suka faru a matsayin qaddara sannan kuma kodan gaba su guji yiwa ‘ya’yansu auran da basa so ko dan gujewa faruwar matsala makamciyar wannan.” Baba malam da Alhaji sai godiya suke masa dan gabadayansu sun yaba da hankalin yaron kuma abinda yayi musu ba zasu ta’ba mantawa dashi ba shiyasa suke tayi masa godiya tare da yiwa iyayansa addua….Cike da jin dadi Bash yake amsawa yana shafa wuyansa hade da sunkuyar da kansa irin na munafukai…..Abbah Magaji da Abbah Abbas kallonsa kawai suke baran Abbah Magaji da yasan waye Bash d’in shiyasa bakinsa ya mutu yakasa cewa komai yana jin yanda Bash yake ta basu labarin waye mahaifinsa, ba’aje da nisa ba suka gane mutumin tunda gabadayansu masu sauraran redio ne shi kuma Aminu dan Jarida yayi suna sosai akan aikinsa kuma yayi aiki a gidajen redio da dama shiyasa su ganeshi nan take.
Alhaji yace.”Duk da bamu ta’ba ganin mahaifinka ido da ido ba amma muna sauraran muryarsa hakika mahaifinka ba ‘boyayye bane kuma munji dadi da yarinyar ta kasance a gurunku idan ka koma gida kayi wa mahaifinka godiya a bisa karamcin da akayi mana.” Bash yace.” Ya kwana biyu baya gida aiki ya kaishi amuruka amma idan ya dawo zan fad’a masa sa’kon gaisuwarku.” Baba malam yace to babu damuwa Allah ya dawo dashi lafiya.” Gurin ne yayi shuru na minti biyu kowa na sa’ke-sa’ke a cikin ranshi, Bash ya gyara zamansa kansa a ‘kasa yace”Malam ina neman alfarma a gurunku idan zan samu.” Da sauri Baba malam yace.”Wace irin alfarma kake nema yaro.” ? Bash yace.”Inaso idan Naja’atu ta ‘kare iddah na aureta idan babu damuwa.” Baba malam yayi murmushi yana kallon Alhaji yace.”Kaga mahaifinta nan dashi za kayi magana.” Bash ya kalli Alhaji yana dan murmushi….Abbah magaji mikewa yayi had’e da zura takalminsa ya mikawa abokinsa hannu da fad’in “Zan nufi gida Sai ka shigo kenan.” Abbah Abbas yace.”Ka zauna a ‘kare maganar da kai mana.” Girgiza kansa yayi yace.”Tunda duk kuna gurin ai babu matsala ina fatan Alheri a cikin al’amarin.” Baba malam da Alhaji suka amsa da ameen.” Shi kuwa Abbah Abbas ido kawai ya zubawa Bash yana kuma sauraran amsar da Alhajin zai bashi….Alhaji Yace.”Babu komai Bashir shi aure rabo ne idan Allah yasa wannan yarinya matarka ce sai kaga ka aureta idan kuma baka da rabo sai kaga wani ya aureta amma dai musulunci bai baka damar tunkararta a yanzu ba ka bari tukkuna ta kare iddah sai ka shiga layin zawarawan ta.” Bash yace.”To nagode sosai Alhaji nagode da karamci ina kuma addua Allah yasa Naja’atu rabona ce.” Suka amsa da ameen banda Abbah Abbas da yake jin takaici na neman dagargaza! masa zuciyarsa mtwsss! mi’kewa yayi dan ganin zaman ma da yake a gurin bashi da wani amfani ya daure ya bawa iyayan nasa hannu da fad’in “Shima zai wuce gida domin yaje ya huta, Bash ya bashi hannu da fad’in ” To Alhaji a huta gajiya nagode sosai da kulawarku a kaina.” Abbah Abbas ya daure ya amsa da babu damuwa kai ma ina maka fatan alkairi tare da adduar sauka lafiya.”
Kai tsaye cikin gidan Alhaji ya nufa yana tafiya tamkar zai tsaga ‘kasa sabida yanda yake taka ta da karfi! wai! kishi ne ko me? Koda ya shiga palon samun Naja’atu yayi da Munira sai ciye ciye suke na irin tsabar da sukayi ta saudia sun sake suna hira harda shewa ga Halisa a zaune a gefe kamar wata mujiya!!! dan tuni Yaya Ramlatu ta tafi…….Saboda ba kunyar da hajia ta bata shi yasa ta kasa zama sai ta tattara tsarabarta ta ‘kara gaba cike da takaicin abinda hajiyar tayi mata….. Halisa ta tsurawa tv ido kamar mai kallo amma ita kadai tasan takaicin dake cikin zuciyarta gefe guda kuma tana mugun mamakin d’aurin gindin da yarinyar take dashi a gurin hajia………Naja’atu tunda ya shigo palon bakinta ya mutu sunkuyar kanta ‘kasa tayi Munira nata magana amma bata tanka mata ba..To itama Munirar kamshin lafiyayyan turaran da taji ne yasa ta kalli bakin ‘kofa….Ta tsira masa ido tana tunanin inda tasan shi…Abbah Abbas ne mai zuwa musu visiting makaranta sai taga kamar ya dawo matashi gabad’aya mutumin ya’ki tsufa! wallahi bata ta’ba tsammanin zata ganshi hakaba ta dauka za taganshi furfura ta baibaye masa fuskarsa sai taga akasin haka ya sake zanzarewa yayi wani fresh dashi…Gaskiya ya burgeta tana son namijin da yake kula da kanshi kuma dan gayu….Muryarsa ce ta katse musu tunaninsu inda yake magana da Halisa yana tambayarta ina Hajia? Halisa na fari da ido tace”Bata jima da hawa sama ba.” Ba tare da yace komai ba ya nufi saman…Gabad’ayansu har ita Naja’atun suka bishi da kallo…..Halisa ta juyo tana kallonsu tare da ta’be bakinta tace”Sai dai kallo daga nesa dan wutsiyar raqumi ta riga tayi nesa da ‘kasa komai na babba yafi na yaro! wannan dai mijin mace d’aya itace Halisa.”! Munira ta d’age! girarta tana murmushi had’e da girgixa kanta tace”Wallahi kiyi mana shuru da bakinki idan ba hakaba ki raina kanki ko yanzu mukayi ra’ayin komawa zamu koma har kike wani cika baki….. Ji wata magana dan Allah “Wai komai na babba yafi na yaro hahahaha to me zaki nuna mana.”? tafada tana she’ka mata dariya hade da nunata da hannu.” Halisa tace” Eh ai dole nayi magana naga kun bishi da kallo sai kace zaku cinye shi.” Naja’atu ta tab’e bakinta tana girgiza kai tace”Dan Allah Munira kiyi mata shuru ni bana son damuwa wallahi so nake ma su tafi su bamu guri mtwws! Halisa tace “Aikin banza kawai ki daina dena za’kewa a gidan da baki da gado dashi sai kace gidanku sai wata fuffuka kikewa mutune.” Naja’atu shuru tayi bata tanka mata ba, Munira kuwa ta mayar da Halisa kamar mahaukaciya sai dariya take mata, Halisa ta cika tayi fam fam! takaicin ya isheta, aikuwa yana saukowa wai zata kai mai ‘kara! ya kuwa buga mata razannaniyar tsawar da tasa ta dauki jakarta babu shiri tayi waje! bayanta yabi ba tare da ya kalli iskar da ta d’ebo su ba.
Share this
[ad_2]