MADADI Page 51 to 60

Halisa ta matso kusa dashi tare da dafa bayansa cikin tausasawa tace”Kayi hakuri abban mufida ni dama nasan da kamar wuya yarinyar nan ta bar cikin nan tunda da kunnena naji tafada cewar ita ba zata ta’ba haihuwa da kai ba tunda bata sonka kuma duk yanda za tayi sai tayi ka saketa ta auri wanda take so gashi kuwa ka gani kuma kaji da kunnanka wanda idan wani ne yazo ya fada maka cewa za kayi karya ne shiyasa kullum nake cewa dakai yarinyar annobace a cikin mu yana da kyau dai tun wuri ka nemawa kanka mafita amma gabadaya zama da ita ba alkairi bane.”
Abbah shuru kawai yayi yana ta nazarin maganganun Halisan tabbas halisa tayi gaskiya yana da kyau tun kafin yarinyar tayi masa wanwar! yayi gaggawar cire ta daga rayuwarsa dan bazai iya jure wannan al’amarin ba, wato shi ya gama shan wahalar dasa ‘kwansa lokaci guda ayi masa asararsa gaskiya bai zai iya daukar wannan rashin mutuncin ba dole ne ya dauki mataki a kanta..Halisa ganin yanda ya fusata! sai taji dadi ta cigaba da zugashi kancewar kada ya yarda har in dai yarinyar tayi nasarar zubar masa da ciki to ya dauki mataki mai tsauri a kanta.
Jinta kawai yake yi yana ganin ita bata isa ta nuna masa ga irin hukuncin da zai dauka akan yarinyar ba ko wane irin hukunci ya dauka akanta ya barshi a zuciyarsa sai ya tabbatar da cewar ta samu nasara a kansa sannan zai zartar dashi.
Duk inda aka san za’a ga Naja’atu an dubata ba a ganta ba, hankalin iyayenta da duk wani wanda ya shafeta ya tashi, baba talatu kuka kawai takeyi dan takasa daurewa sai salati take tana kiran sunan Allah da fadin Allah ya bayyanta yarinyar a duk inda take……Baba malam kuwa alwala ya daura ya hau kan dadduma domin shedawa Ubangiji halin da ake ciki……Abbah magaji da Abbah Alhassan kam gidajen redio suka nufa domin shigar da cigiya..to al’amarin ya fi karfinsu dole sai sun had’a da cigiya dan ganin duhun dare ya shigo babu wani labari.
Yaya Ramlatu ta samu labari a bakin Salim bayan ya dawo daga kasuwa ya kunna mata roconding din ta saurara! aikuwa bata bari gari ya waye ba ta dauki mayafinta tare da wayar Salim din ta nufi kofar na’isa tana shiga gidan nasu kai tsaye sama ta nufa dakin Alhaji suka gaisa kamar abin arziki kawai sai ta kunna masa roconding din tace ya saurari abinda Naja’atu ta aikata.
Alhaji Sama’ila da ba lafiya ya cika ba dalilin da yasa duk abinda akeyi be sani ba dan baba malam cewa yayi kada a fada masa saboda lalurarsa kada a tayar masa da hankali
Jin audion Naja’atu yasa jikinsa ya rikice! sosai ya dinga salati yana kiran sunan Allah jikinsa na wani irin rawa har sai da ta firgita da ganin halin da ya shiga…Abbah Alhassan ya shigo dakin ya ganta a zaune ga Alhajin na makyarkyata yana neman faduwa, da sauri yaje ya rikeshi yana salati! Yaya Ramlatu jikinta sanyi yayi ganin jikin mahaifin nata ya rikice sai ta shiga inda inda a lokacin da Abbah Alhassan ke tambayarta abinda yasa shi shiga damuwa tace”Itama tazo gaisheshi ta ganshi cikin wannan yanayi…Da sauri ya kira Salim a waya yace maza yazo zasu kai Alhaji asibiti….Minti goma salim ya iso gidan suka rirrike Alhajin suka sauka dashi kasa…..Hankali a tashe hajia Rabi amaryasa tabi bayansu…ita kuwa Yaya ramlatu a sanyaye ta fita daga gidan a maimakon ta nufi gidanta sai kawai ta shiga gidan Baba malam suna zaune cikin alhini da damuwa ta tsaya a kansu babu gaisuwa kawai ta kunna musu muryar ‘yarsu! gurin yayi tsit! sai da suka gama saurara sannan ta kashe wayar ta kama hanya ta fita daga gidan ba tare da tace uffan ba, tana fita baba talatu ta cigaba da share hawaye tana girgiza kanta da fadin wannan yarinya kin janyo mana abin kunya a idon duniya innalilihi wa’ina ilaihi raji’un.
