MADADI 1-END

MADADI Page 51 to 60

Misalin karfe daya rabi na dare ya tashi yaje ya dauro alwala ya fuskanci alk’ibula yana kaiwa Allah kukansa ni dai ban ta’ba ganin babban mutum na kuka ba sai akan Abbah Abbas gabadaya ya kasa daurewa ganinsa a gaban mai kowa da komai yasa zuciyarsa ta karye ya shiga zurarar da hawaye yana me kai masa kukansa.

A daidai lokacin shima baba malam ya kadaice kansa da Ubangiji yana nemawa rayuwar yarsa sassauci gami da za’bin alkairi dan yanzu gabadaya al’amarin ya fice masa daga rai sai dai neman zabin Allah duk abinda kuwa ya zartar shine daidai.

Karfe uku daidai Naja’atu ta mike zumbur! jin yanda wani irin mahaukacin ciwon ciki ya turnuketa kafin kice me ta fita a hayyacinta…salati ta shiga yi tana murkususu a kan shimfidar da take kwance…Maman Sajida ta tashi da sauri ta kunna fitila tana kiran sunanta, Naja’atu hannunta ta rike tana hawaye tace” Baiwar Allah ki taimaka min hakika ina azabtuwa a cikin wannan daran.” Maman Sajida tace”Sannu ni wallahi dana ga kinyi bacci na dauka kinji sauki ashe ke kadai kika san abinda yake damunki sannu bari gari ya karasa wayewa na kaiki asibiti.” Naja’atu kanta kawai take dagawa tana ambaton Allah a cikin zuciyarta…

haka suka kasance har garin Allah ya waye maman sajida taje tayi alwala tayi sallah agurguje ta fita ta kira makociyarta Maman Ladi suka fara kokarin kama Naja’atu domin su mikar da ita! Ita kuwa rintse idonta kawai takeyi cin yanda kwankwasonta ke amsawa sai kawai ta saki karamar kara ta koma ta zaune tana mike kafarta kawai suka ga jini na bin cinyoyinta…Sai suka shiga salati suka kamata da kyar suka kaita bandaki suka tsuganar da ita…Maman Ladi tace”Yariyar nan ‘bari za tayi innalilhi! Maman Sajida tace “bari naje na dauko babur . da dauri ta fita daga bandakin…Wai Naja’atu kwanciya tayi a bandakin duk kaxantarsa bai dameta ba taimakon Allah kawai take nema…Kafin maman Sajida ta dawo ma ai akin gama ya riga ya gama tuni cikin ya bi rariya tunda duk ga daddaginsa nan a kasan bandakin sai uban karni ne ke tashi a gurin ….Maman Ladi ta ri’ke bakinta cike da mamaki take kallon Naja’atun tace” Ashe ma cikin baiyi kwari ba to Alhamdullhi tunda Allah ya rabaki da wahala haihuwar d’an shege a wannan zamanin ai masifa ce.” Naja’atu a galabaice take kallon matar tace”Kina nufin cikin jikina ya fita.”? Maman Ladi tace”Ga zahiri nan kina gani a kasa yana bin rariya sai ki godewa Allah! ajiyar zuciya ta sauke tana godewa Allah a cikin zuciyarta.

*Wayyo Allah Abbah Abbas????????*

_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya ‘kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_

43

Maman Sajida ta shigo bandakin da sauri tana fad’in” Maman Ladi kamata mu fito da ita ga babur can na samo a waje.” Maman Ladi tace”Wane na kamata ai tuni cikin ya zube kada ma kiyi asarar kudin motarki.” Sororo maman sajida tayi tana kallon Naja’atu dake durkushe kamar wacce take kan gwiwa!(mace mai naquda) A sanyaye tace”Ai shikkenan to Allah yasa haka shi yafi alkari ni wallahi ma ban dauka ciki ne da ita ba.” Maman Ladi tace”Ke dai maza kije ki sallami mai babur ya tafi sana’arsa kin barshi a waje.” Maman sajida tayi saurin juyawa ta fita daga bandakin…Maman Ladi ta kalli Naja’atu da fadin”Sannu yaya yanayin jikin naki.”?

