MADADI 1-END

MADADI Page 51 to 60

*Ayi hkr ayi manège*

*Vip Mdd ba haram bane naga comments dinku akan pegenmu na yau kuyi hakuri da duk wani pege da zaku karanta anan gaba a yanzu ne sa’kon labarin yake so ya isa shiyasa kuke jin rashin dadi! kuyi hakuri ku cigaba da karantawa daki daki insha Allahu zaku fahimci inda na dosa*

*MANZIR _ALWAFIR ABUJA????????*

_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya ‘kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_

Mdd 44

Naja’atu na zaune tana kallon yanda Mmn Sajida keta aikin abincin siyarwarta tana kallo ta kammala komai ta shirya cikin kuloli gwanin sha’awa, Mmn Sajida nada tsabta da kula sosai a kan sana’arta shiyasa take da costomas sam ba tayin kwantan abinci komai yawan abinci idan ta fita dashi tas take siyarwa ta had’a kan kudinta..Mmn Sajida haifaffiyar jos ce iyayenta da kaninta duk suna garin tayi aure shekaru goma da suka wuce sun haifi yara biyu da mijinta kafin Allah yayi masa rasuwa, tun bayan mutuwar mijinta ta soma fuskantar matsala ta rayuwa ‘yan uwanta dana mijin nata kowa kansa ya sani babu mai taimaka mata da sabulu ko omo yace tayiwa yara wanki idan taje neman taimako kafin ayi mata sai an gama wulakantata tukkuna to tunda ta fahimci rayuwar duniya haka take sai ta kama kanta ta shiga neman kudi duk domin ta rufawa kanta asiri da yayanta inda Allah ya rufa mata asiri ma gidan da take ciki na mijinta ne shiyasa wasu abubuwan sukayi mata sauki sai kawai ta yanke shawarar zamanta a ciki domin tasan babu wanda zata jewa da marayun ‘ya’yanta ya ri’ke su tsakani da Allah ganin yanda duniya ta koma kowa kansa kad’ai ya sani kad’an ne masu tausayi da tsoron Allah…….Sai kawai ta yanke shawarar siyar da Kayan d’akintata shiga sana’ar siyar da abinci cikin ikon Allah Ubangiji yasa mata albarka a ciki…Yanzu Mmn Sajida tafi karfin komai sai dai wani ma yazo yaci alfarmarta, Mmn Sajida bata da rowa ko kadan sai dai abotarsu da Mmn Ladi yasa ta d’an koyi wasu munanan d’abi’u daga gurinta.

Tare suka fita da Mmn Sajidan ta zauna kusa da ita tana d’an taimaka mata da wasu abubuwan….Mazan da sukayi yawa ne a gurin yasa taji zaman gurin ya fita daga ranta, ta tsani kallon k’urrula ko kadan ta fahimci mazan garin su kuma dabi’arsu ce..Da har tayi niyyar shiga gidan kodan ta huta da kallon da ake mata sai kuma ta hakura ta daure ta zauna ta cigaba da taimakawa Mmn Sajida dan ta lura abin yayi mata yawa kowa idan yazo da kalar abinda yake so…….Naja’atu na kallon wani magidancin mutum wanda tunda ya tsaya a gurin yake kallonta yana mata murmushi, har sanda Mmn Sajida tazo kansa tana masa magana hankalinsa gabadaya na kan Naja’atu sai kace zai cinyeta…Mmn Sajida tace”Haba d’anTalle tun dazu nake magana kayi shuru yanzu idan wani na sallama kace na tsayar da kai.”

Mutumin da ta kira da ‘DanTalle ya shafa gemunsa a sanyaye yace”Mmn Sajida yaushe kika samu yarinyar nan lallai na kwana biyu banzo gurin nan ba.” Mmn Sajida sanin halin Dantalle yasa tasha kunnu sosai tace” Bakuwa ce wannan kuma ba irin taku bace kai dai ka fad’i me kake so na zuba na had’a maka.”

Yace.”Ki zuba min shinkafa da wake da miya.” Mmn Sajida na kokarin zuba masa tace” ‘Kashi ko nama wane zan sa maka.” ? Hankalinsa na kan Naja’atu yace”Ki samin ‘kashi.” Mmn Sajida ta had’a masa komai ta mika masa ya dauki jarkar zu’bo guda d’aya a sanyaye ya nufi cikin ‘yan uwansa dake cikin rumfar kwanon da Mmn Sajida ta tanadar musu.

