MADADI 1-END

MADADI Page 51 to 60

Maman sajida tace”Ta’b! aikuwa gaskiya nayi miki na Allah da annabi ke zaki wanke kayan jininki…Dakinta ta shiga ta dauko mata wasu kayan ta fita tana jan karamin tsaki! gaskiya tayi abinda zata iya haka kawai azo ana sata aikin jini.

Naja’atu tana kuka tana kimtsa jikinta, tasa zanin data cire ta goge inda ya baci ta fito da kayan a hannunta, bandaki ta nufa tasa su cikin bawo ta zuba ruwa da omo ta shiga wankewa…Maman sajida ta koma dakinta ta sake gyarawa sai mita take ta dauko turaran wuta tasa sannan ta fesa turaran kamshin daki ta nemi guri ta zauna tana jiran shigowarta.

Naja’atu tazo ta zauna jikinta duk yayi sanyi idan kuka ganta sai kun tausaya mata, sosai take bukatar kulawa sabida jinin data zubar…….Maman Sajida ta kalleta a nutse tace”Meye sunanki. da sunan garinku”? 

Tace”sunana naja’atu kuma ni ‘yar kano ce nazo jos ne gurin kawata munira ina sauka a tasha wani ‘barawo ya warce mun jakata da wayata da kudina duk a ciki..bayan na shigo cikin gari kuma wasu ‘yan iska suka biyo ni da gudu suna so su cutar dani shine dalilin daya sa kuka ganni ina gudu.

Maman sajida tace”Ayya Allah y kiyaye gaba, sai dai abunda ya bani mamaki dake shine, dama kin san kina da ciki ko kuwa kema baki san kina dashi ba dan gaskiya ni kallo daya nayi miki naga kamar mutuniyar arziki ce ke.”

Naja’atu tace”Nasan ina da ciki shine dalilin daya sa ma na bar garinmu nazo nan.” Maman sajida tace”Abun kunya kika gudarwa ashe.”? Da sauri ta girgiza kanta tace”Ko daya cikin nan da ubansa ba shege bane kamar yanda kuke tsammani…Auran dole akayi min da mijin yayata bayan rasuwarta……..Tiryan tiryan Naja’atu ta sanar da mmn sajida labarinta…Maman sajida tace”Ni kam banji dadin abinda kika aikata ba na’jaatu da kinyi hakuri kin zauna da mijinki da yafi miki alkairi wallahi to da kikazo garin jos me kike tunanin zaki samu.”

Tace”Nazo gidansu kawata ne amma bada niyyar na zauna ba idan an kwana biyu zan koma gida.” Maman Sajida tace”To ai kince kin mance kwatancen gidansu kawartaki.” Tace”Wallahi na mance Amma dai mahaifinta fitacce ne sunansa Alhaji Aminu d’an jarida! Maman Sajida tace”Ai nasan gidan can bayan layi ne.” 

Ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala a cikin ranta…Maman sajida ta mike da fad’in “Ni zani kasuwa yanzu idan na dawo da wuri sai na rakaki gidan idan kuma ban dawo ba sai dai gobe tunda kinga yanayin sana’ata ta dare ce.” Tace”To nagode maman sajida ai tunda na samu gidan zuwan ba zaiyi wahala ba sai kin dawo.” Tace”To su Walid da Sajida idan sun taso daga skull zasu shiga gidan maman ladi su zauna idan zaki shiga ki zauna kema sai ki shiga.” Girgiza kanta tayi tace”babu komai har kya dawo ina gida.” Maman sajida tace to tare da kama hanyar fita daga gidan kafadarta rataye da jakarta.

To can gida haka suka wayi gari cikin alhini gami da damuwar ‘batan naja’atu! hauwasa sukace labarin duniya baya ‘buya sai ga mutane suna doko sallama da sassafe suna shiga gidan malam da Alhaji wai sunzo jaje! wannan al’amarin ya sake d’agawa baba talatu hankali da yake bata iya tashin hankali ba tsakanin jiya da safiyar ranar duk ta rame kuka kuwa tayi har ta gaji! Jama’ar da suke ta tururuwar shigowa gidan yasa ta shige daki ta kwanta duk wanda yazo sai dai Baba Magajiya wacce ta kasance ‘yar uwa a gareta ta sallameshi wasu dai gulma suke zuwa wasu kuwa suna zuwa ne domin su jajanta al’amarin to komai dai menene kaddara bata wuce kan kowa ba.