Murya na rawa tace”Jiri nake ji da ciwon mara.” Ta’be bakinta tayi tace”Ai dama dole kiji haka tunda kin zubar da jini ciwon mara kuwa ai ya zama dole haka kawai da kuruciyarki da komai a maimakon kiyi aure ki raya sinna sai ki dinga bin maza duba dan Allah wani shegen gardi yayi miki ciki ya barki da wahala shi yana can a kwance wallahi kuyiwa kanku fad’a.'”

Wasu hawaye ne masu zafi suka shiga zubo mata, ashe kallon karuwa suke mata…Da kyar tace”Baiwar Allah ki daina yi min kallon karuwa wannan cikin na jikina yana da uba.” Maman ladi tace”Ai dama kun saba dauko ciki idan ku kaga asirinku zai tuno kuce cikin ku yana da uba to dama wane d’ane bashi da uba! kowa ne d’a yana da ubansa sai dai wani ana samar dashi ta hanyar da bata dace ba.

Naja’atu shuru kawai tayi tana jujjuya kanta gaskiya maganar da matar nan takeyi tayi bala’in ‘bata mata rai….Maman Sajida ce ta shigo bandakin suka taimaka mata ta mike tsaye ta jingina da bango(garu) Maman sajida tayi saurin zuwa dakinta ta dauko mata daya daga cikin kayanta riga da zani na atamfa da sabon pant gami da audigar mata suka taimaka mata ta gyara jikinta, cikin kasala gami da jiri suka kaita suka ajiye a tsakiyar ledar dakin.

Maman Sajida ta dukufa aikin gyara bandakin yayin da ita kuma maman Ladi ta dage da surutai gami da farfadar mugwayen kalmomi akan naja’atu tana zuga maman sajida akan ta koreta dan daka gani ba mutuniyar arziki bace.”

Maman sajida tace”Nima shawarar dana yanke kenan anjima kadan idan ta samu nutsuwa zan zauna da ita na tambayeta garinsu idan ta tsaya yi min inda inda to korarta zanyi dan ba zata janyo da mutuncina a gari azo anayi min kallon banza ba.

Maman Ladi tace”Wannan shine tunani mai kyau ni na tafi gidana dan zan shirya ‘yan makaranta.” Maman Sajida tace”To nagode.” 

Naja’atu duk irin maganganun da sukeyi a bandakin tana jinsu, wasu zafafan hawaye ne kawai suke tsere a kuncinta yanzu idan maman sajida ta koreta ina zata nufa na farko dai tayi al’kawarin ba zata koma kano ba domun har yanzu bata karaya ba, tana nan a kan bakanta , na biyu kuma bata san gidansu munira ba ballantana taje can tana ganin zata fadawa maman sajida labarinta watakila ita zata fahimceta.

Maman Sajida ruwan tea ta d’ora musu ta aiki yaronta ya siyo musu kayan shayi, sannan dama tana da ragowar miyar jiya me yajin tsiya ta du’mama da yake akwai nama a ciki sai ta samu dan madaidaicin abu ta zubawa naja’atu miyar ta hada mata tea din ta kai mata har inda take zaune, tace”Gashi nan babu yawa miyar jiya ce na d’umamaki sai ki dangwala da bread. ga tea nan kuma.” A sanyaye tace”Nagode abinda kikayi min Allah yayi miki.”

Maman Sajida tana kokarin fita daga dakin tace”Ayya ai babu komai dan na taimake ki kina cikin halin taimako….Naja’atu tea din kawai ta iya kur’ba tana jin yanda jini keta ‘bul’bulowa daga jikinta, takure jikinta tayi tana adduar Allah ya takaita mata wahala…Gabadaya miyar naman da maman sajida ta ajiye mata ba tayi mata ba shiyasa ko kallonta ba tayi ba, tana gama shan tea ta mike da niyyar sanja guri! kawai taji jini ya tsinke mata! da sauri ta durkusa kasan dakin jikinta na rawa, zanin jikinta ta d’an janye nan taga jinin duk ya ‘bata gurun..Maman sajida ta shigo ta ganta tana kuka gata a durkushe tace”Ke kuwa me yasa kike haka sai kace wata wacce zata haihu sai durkuso kikeyi.” Tace”Kiyi hakuri dan Allah ina mikewa naga jini na bin jikina shine tsoro yasa na tsuguna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button