Naja’atu tana can tana gagaranba a garin jos dan tun bayan saukar ta a tashar garin tana fitowa daga mota wani matashi ya warce mata pose dinta da wayarta a ciki da kudadenta! abinka da tasha da turmutsutsu babu wanda ya ankara da abinda ya faru!! ta dinga kuka tana waige-waige a tashar ga duhun dare ya kawo kai yanzu ya za tayi ta kira Munira dan gabadaya ta manta sunan unguwar tasu ballantana ta shiga motar da zata kaita unguwar ta nemi gidan…Hannunta ta kalla taga dari biyar da dari biyu ajiyar zuciya ta sauke wannan ‘yan canjin sune kawai suka rage mata, dan haka da sauri taja akwati ta fita daga cikin tashar lokacin anata kokarin shiga massalaci domin sallar magariba….Tafiya me tsayi tayi ba tare data san inda ta dosa ba, gajiya da yunwa yasa ta nemi gefan titi ta zauna tana kalle-kalle!! ta jima a zaune a gurin tana kallon mutane nata shige da fice wasu matasan samari na nuna ta suna dariya sai ta tsorata ta mike da sauri ta bar gurin…Sawun tafiya taji a bayanta tana juyawa ta ga wannan matasan suna binta sauri ta ‘kara tana hard’ewa yayinda gefan cikinta ke wani irin murd’awa!!! Kafin ta ankara taga sun kewaye ta, a tsorace take kallonsu da fadin” Ni bakuwa ce a cikin garin nan dan Allah ku taimaka min kada ku cutar dani.”
Daya daga cikinsu yace.”Muma ki taimaka mana sai mu taimaka miki wane gida kike nema.”? murya na rawa tace”Wallahi na manta address din gashi wani ‘barawo ya fizge min jakata da waya ta a ciki ballantana na duba.” Hahahaha! suka sa dariya suna nunanta dayan yace.”Kizo kawai muje dake masauki baki da matsala tunda kin hadu damu.
Tsorata tayi ta dan matsa gefe tana neman hanyar guduwa, wanda yake gefanta ya fizgo hijabinta yana kokarin sha’ke mata wuya! da sauri ta fizge ta bangajeshi a guje ta kama hanya! aikuwa suka rufa mata baya…Takalmanta da akwatin kayan dake hannunta ta watsar ta dinga gudu tana kiran a taimaka mata! Jos dai ba daya yake da sauran gaguruwa ba! yawanci gidajensu babu doguwar katanga mafi akasari ma a waje suke rayuwa dan haka tana shigowa cikin mutane tana wannan gudun jama’a suka kewayeta suna tambayarta abinda ke faruwa…Su kuwa matasan samarin nan ganin ta tsere musu sai suka koma da baya suka dauke akwatin kayanta data jefar sukayi nasu guri
Wata mata ce ta rike ta ta kaita gidanta ta zaunar da ita tana tambayarta daga wane gari take!? Naja’atu kwanciya kawai tayi tana zirarar da hawaye wannan wace iriyar masifa ce? matar ganin bata kulata ba yasa ta tashi ta bata guri, dama abinci take siyarwa a kofar gidanta sai kawai ta koma ta cigaba da sallamar mutane….Wani irin kuka take tana rik’e cikinta wani matsiyacin ciwo yake mata! sai kyarma jikinta keyi…..sai kusan sha d’aya na dare matar ta shigo gidan ita da ‘yan yaranta biyu…Ganin Naja’atu a kwance a inda take yasa ta tsaya a kanta tace”Baiwar Allah nifa tausayi kika bani shiyasa har nayi sha’awar taimaka miki amma dan wulakanci tun dazu sai magana nake miki kinyi min banza
Naja’atu da kyar ta iya mikewa zaune tana share hawaye tace”Dan Allah kiyi hakuri bani da lafiya shiyasa na kasa yi miki magana.
Tace”Me yake damunki.”? A hankali tace”Cikina ne yake ciwo.”? matar sam bata dauka ita din matar aurece bace tace”Yanzu dare yayi dana kaiki chamis amma bari na dauki miki ja da yallow kisha idan baiyi miki ba sai kisha kanwa zaki ji dadi.
Naja’atu tace”To nagode.” Daki matar ta shiga ta fito hannunta rike da plate a rufe da abinci a ciki tace ga abinci ki fara ci sai kisha maganin.” da sauri ta kar’ba dama yunwa na damunta…Lomar farko ta raina kanta dan jin yanda bakinta ya game da yaji!n attaruhu! miyar sai kace ta mayu saboda tsananin yaji! ruwa ta dauka da sauri tasha, ta dauka ta karayin loma guda…Tana zukar bakinta ga abincin da dadi amma sai uban yaji!!! Miyar ta ture ta shiga cin farar shinkafar amma duk da haka akwai yaji, wani irin amai ne ya shiga yunkuro mata ta dinga danneshi amma ina!! a guje ta nufi bakin rariya ta shiga kelayawa tana kakari da rike kirijinta da yake mata wani irin zafi……matar ta tsaya a kanta tana yi mata sannu har ta gama ta riike ta suka dawo suka zauna tana mata sannu ta mika mata kwayoyin maganin ja da yallow da wannan maganin mai mugun dacin tsiya na tsayar da gudawa! ba tare da tunanin komai ba ta karbi maganin ta watsa a bakinta ta kora da ruwa!! (Shan magani barkatai ba tare da ka’ida ba yana janyowa mai ciki babbar matsala matar tace”Sannu bari na shiga na gyara miki guri ki kwanta gobe kafin na fita kasuwa zan kaiki asibiti a dubaki..Naja’atu daga mata kanta kawai tayi tana jin wani irin jiri na d’ibarta.