‘Bangaran Abbah Abbas kuwa duk yana samun labarin abinda ke faruwa daga bakin Abokinsa da Salim dukkaninsu sun sheda masa cewar babu wani cigaba dan har yanzu babu wani wanda ya kawo musu labarin ya ganta a wani gurun……Abbah Abbas kasa ‘boyewa mahaifiyarsa al’amarin yayi duk ya sheda mata halin da ake ciki…..sosai hajia Abu ta shiga rudani da tashin hankali itama sai da ta zubar da hawaye tana fad’in “Ina yarinyar nan ta kai kanta da ‘karamin ciki a jikinta me yayi zafi!? da har zata nemi salwantar da rayuwarta akan abinda babu dole a ciki, idan auran Abbas ne bata so to kam insha Allahu za’a warwareshi domun ta samu zaman lafiya in yaso daga baya sai ta auri wanda take so……Halisa kuwa sai nuna alhini da damuwarta take a kan lamarin gefe guda kuwa sai suyi waya sau uku da Yaya Ramlatu suna sake tattauna maganar da kuma ‘karawa kansu kwarin giwa tare da sake gazgata maganar boka ai dama ya fada musu cewar yarinyar za’a nemeta a rasa yanzu abu daya ne ya rage a cikin maganganun da bokan yayi.

Naja’atu kasa zaman cikin gidan tayi sai ta lalla’ba tasa hijabinta ta fito wajen gidan ta samu rumfar kwanon da jama’ar maman sajida ke zama ta zauna tana kallon yanayin garin….Tamkar bariki kowa sai abinda yake so yake yi mafi akasari ma ‘yan matan garin basa yawo da mayafi a jikinsu gasu yawanci duk ‘kananun kaya ne a jikinsu da wuya ka gane kafuri da musulmi….Yanayin garin sam beyi mata ba sai dai kuma yanda suke gudanar da muamularsu ta babu ruwana da kai ya burgeta.

Babur ne ya ajiye maman sajida a kofar gida, ta mike a hankali ta iske gurin da take…Maman sajida ta shiga dauko ledojin kayan miyarta Naja’atu ta taimaka mata suka fito da kayan…Sallamar mai babur din tayi suka dauki kayan suka nufi cikin gidan……suna shiga mmn sajida ta shiga aikace akaice hura wuta tayi ta d’ora madaidaiciyar tukunya sannan tazo ta zauna tana gyara kayan miya, naja’atu kuwa suna hira tana taimaka mata da yankan salak da kabeji! maman Ladi ce ta shigo gidan yara na biye da bayanta.

Mmn sajida tace”Wallahi yanzu nake zancan ku a raina.” Maman ladi ta zauna kusa da ita tana fad’in “Ai nasan yau zakije kasuwa shiyasa naje na dauko su daga makarantar da kaina amma gaskiya yau kin dawo da wuri.” Maman sajida tace”Wallahi nima naga saurina yau ba cunkuso a kasuwar…..Naja’atu tana jinsu suna ta hirarsu bata sa musu baki ba, haka kawai Maman ladi bata kwanta mata a ranta ba….Taji maman ladi na cewa”Amma dai yarinyar nan ta fad’a miki daga wane gari take ko.”?.

Maman sajida tace”Eh daga kano take ashe gidan Alhaji Aminu dan jarida take nema tazo gurin Munira ne.” Mmn Ladi tace”To ikon Allah ai sai kiyi mata jagora zuwa gidan. Mmn sajida tace”Eh insha Allah gobe da wuri zan kaita gidan.

Naja’atu takaicin maman ladi kamar ya kasheta ta lura matar ‘yar bakin ciki ce sai kace a kanta take tabi ta damu! Bai dace mmn sajida na k’awan ce da ita ba tunda ita zuciyarta mai kyauce ta tabbata da mmn Ladi ce ba zata ta’ba yarda ta zauna mata a gida na yini guda ba……Kafin mmn Ladi ta tafi gidanta sai da tayi wa mmn sajida wayo ta kwasar mata kayan miya har yankakken salak din sai da mmn ladi ta d’iba sai dariyar ya’ke takeyi irin ta dubara….Ita kuwa mmn sajida sai girgixa kanta take tana mamakin rashin imani irin na makociyar tata ita da take da miji mai bata kudin cefane amma bata godewa Allah ba tazo tana d’ebe mata kayan sana’arta bata duba irin wuyar da take sha da marayun ‘yayanta kullum sai tazo ta dauke mata abu a gidan, ashana wannan mmn ladi bata siya sai dai duk sanda zata d’ora girki ta shigo ta dauki tata, idan taga maginta ta bude ta zazzaga gishiri ta zazzaga har manja da mankuli tsiyayar mata takeyi…al’amarin dai na mmn Ladi babu mutunci da tausayi a cikinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button