Yana barin gurin Mmn Sajida taja tsaki tace”Narasa wane irin hali ne da Dantalle wallahi ko wace mace ya ‘kyalla idonsa a kai yace yana so. Ta kalli Naja’atu da fad’in “Nasan shi da mugun bin diddigin tsiya saboda haka kiyi taka tsantsan dashi koda wasa kada ki sakar masa fuska har Allah yasa ki bar garin nan.”

Naja’atu a sanyaye tace”Nagode Mmn Sajida nima wlh mutumin gabadaya beyi min ba tunda ya tsaya a gurin nan yake kallona kamar maye.” Mmn Sajida tace”Kad’an kika gani ai haka yake mugun son mata ne dashi ga shegen aure auren tsiya hanzu haka matansa hud’u amma baya cin abinci a gidansa kullum yana nan yaci mai dadi ya barsu da garau garau shike nan yawon bariki da kashewa matan bariki kudi.”

Naja’atu tace”Allah ya shiryeshi idan zai shiryu…..Koda DanTalle ya kammala cin abincinsa sai yazo ya tsaya yana gyara bakin aljihunsa domun fito da kudi Mmn Sajida taga ya dauko dubu hudu ya mika mata tace”A’a Ai dari shida ne kudin abincinka.” Yace.”Eh na sani nayi niyyar yi miki kyauta ne ki dauki dubu biyu sai ki bawa yarinyarki dubu biyu.” Mmn Sajida tace”Anya za’ayi haka kuwa na fad’a maka komai kuma kasan ni bana cikin wannan shirman da kuke yi.”

Yace.”Haba Me yasa kike wannan maganar Mmn Sajida ni bada wata manufa na baku kudi ba nayi niyya ne kuma idan inason yarinyar nan da aure zan so ta bada wata manufa ba.

Mmn Sajida tace”To godiya mukeyi Allah ya ‘kara budi.” Ya amsa da amin yana kallon Naja’atu da wani shegen murmushi a fuskarsa..Girgixa kanta kawai take tana mamakinsa lallai kam ya ci sunansa ‘DanTalle ita wannan ko a ‘kafa a daura mata shi a ta kwance da gudu, daka ganinsa idanunsa a bude suke kar!! dasu irin na mayaudara! Ya juya baya da niyyar barin gurin tabi shi da kallo! ‘Tab! gabad’aya bashi da tsarin mazan da take so wani siriri dashi kamar zai karye sai dogon wuya kamar mari’kin lema a ganinta ma ina yaga kuzarin da zai tunkareta..ita duk wani siririn mutum raina shi takeyi tana ganin kamar basu da wani karfi da kuzari( Kaji wauta irin tana Naja’atu ‘kananun maza ma sunfi jaraba kuma babu abinda za’a nuna musu)….Sai kusan sha daya da rabi na dare Mmn Sajida ta siyar da abincinta suka harhada kayan suka shiga cikin gidan.

Karfe takwas na safe sun shirya Naja’atu tayi wanka ta shirya tsaf Mmn Sajida ta bata sabuwar atampa da mayafi tasa a jikinta sannan kuma ta hada mata wasu atampopin kala uku tasa mata a leda viva Naja’atu ta dinga yi mata godiya tana mamakin karamcin matar gaskiya samun Mai hali irin nata sai an tona.

Suna kokarin karyawa Mmn Ladi ta shigo gidan, ganin naja’atu cikin sabuwar atampa sai tayi kici kici da fuska ta wani dogare a bakin kofa tsabar bakin ciki da hassada yasa ta kasa shiga.

Mmn Sajida tace” Ki shigo mana ki zauna dama yanzu nake cewa zan aika Walid ya fada miki ko zaki zo muje tare.”

Mmn Ladi ta ta’be bakinta tana girgiza kanta da fad’in “Babu inda zani aikin gidana ma ya isheni.”

Mmn Sajida tace”To shikkenan ki shigo kisha tea gashi muna hadawa.

Babu kunya Mmn Ladi ta shigo tana ya’ke da fadin “Kamar kuwa kin san ban karya ba har yanzu dan yau mutsiyacin mutumin nan ko ‘kwandala bai bani ba ya futa.

Mmn Sajida tace” Ke Mmn Ladi kiji tsoron Allah ki daina tsinewa mijinki wallahi ki dinga hakuri da yau da gobe idan kina ganin ba zaki iya jurewa ba to ki nemi sana’ar yi amma zagin miji da tsine masa bashi da amfani.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button